Sashe 41
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya sha wahala ba. Haka rayuwa ta cigaba ma junnut da khaldun har Allah ya sa ta samu daman rike kasa wajen sa kewa da tunanin shi aranta. Gradually son shi yayi mata zurfi Amma Tunda tazo daga baya ta fahimci cewa duk hadin kaamil ne, babu ma Ko number ta a wayar sa sai itama ta dauko dabiun jan aji irin nasa dan abun ya ci mata rai bana wasa ba,duk abunda yayi itama irinsa zata masa,gashi zatayi ta korafi adan dole jahan khatun ta cire mata tsoron sa har ta samu bakin titsiye shi cikin magana shikuwa wani bin mamakin ta ma yake sha,gaba daya ya lura da iya nuna zagewar ta akan maganan alkwarin auren dake tsakanin su shikuma sam baya son shirme infact aranshi yafi son yaga yaso mace sosai badai macen tafi shi zagewa ba So most time ib tana surutu sai dai yayi mata shiru har ta gaji ta kashe wayar amma kuma idan tayi kwana biyu bata ji shi ba sai kaga ta kira layinsa koda kuwa bazai dauka ba. A bangaren jahan Aarah kuwa babu yadda ta iya ne da biyayyar mijin nata amma tun bata san waye yarinyar da aka laka ma dantan ba taji abun sam bai mata ba. Anything from dilshad khatuns kingdom awajen ta ba Alheri bane. "Duk dama ance alkwari kawai akayi musu amma kusan kowani rana abun sai ya dame ta azuciyar ta. AHUMAGGAH* -london Bayan kusan kwanakin wata guda junnut ta kammala jarabawan ta na gaba da primary. Anan suka sata agaba da huduba marasa amfani,domin kuwa babu ta inda kalaman su yake karkata taje face rudin duniya Jahan khatun ce ta dada zurma zuciyan junnut har ta amince cewa ita dib mace ce mai tsananin daraja da mulki dan haka bazata ta cika sauke kanta Kamar sauran mata ba Musamman da akan nuna mata hoton khaldun sa'ood ake kuma jaddada mata cewa nan gaba shine fa mijin ta. Doka ne junnut in taje america bazata yi saurayi ba dan haka kudin sosai aka sake mata wanda shi kadai ma ya isa ya dauke mata duk wani sha'awan rayuwa da wani wanda bai kai ta ba dukiya. Toh A Washe gari da asubahin fari jirgi ya tafi da ita xuwa chan united states. Bangarena kuwa tun ranar da nagama waec jahan Aarah ta gama min bayanin komai a nitse. Big sis subaya is all excited cewa zan koma zama da su amma sabida mijin ta sadaat sai kwata kwata bana jin wani dadi Dadin karawa ban taba tunanin son da jahan Aarah take nuna min zai yi tasiri a zuciya ta ba sai da muka shiga jirgi muka taho gidan big sis subaya a saudi arabia. Gaba daya sai naji ni cikin shaukin rabuwa da ita I was quiet for sometime,bana fiye motsawa kamar ba yau na fara zuwa kasar waje a rayuwa ta ba. Duk wani zumudi da jjc yaki zuwa min,big sis ce take ta famar jana ko ina tana nuna min wurare. Saudi arabia its a perfect place but i just cant wait to go to my new school in london. Zaman sati guda danayi da su sai da naji nagaji sosai,sadat is alwys on my nerve ga big sis gaba daya bata da gane abu,abun nata ma sai gaba gaba yake yi. Yanzu gashi har ya tursasa ta muna cin abinci tare har dashi a tsakiyan mu. Haka zaiyi ta jefo min silly looks,ba dama na dan kware da ruwa sai yafi kowa daga hankali awajen yi min jaje. har naji nagaji nafara ina shiga kitchen ina taya mai aikin su girki,toh daya gane hakan ba karamin masifa big sis ta sha a hanun sa. Big sis sai tace min ki daina yawan wahal dakanki tunda kinsan darling sam baya son bacin ranki And i also do not want to see you suffering," Ni kuma wanann ba irin kalar rayuwar da zan iya bane tun ina ma big sis bayani har na dawo inta na min maganan sadaat yace kaza akaina saii dai in yi shiru ina jin ta. I just wonder when she wll realised all this. Washe gari da aka ce zan tafi london ji nayi kamar an saka zuciya ta a kankara Here comes my freedom,Atleast zanci abinci,nayi yawo nayi duk abunda nake so batare da sa idon wannan mijin big sis din ba,araina har na fara harsashen hala idan yaga bana nan zai fi bada hankalin sa akan big sis bani ba. Da safen da jirgi na zai tashi tare da su duka muka je london din,ga wani uban shoping din da suka mun,tsaban abun takaici sadaat har da kokarin sa wajen siya min inners. A hakan kuma duk big sis bata dauke sa wani abu ba. Babban universityn dake london din aka saka ni,inda zan karance full 3 +1yrs nutrition course! Im just 15;16 dan haka aka damka ni wajen university maiden,don fir naki shawaran sadaat na cewa akama min hotel ko apartment ba hostel ba. Bansan nufin sa ba amma Har kuka sanda nayi ma big sis sannan ta dan tsaya min har ya amince aka barni na zauna a hostel din. Besides bansan komai game da london ba,and i need my space. So nake na bude idanuna dakaina na batare da sa idon kowa ba ko dan domin nasan abunda ke min zafi Kwana biyu big sis sukayi min kafin suka koma saudia,a hakan ma bata gamsu ba sai da ta nemo min student mate dina musulmai daya daga nigeria sunan ta Khadija daya kuma daga instanbul frm turkey sunan ta jasmin itama duk musulmar ce. Kafin su tafi a cikin tarairaya big sis take cemin idan akwai matsala na kira mijin ta ko ma na kira ta In babu kuma sai hutu zasu zo su dauko ni Nace mata toh kuma A haka mukarabu. Daki na na koma nayi kwanciya ta na dada lumshe ido dan Har Wani sanyin iskan freedom ke bin jinin jikina. I miss my big sis amma idan na tuno Ayanxu there is No more sadaat sai naji dadi Dan shikadai ne abun daya takura ma rayuwa ta. Bangaren junnut kuwa a wani tangamemen condimonium na yayan manyan kasar aka kama mata. Dogon Gidan sama ne mai hawa shida,site din ta na hawana karshe. Sai ya kasance Ni ina kasar london,junnut Dina tana kasar America We both exist in 2 different location batare da mun kawo tunanin hakan ba. And My first day in college was full of abun mamaki. ,sabbin kawaye na da big sis ta jona mu, wato khadija da jasmine gaba dayan su babu tayan baya Na lura wato shi dan nigeria ko aina yake zaka samu he is naturally upgraded suna da saurin wayewa ga wayo da iya bi da mutane Khadija yoruba girl ce tana da jikin girma kuma farin fatar ta dan dai daine,jiya da muka fito lecturs naga yadda ta ware tana takun ta hankali kwance tana muamala da kowa tamkar wanda ta san london din kawai abun sai ya bani mamaki. Nikam ban wani sake jiki na ba,am shy and quiet,toh tunda dija ta gane hakan ta fara sani agaba tun bana so har na fara bin ta ina warwarewa She has been encouraging to chill,tace ki mance fa nan london ne ai kalar fatar nasu baifi namu ba,and you see this big girls da suka fimu jiki da tsayi duk sa'oin mu,turawa ai girman buredi ne dasu .. Nikuma na lura da suna da rainin wayo musamman yan first year ace sunga kai ba kalar fatar su ba. But still some of them are cool,wasun su ma basu magana da kowa harkan gaban su kawai sukeyi. And jasmine,ita kuma yar kinibibi ce ga shegen iya masifa da kadadi Shiyasa ma tun a satin mu na biyu aka fara sanin mu a ajin mu,duk wanda ya gaya mana baki sai ta fada masa jaja zir. Sau biyu tana tada hargitsi acikin filin aji Nice dai shirun acikin su,amma sabida ina da kyau sosai kuma na fisu tsarin jiki wasu students ma sabida ni suka fiye shiga harkan mu. Nidai Abunda ya sa na dada jin dadib tarayyar mu shine dukan su suna da kwakwalwa da kaifin tarbiya,ban taba jin sunce muje adult party ba,barin ma jasmine akwai ta da rike addini ita kuma khadija ta ta kere mu a a ilimi da baiwar gane karatu. After six weeks aka raba mu a activites,sai kowa ya koma yin asalin abunda ya kawo shi,amma da shike same level ne kusan tare muke fitowa sai mu hada hanya nu dawo dormetry. Su suka sa ni na dan ji dai dai,dan bamu komawa hostel wani bin sai munje yawo iri da iri acikin gari. A haka Har muka saba sosai aka fahimci juna. Dan idan nayi waya da jahan kuma suna kusa sai kaga sun karba sun gaishe ta. Bangaren junnut kuwa rayuwar ta is private,ita kadai ce a apartment din ta dan haka babu mai shiga harkan ta. At her age anan america sai bata fara tuka kanta ba,driver aka kawo na musamman wanda idan zata fita shi zai na janta ko ina. Haka take zuwa class ta zauna,high level girl babu ruwan ta da magana da kowa,ga wani irin shegun dreses masu dan uban tsada data ke sawa,she is alwys on 5inchs rock stud,ko designer sandal hills. Uwa uba heavy make up sai dai tana dan rufe gashin kanta da scarf. A schl din su sai ya zamto babu wanda take muamala dashi,sai da aka kai kusan 4 month kafin ta hadu da wata princess yar japan. Sunan ta princess hildah,sosai halayen su ya zo kusan daya Gashi itama yar gidan masu shine,dan bayan hildan,junnut ita kadaice student din da ake kawo ta school da exotic sport cars kamar su jaguar,aventador,benz sport,wani bin zakaga hilda harda tuko lamboghini. Toh Da ita kawai junnut ke fita Shan iska,da haka har suka dawo close allies Basu zuwa wani waje in wajen bai cika sunan sa na manya bane! Hilda it ta fara koya ma junnut dabiun saka tsadaddun manicure and pedicure irin su black and white diamond nails Dogayen atachement na human hair da clothing fashion styles na zamani kala kala,suna deban wankan su just