← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 173

Sashe 123

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace tsaya bahiyyar tazo.. junnut taji wani raas dn bata so haka ba but its a do or die affair kawai sai ta fuske har aka kirawo bahiyya cikin gaggawa Hjy indirah ta watso ma junnut kallo mai raxanarwa tace ehen munajin ki "Rimi rimi junnut ta sake gwamutso labarin Ahumaggah ajuye ta shiga musu fiye ma da yadda ta tsawwala al'marin agaban jahan khatun dazu Bahiyya dake jin kamar xata mutu bata san sanda ta fashe musu da kuka mai sauti ba,ta juya a rufe ta kalle junnut Sai taga junnut kamar ko ajikin ta jahan khatun nan ta sami daman yin diri sai dada kawo rashin mutunci take tana cewa badai su hada zuria da tsinanniya Bahiyya tasha mamakin junnut matuka har bari take tsaban takaici fushi da mamakin junnut... Tanaji junnut din tana basu shedan cewa aje chan garin su ayi tambaya in sunce karya take yi mata. "Tsananta kuka da firgici da Rashin cewar komai da bahiyya tayi shi ya sace ma su jahan Aarah gwiwa sukayi shiru..duka basu ce komai ba Anan Sanda jahan khatun ta gama azalzalar bahi da mugayen kalamai marasa dadin ji.... Tace Allah ya sawwake saood ya aure mace marar daraja irin ki,raped and cursed?...yar matsiyata.munafuka...god forbid kizauna acikin zuriar mu..ai dama daga ganin idon ki nasan kinsan maxa Ta wani dago fuskan bahiyya dake sunkuye jike da tears tace ai sai ki amsa kice karya aka maki ke ba ragowar ahumagga bace,kuma ba a tsine maki an kore ki a garin ku... "Bahiyya ta dago raunannun idanun ta kalle junnut tsawon minti uku suna kallon juna junut ta dauke kanta ta hade rai.. "Azafafe bahi tayi saurin mike wa zata fice awajen tana kuka idanun ta a rufe,tsaban yadda take jin jiri sai tayi kamar zata fado jahan Aarah tayi saurin taro ta ta rungume ta. Cikin wani irin sautin damuwa ,tsananin fushi da tausayin ta kankame ta tana cewa noor Ina zakije ne?Ai ba agama maganan ba..kiyi shiru ki barsu su karasa Ba part din su suka gaya mana ba?ran jahan Aarah bai taba baci irin na yau ba..tace ,'what make u think i will believe them ..koma hakan ne to sai me? Ue my doter..Ure a human being,u dont deserv embrasment and disgrace,in har ni uwace wajen ki ba wacce ke da ikon tuhumar ki akan rayuwar ki na da chan.. "Wani irin kuka bahi take tana shiga jikin jahan Aarah da wani irin tsumayin zafi da karayar zuciya numfashin ta har sama sama yake alaman abun ya taba ya sosai..atake muryan ta ya dishi gaba daya jikin ta ya dau xafi har bata so ta dago idanun ta ta kalle su Ahakan Abun ya mugun taba junnut amma sai ta daure ta danne zuciyar ta sai kananun tsaki take ita daya. Hjy indirah tayi shiruuu cikin naxari..can ta jawo bahiyya daga hannun jahan Aarah ta aje ta atsakiya A nitse cikin kwantar da murya tace Bahiyya...my princess,Wai dagaske ne hakan ya faru dake?Koko sharri akayi maki! Bahi ta dago ta kalle hjy indirah tanaji kamar zata fashe..sunkuyar da kanta kasa tayi,wani xuciyar nace mata ta tona asirin junnut din kawai Amma maganan abbun ta yafi damun ta ayanzu sosai "Sai tayi shiru Wani kundin tunani mai zurfi ta shiga "Meyasa junnut xata min haka..wannan magann Siriin mu ne..Alkwarin mu ne..ko a mafarki bata taba tunanin rana mai kaman ta yau xaizo ba Akan namiji?lallai junnut ta dauko abin da zafi kodai junnuut gaba take son muyi ne akan haka if nor mai zata gaining inta raba ni da rufin asiri na.. To nidai I will neva do that..he who breaks his promises is cursed. Dama Abbu na sanda ya gaya min haka kafin ya bar duniyan nan.. Toh In har junnut ta mance da rayuwar mu ni bazan mance ba. Jin bahiyya ta bata shiru atsakiyar su yasa Jahan khatun ta wani bushe da wata makahuwar shewa. Ayyuuuriri...... Ashe ma duk burgan banza ake mana wai yarta,kaga masu yayan arxiki,masu tarbiya suna shan mamaki halayen yayan nasu da suke boyewa.. Hahahah Allah kan hada mutum da abunda ya dace dashi,shiyasa ma ya bada kyautar tsinayyar ya ma wasu agidan nan. . Wasu zafafan hawaye suka sake saukowa kan fuskan bahiyya Kan ta hankara taji an wani finciko ta jahan khatun ce Babu kunya,jahan khatun tace zoki fice,ure dismised, saood zai aiko maki takardan ki,wanda suke son ki sai suje can dake ku karata amma ba agidan nan ba. Ta shiga jan bahi hjy indirah ta riko hannun ta itama kuka mai ban tausayi bahi take yi Sosai ran jahan Aarah ya baci,daga ganin yadda hannun ta take rawa zaka gane cewa bata so ne tayi loosing temper.. "Ki sake ta...hjy indirah ta tsawatar Amma jahan khatun bata fasa ba, Hjy dadagewa tayi ta fincike bahi ta jefo ta wajen jahan Aarah,wani saukan tassss jahan khatun taji akan fuskan ta sanda taji dauke ji da gani Wai Baki da hankaline?... Wai Ke wata irin dabba ce da baza kisan ya kamata ba. Roh Bahiyya bazata fice agidan nan ba kije ki gaya ma uwarkin karfi yaci daru ya danne.. Ni indirah,.. jinin hamood ba gayyar karare ba daga yau na saka dokan cewa yarinya bazata bar gidan nan ba kuma aure yau aka fara shi ko da kuwa Shaidan ne dakansa ya sauko ya tsine mata ba aljanu ba Hjy indirah,...ta rife idon ta cikin azaban masifa mai kada hanji...tace suwaye kuma ahumagga? ...Ahumaggan banza da wofi?al'adace ba addini ba,wannan ai ku ya dama mu bai dame mu Da kike cewa bata da daraja ke din kina da shi ne?. .a duniyan nan waye cikinsa baiya fitar da tusa mai wari ke inda za'a bincike naki rayuwar ai da ba haka ba.... Ni bana son hayaniya khatun maza ki kama girmanki,banda ma rashin da'a irin taki...yanzu rayuwar yarinyan nan ma saikunsa mata ido? Toh wa billahil aziman baku isa ba. Kuje kuyi duk abunda zakuyi ga fili ga doki saura sokuwa.. A haukace hjy indira ta isa bakin door ta mata nuni da waje tace out...cos u have overstayed ur wlcome..iskancin banza iskancin wofi Kuna abu kamar ba nagaba daku Wani kukan munafurci junnut ta fashe dashi ta dawo jikin jahan khatun da tuntuni ta kasa cewa uffan dafe da kuncin ta tana hurowa kamar bakar maciciya Wani kallon barazana ta bisu da shi,tawani girgiza kai cikin tsananin fusata tace zamu gani..ta fita junnut na binta a baya Masifa hjy indirah ta cigaba dayi bahiyya tana ta kuka dan bata taba ganin bacin ransu kmar na yau ba... Jahan Aarah da tuntuni ta daskare cikin bacin ran,ayanzu babu abunda take yi sai imagining labarin da junnut ta bayar akan bahiyya... Ta juyo zata tuhume sai taga bahiyyar ta iso gaban ta da sauri ta zube gwiwar ta akasa gwanin ban tausayi ta hade hannun ta biyu cikin matsanincin kuka tace'...dan Allah kiyi hakuri mumy...kiyi hkuri ban boye maki wannan maganan da wani nufi ba.. Jahan Aarah tana da tausayi sosai,ganin bahi ahakan na balain sosa mata rai sai ta yunkura xata dago ta ta rungema ta Hjy indirah tayi saurin dakatar da ita da ido... Hjyn Ta karaso cikin yanayin mata fada tace baki kyauta min ba nooor... Ashe bazaki gaya mana dukkan labarin ki ba..?yanzu meye amfanin hakan da akayi maki....kinji dadi kenan...what else are u hiding from us.. "Bahi ta dago hawaye nabin kuncin ta har muryan ta na rawa tace, wallhy Babu komai small mum iya wannan ne kawai ban fada ba Kuma akwai dalilin yin hakan dan Allah kuyi hakuri ku fahimce ni Jahn aarah ta daure tace dagake takeyi wai anyi raping dinki?..kuma aljanu sun taine maki an kore ki..bahi tayi shiru can kuma ta dago ta kalle jahn arahn tace " Eh,an kore ni akan laifin hakan amma wallhy ni babu wanda yataba raping dina"its a conspiracy"..dan mu taimake rayuwar juna muka kulla shi..sai ta dan kalle jahan muryan ta na rawa tace ..mum u can check me up if u want. "Nasan babban al'amari ya faru aranar,amma Wallhy siriin mu ne. Da ni da junnut da Abbu mu kadai muka san gaskiya Mum Nayi ma mahaifina alkwari maii nauyi akan haka ...wanda aganina b tsananin wahalan raywr mu ta duniya bai kai ace mun saba alkwarin mu da iyayen mu Ure my parent now,..sam Banji dadi daya kasance nice zan jawo maku bacin rai da abun magana ba...kune kuka rufa min asiri wallhy farincikin ku shine abun alfahari ne,kuyi hakuri nasan baiyin dai dai ba ...inda halin kuyafe min...a hankali ta share hawayen ta tana jan shesaheka.. Dago ta jahan tayi gaba daya itama idanun ta sun cicciko da hawaye Dukan su kallon ta sukeyi Hjy indira ce ke jin ta yarda da zantukan bahiyya babu kokwanto ko shakku,bare aje ga jahan Aarh dake matukar jin koda gaskiya ne hakan ya faru da ita bazata taba tozarta rayuwar bahiyya ba.. Suka zaunar da ita a tsakiyar su cike da lallabi da kalamai masu sa karfin gwiwa,suna bata asurance din cewa komai ya wuce awajen su sannan muddin suna raye zasu taya ta kare alkwarin data dauka ma mahaifin ta.. Nasiha hjy indirah ta mata sosai tana gwada mata cewa wani dan adam ko Aljani bai isa da rayuwar ka ba sai ayadda Allah ya ga dama Bisa ga magann raba aure da jahn khatun keyi,jahan Aarah ta dan danne kunya ta tambaye ta tace kun sasanta tsakanin ki da mijin na ki?.. Bahi bata da option ta gyada kai a kunyace itama..duka suka sa mata albarka,har site dinta suka sa aka kaita.. Tana isa bata duba khal ba tukun sanda ta shige dakin ta yi ta kuka tana tuno da maganganun mahaifin ta tare da abunda junnut tayi mata. Da kyar ta dadafe ta kai kanta bathrum ..cusa fuskan ta tayi cikiin shower,..ruwa mai sanyi yana kwalala daga dukan fusknta izuwa jikin ta tana sauke numfashi,sanyin ruwan ne ke taya gangan jikin ta sauke rakin sa.. Tana gamawa ta dauro alwala ta kai 2 hrs tana karatun qur'ani cike da daukaka muryan ta Tuni sanyin niimaar Allah ya wanke xuciyar ta tasss,sai ta mike taje dakin shi.... turo kofar ta keda wiya ta same shi shima yana kan dadduma yana ta
Chapter 123 · 0% Book details