← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 173

Sashe 101

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

abunda ake ciki Jahan Aarah Kasa zama tayi tana jeka ka dawo tana kuma jefo masa tambayoyi,...bayan Ranta ya baci sosai hankalin ta ya tashi..subaya na zaune agefen gadon khal rungume da bahin taga kira jahan...tace kizauna anan bari naje na dawo karki fita kinji?... Tayi sauri ta isa falon jahan.. Da sallaman ta shigo Tana durkusawa zatayi gaisuwa jahan ta dauke ta da wani makahon mari.. "Haka kika rike min yata?...subaya kin bani mamaki. Under ur roof amma baki ma lura...in kashe ta za'ayi ma bazai dame ki ba ko?..what sort of live is this,wai nace maki dole ne nooor sai ta zauna a hannun ki. I shud have known that ba rike min ita zakiyi ba ke mijiin ki ne y dame ki Ni Babu ruwana da abunda ya shirya akan ki,ai dama sa'ood yaki jinin yaron nan amma naki daga kai sabida farincikin ki But u failed me... Bahiyyar yar shekara nawa ce da baxaki san abubuwa nadamun ta ba Amma wai har baki da tunanin da zaki iya sanin gaskiya da karyan mijin ki?..inason da kike ma yar uwann kin .. Na fahimce ku ku biyun..wato tsame ta kukayi daga jikin ku dan son zuciyar ku ..sabida kunga ita ba jini na bane .. And you...angel...ta juyo ta kalle shi kansa na kasa sabida baya son ganin bacin ran ta bata son mashi fada amma yau sosai ta bata ranta.. U lied to me... kace kana son aure da bahi dan kana bukatar haka..ashe akan subaya kake so ka cutar da marainiyar Allah... "U did well ok Yanzu ai kunji kunya da kuka gane cewa karamar yarinyar da kuka raina is ready to secrifice her life for ur happiness... ...Ba gaskiyar ta fito ba..kaje da yar uwan ka subaya ku warware matsalan ku... ni zan warware auren dakuka laka mata....U most go and set my doter free yanzu nan ...kabani yata...i mean it Muryan shi har na rawa ya waro idanun shi Yace Pls Mamah kiyi hakuri.. Ya dago ya kalle ta hankalin sa a mugun tashe Yaune rana na farko da ta kore shi a site din ta out of anger ...baiso ya tafi ba amma yaga alaman babu sauki A fuskan jahan,shi maganan zata raba aure shi yafi kada masa hanjin ciki...Daya bar wajen Kasa zama yayi yana ta jeka ka dawo Subaya kam tuni ta rusuna gaban ta,ta dinga rokon ta tana bada kanta dukkan laifin duniyar nan gwanin ban tausayi.. Tace mum..nice na saka shi yayi maki laifin dan Allah ki karki masa purnishement mai tsauri...he love her,,misunderstanding ne ..jahan bata ma kula ta ba har ta gaji ta bar site din.. To kaamil ya kira Khal akan yadda zasuyi da rayuwar sadat. Tuni jahan ta aiko maids aka kawo mata bahiyya site din ta Agidan ba asake barin bahiyya ta fito ba aka boye ta sosai ..jahan bata huta ba anata fannin sanda ta shiga ta fita tasan yadda ta shawo kan al'amarin tun daga sama. Khal da subaya sunsha fada wajen alhaji hamood,musamman ma da sukayi ta boye komai har akan maganan auren nashi. Bahiyya kuwa tasha tarairaiya Ita kanta bata taba ganin tashin hankali kamar na ranar ba.. Gaba dayan su sanda suka bata tausayi,tayi ta bayani ma jahan da kyar ta karbi uzurin ta ta yafe ma subaya da khal har aka samu aka hadu waje daya sukayi family talk tsakanin su.. Alhj yace kar su sake boye komai tsakanin su,dan haka ne ma subaya ta fito fili ta gaya musu cewa cikin sadat dake jikin ta na tswon wata biyu ya lalace sabida yawan shiga shock din data yi.. But xubar cikin is not upto 3 days dan haka jahan tasa mu damar hada ma cikin certificate ta turo ma lawyern ta shedan daya sa akan file case din data ke shiryawa mai zafi akansa Jahan Aarah bata wani sake musu fuska ba,dan har iyanzu bata magana normal ma kowa acikin su sai bahiyya Da kaaamil ya mata bayanin plan dinsun ma da kyar ta amince... By 1.ocl na rana suka watse agidan khal da bahiyya da subaya suka tafi abuja Sadat kam tun 8 ya bar gidan da document din subaya baima san me ake ciki ba. Suna isa abuja gida ya warware dan sakewar da kaamil yayi yasa jahan khatin tayi tunanin ko maganan ta yaji ya share tashar bahiyya...,subaya dataje wajen kakan ta dilshad yau ta fara ganin su junnut Junnut sai rawan kai take nata ita adole taga sister inlaw,dan jahan khatun tace mata ta kama kafar subaya sosai...indai akan khal ne ... Subaya, kaamil da khaldun suka dai suka san me suke ciki,.. Kowa acikin su yayi tsam ne yana jiran kiran sadat awayar bahiyya.. Da shike su hjy indira sun iso suma,sai subayan take debe musu kewa By 4.pm bahi ta fita wajen sadat..duk tracker da suka saka mata ajikin ta babu wanda baiya reading awayar su .. Sadat dake cikin tsananin farin ciki yana ganin dosuwar bahi yaji wani sanyi aransa ...... Kaamil na wajen shikam a cikin daya daga cikin abandorned cars din da aka aje awajen yana kallon su... Bai wani saka kayan arziki ajikin sa daga shi sai wandon sojoji da khaki vest duk damtsen sa sun fito boro boro.. Ta bata rai kamar da gaske,wawan tuni ya shiga jefo mata maganganun banza yana cewa daga yau ta dawo Amaryan shi... Dama sun shirya Draman su da su khal dan haka,batace masa uffan ba,sanda ya kama hannun ta zai sata a mota su tafi airpot ta gantsara masa cizo ahannu ta ja da baya Cikin neman taja lokaci tace ka tsaya ni fa ban shirya ba.. Dariyar mugun ta ya Yai yanacewa ai bata isa ba tunda ya bar rayuwan subaya da khaldun dole ne itama ta zamto a shirye... Yace ke bani abun wuya na...tace abun wuya? Ohh gosh wallhy na manta dashi a harsgitse yace what?. Tace yes..wani wawan marin ya sauke mata yanacewa kika manta dashi?..dan ubanki baki sam rayuwa ta bane anan... To ya kike so nayi..kin dauka ko lallaba ki zan dingayi...ya wani cakumo ta azafafe yace ni bana son shirme kuma ba zan dauki iskancin kin ba. Tuni idanun ta suka ciko da ruwa Shakure ta yayi yana dangwarar ta kamar ya samu kariya jin numfashin ta yana sarkafewa ta tsala ihu tana da kyar cewa Toh Ka sake ni .. to aina kija aje min abun wuya ta ..fincike jikin ta takeyi kamar da gaske tace nifa ban san ni... A zafafe sadat yace kin batar?dan ubanki batarwa kikayi Duk hakan na tsumo kaamil amma haka ya daure bai fito ba sanda yaga bahi tayi iya kokarin tana jan sa har lokacin da khal zai iso Sun dage sai jani in jaka sukeyi da sadat ya fada ta fada tasha maari har sau takwas fuskan ta ya kumbura yayi ja.. Cikin mugun jin haushin ta sadat yace ni kina bata min lokaci,muje kawai dole ne ma na kashe su..ta make hannun ta ya kwato tace leave alone ai zanje na kawo maka Yace bazaki je ba tace sai naje Wani muguwar murya suka jiyo daf abayan su...cikin dakewa yanacewa What is this shinanigans? A firgice sadat ya sake ta ya juyo,dan ko a lahira ne baiya manta muryan sa'ood... Sadat dake raba idanun sa Tun kafin ya gama dawowa da idanun sa akan bahiyya da tuhuma ta sai ga kaaamil ya fito Abayan kaamil sojoji ne masu jan hula hannun ya musu suka fito da wani kerarran mota suka faka tuni aka gewaye shi Sadatt yayi hadiyan yawu yafi sai dari a dakika daya .Baiyi tunanin bahiyya zatayi masa haka ba Sojojin su suka tsaya gefe da gefen sa,Wajen kaamil bahi ta koma ta tsaya daga bayan sa.. Khal dake ji kamar zai cinye namar sadat danye baice komaii ya shiga hada gagarumin wuta mai ci bal bal a tsakiyar filin Wajen tuni waje yayi dishi dishi yayi dan duhu duhu sabida babban tayar mota yake konawa Idanun sadat tuni yayi jajir.. Sai zufa yake ta kayi amma sai yayi irin basarwan nan minti daya zai gyara neck tie ko zanzaron wandon shi Kamar mahaukaci ya fara fade fade yana zage xage Kaamil ne ke amsa shi cikin azalzaa masa masifa...da barazan masu kada hanjin ciki shikan damaan yasan kaamil ya tsane sa Kuma ayau tunda yagan su su biyu Yasan tashi ne ya zo karshe,wani dadin haushin dayakeji bai wuce da bahi tace babu magic necklace dinsan anan ba Irin abubuwan dayake tsoro kenan gashi tafaru ta kare ...but ahakan ma Rashin kunya ya ke shiri zai musu Toh Yasan idan ya zage subaya dukan su ransu zai baci suyi masa duka,out of borin kunya da tsananin firgicewan tsoro ya shiga zagin bahiyyar yana gwada musu cewa ya wulakanta ta kuma idan suka taba shi yana da hanyar da zaisa aka masu a daure su tunda shi lawyr ne. Khal yana gama abunda yake ya taho gaban sa,irin yayi basarwan nan zai fuskance shi,a baxata yaji an danna fuskan sa ajikin wani hankerchief....wani garin daya zuka har brain dinshi taje bari ya shigayi karkar tsaban reaction din daya bayar sanda bahi ta dada boye idanun ta abayan kaamil.. Five minutes khal bai sake shi ba sanda ya lura cewa abun ya shige shi ,yana matsawa ajikin san kuwa sadat ya rike kansa ya danna wani irin gigitaccen kara... Goma goma yake kallon su yana wani irin juyayai daga ganin sa kasan yana cikin wani irin mugun halin da bazai iya misaltuwa. High grade cocaine irin wanda baban shi ke sayarwa shi khal ya dura masa almost 1full dose acikin raman hancin sa Kaaamil ya fashe da dariya..Ya sa bahi ta shiga cikin motar da aka kawo din cikin jin dadi da nishadi yace mata its fun time. Wani vuuum vuummm tayi.khal ya hankade sadat agaba tana binshi da motar a madaidaicin speed yana gudu da kafan sa yana zaga filin kamar tabbatacen mahaukaci.. ,..ga radadin cocaine na ratsa shi yana ta sose sose kamar ana cizon sa...khal da kaamil suna gefe suna kallon su.. Bahiyya kuwa Tun abun yana bata tsoro har taji tana samun sauki dataga sadat acikin wani irin wulkantaccen yanayi... Inta kalle hawayenn azaba dake kwalala
Chapter 101 · 0% Book details