Sashe 32
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni dai tunda na tashi naji ni garau sai bandamu ba.. But Dan na kaucar da irin wannan matsalan sai na tuno da wani recipe din smoothie wanda da hannu na ma zan iya yinsa ba sai nayi amfani da wani processed drink ba. Da sauri na bude fridge na fara dube duben ingredient din hada shin. Nan na dauko ayaba guda daya na saka a freexer na kara masa karfin sanyi don kuwa so nake ayaban yayi kankara sosai. Anan na fito da green matcha tea powder na debe kopi daya,na hado da ground flax seed rabin tea spoon da kopi guda na fresh almond milk. vanilla extract dina na gefe and finally sai na dauko cocunut na yi shredding dinsa yayi kyau na hade su waje guda cike da kwarewa na hada abunda ake kira "Cocunut matcha smoothie" Its soo yummy and pleasant to the eyes ga dan uban qamshin shi daya cika min hanci har bana jin qamshin sauran abunda na soya. Ko da naje ina shirya tray din jan dinning bansani ba ashe Tsaye yayi daga baya na yana ta kallo na Nasan dai Ya danji dama dama dayaga na warke but his face wasnt showing any emotion. Bansan yana baya na ba Dan haka da muka ido sai nayi saurin kau da idanuna cikin sanyin jiki hade da tuno duk abunda ya faru jiya tsakani na dashi,wani boye murmushi na nayi sannan nace ina kwana? Sama da kasa ya kalle ni,ko ya amsa ko bai amsa ba oho,dan ni dai banji ba. Zama yayi idanun sa na kan wayar sa yana latsawa. Nikuwa Cucunut macha Smothie din na fara serving dinsa a cup dan haka ya dauki cup din batare da wani tamtama ba ya shiga kurban abunsa. Abun ya matukar bani bani mamaki Does that mean khaldun sa'ood ya yarda dani?Ko dan yaga nima nasha drink din ne?Nidai Sosai naji dadi araina Toh har na juya plates kenan zan zuba mashi sauran abincin Sai naga ya dago fararen idanunshi Ya kalle ni sai ya kuma juyawa ya dubi seat din gefen sa "Sit...ya furta yana kure ni da wani makalallen kallon aji mai tafe da kasaitar data kafa tarihi araina. ...tuni mamaki ya balbale ni don bansan ko naji abunda ya fada da kyau bane ko banji ba. But wait oo Did he just asked me to sit with him? Ai naji ance babu mai zama dashi anan sai jahan dan ko abokinsa shahrul dayaxo ma banga ya zauna da shi anan ba. Tsaye nayi ina murda hannu cikin rudani,ina dai so na tambaye shi dan nayi clarifyng Amma kuma nasan khaldun baiya maimaita magana so i just took the risk sai na matso kusa da shi na ja seat din na zauna a dan dofane. Shikam Baima sam inayi ba,Looking very calm yaa aje Cup din smothie akan table..ya kalle fuskata dake dan sunkuye. Da wani irin daddan husky voice dinsa Yace Serve!! Banma san lokacin da na dago ba. But Ganin tuni ya dauke kansa ya mayar kan wayar sai nima na shiga serving dinsa daga inda nake a xaunen Halwa bread din na fara ajewa kafin na bi da South indian egg masalan agefe Ganin yayi rabin smoothie dana sa yasa na kara zuba mashi wani shidai Baice min uffan ba har nagama. Daga nan Wayar sa naga ya aje agefe sai ya turo min plates din abincin gaba na. Tsoro yasa nayi rau rau da idanu na,..tunani na ko abunda nayi jiyan ne za ayi min hukunci..but i tot he has forgiven me, a take naji na shiga rudani ma fara tunanin ko dai bai yarda bane? Ban ko gama haukar tunani nan ba naga ya juya another plate ya aje agaban sa a cikin salon da banyi zato ba naga yana serving kanshi da kanshi.. Waje idanuna suka fito suna rau rau da kansu ina ta satan kallon shi baima san dani ba,duk mamakin shi ya kure min tunani barin ma Yadda naga salon daya zuba abincin a plate dinsa simplified and classic cikin iya tsara space tamkar tsohon wanda ya kwarance a aikin dafe dafe wanda ko ni nasan ban iya ba... Yana gamawa kuwa ya dada gyara zaman shi,Loma biyu yayi masu kyau kafin ya dago ya kalle ni,..fuskan sa adan daure Yace Eat"..arude nayi saurin cewa ok.. Hannu na tuni ya daga spoon da fork din amma ban iya komai da shi ba sai mu kaji sallama akan mu. Jahan ce da kanta ta shigo dan haka a take nayi yunkuri zan mike tsaye Ban ma lura da shigowar subaya da saddat ba sai da khaldun ya balla min wata hararar daya maida ni kan seat dina batare da niyya ba. Spoon da fork din na dauka idanuna a kasa na shiga juya abincin cikin fargaba Dukan su fuskan su sai da ya nuna alaman mamakin ganin mu a hakan To top it all ga abinci agaba na. Jahan was like is this for real?ta dan kalle mu da kyau dukan mu.. Na dada sunkuyar da kaina cike ladabi da sanyin murya nace good morning mum. Sai Ta dan dafa kafadata da sauri ta dago ni nikuwa sai cire idanu nake tsaban bugun kirji na,noor are you ok?u r suposed to be on ur bed,Ashe jiya baki ji dadi ba shine bazaki zo ki fada mun ba ko? A yadda tayi min maganan cikin tsananin kulawa Duk sai Na rasa me zance mata sai kawai nayi mata shiru Cikin kasaita mai nuna sanyin bacin rai khaldun Yace mum pls Alaman an yi distrupting din breakfast dinshi kuma baiji dadi ba. Jahan dai Batace masa komi ba ta narka masa kyakywan idanun ta akan nashi lips din ta dauke da miskilallen murmushi mai masa alaman ya dakata mata Yana dauke idanun shi ta dan dafa shi Kasa kasa tace mashi ayi hakuri ..dole ne ya sani na zo nan khaldun,i need To check on my doter. A dan yangace yace not now mum..karya wa muke yi and i need my space. Wannan maganan da su subaya ya ke Nikuwa wannan phrase din nasa na karyawa "muke yi" yasa na dago da kyau na kalle shi Jahan Tasan halinshi sarai dan haka bata tsaya maimaita abunda subaya da sadaat suka fada mata akanshi da safen ba. Itama Zama tayi tare da mu Cikin ido ta dube shi calmy tace Aaban,are we good?da kamar zai amsa sai ya basar abincin shi ya cigaba da ci bai ko kula ta ba,ta kalle shi ta dan kalle ni.. Sai tayi murmushi. Sadat ma ya kalle subaya itama ta kalle shi abun ya matukar basu mamaki Wani shiru ne ya ratsa wajen kowa da abunda yake sakawa aransa A Bazata khaldun ya sake Wani miskilillan murmushi wanda ko lips dinsa basu san yayi shi ba sai ya kada kansa batare daya sake daga idon sa ba. Allah kadai yasan meke gudana aransa a time din Abincin sa yake ci ya hade ransa,sadat daya ga nayi tsuru tsuru bana iya motsi agaban sa'ood da jahan sai lafe ta kunne yace ma subaya ta je ta dago ni a tsakiyan su,... looking like he cares da razanar da nayi Babu musu kuwa subaya ta karaso dan ita kadai tasan wahalar data sha wajen shawo kansa da safen nan Tana kuwa dafa ni khaldun ya balla mata wani mugun harara,amma da shike taga jahan agaban su sai ta share shi tace min get up little sis wa yace miki kizauna anan din zo muje daki,...a hankali na dago na kalle ta sai naga ta na kokarin jawo hannu na. Wani karar Stop it din da mukaji sai da yasa ta sake ni da sauri ta kalle shi adan tsorace,pls let her have her breakfast....sai ya dan saukar da murya ya bita da kallon dagaske yake wani mamaki ne ya turnuke subayan har ta kasa cewa komai sai kallon shi data keyi itama... Agefe kuma bakin ciki,haushi da rudewa ya hana sadaat cewa uffan subaya kamar zatayi kuka ganin dik na razana,jahan dake lura da shi tace pls ka barsu su tafi mana naga kamar ma bacin komai takeyi ba Bai jira ta karasa ba ya dago spoon dinsa ya debo abincin yana kallon jahan din yace zata ci mana.. Sai ya juya gare ni cikin jan aji ta salon yin wasa da tunanin su, nan ya kawo abincin dai dai setin baki na a hankali yace min open Chak wajen ya dauke da ji.. Rawa ma baki nan ya fara yi tun kafin na bude shi,yau nidai naga takaina yau ga khaldun of all ppl wai zai bani abinci abaki,. slowly na bude baki nawa ya sa min spoon din ban ko iya taunawa ba na gumse shi dan mamaki da rudani ya hana zuciya ta sakat And More than anyone awajen zuciyan sadat kamar zai fice daga kirjin sa tsaban bakin ciki. Jahan kam murmushi tayi,ta mike tare da cemin idan na gama break in nazo tana nema na. Ban iya amsawa da words ba na gyada kai,am sure jahan ta fahimci halin da nake ciki alokacin sai bata juyo ba har na dena kallon ta Subaya gaba daya ta kasa kamu kan tashan. Dan sosai sadaat ya zugata da safen ma har suka je wajen jahan da magana akan abunda ya faru jiya gashi khaldun sai juya abubuwa yake. ayadda suka juya ma jahan labarin ta dauka ko zata zo ta samu bahiyyya na kwance awani hali Sai gashi khaldun is set to suprise them ..babu wanda ya yi tunanin zaiyi abunda yayi yanzu Khaldun ya cigaba da bani abinci abaki har hawaye suka gangaro min tsaban tsoro ban ma sani Subaya tayo shiru akan mu dan ko uffan baice mata ba bare ma ya kalle mijin ta Daga nan Bamu ma san lokacin da sadaat din ya fice ba,sabida inda za'a bude kirjin sa aga bacin ran dake ciki da tabbas gobara ne zai tashi awajen Da ya rage saura mu ukun,wani kallon barazana yamin ataikaice alaman naci gaba da ci da kaina shi ya gaji,dan haka yana mika min spoon din ya tashi ya haura sama ya barmu nida big sis munyi lumui muna bin bayan sa da ido. A gurguje