← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 173

Sashe 40

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

iya nuna alaman komai fuskan sa ba,sai dai yana da tabbacin cewa ba lallai ne ya so abunda suke so ba. Gefen junnut kuwa tun safe da tafito daga shashin motsa jiki ko sport wears din bata cire ba ta nufi site din kaamil,its private dan haka acikin ruwan wani katoton pool dake bayan apartment dinsa same shi,sai ta zauna a chair suna hirar sirrin su "Kaamil dirarren namiji ne,fari mai mugun son kara'i, shi babu ruwan sa da komai kuma dai duk abunda zaiyi da yan mata har yau ba ayi macen da ta burge sa har yaji ta sa masa sha'awar aure ba Ko da yaji ance ma khaldun za abada junnut,sosai ya gode ma Allah dan shikam har cikin ransa ba sosai yake ganin zai iya cigaba da biyayya ma dilshad da dad din su ba "He likes beign free ya tsani abun takuri arayuwan sa,ita kuwa junnut badon ta riga ta ga zabin da dilshad tayi mata yafi ba, da ko kaamil akace ta aura ba zai dame ta ba Shima irin mijin datake burin aure ne,ga shi da kyau,naval captain uwa uba dan kara'i ne. Ya kanyi harkan sa da duk wacce ta masa but just for flirting sake,akan party da mata kaamil zai iya kwana baiyi bacci ba. Sai dai in ka ganshi ba lallai ka gane hakan ba,most of times sai yana hutu yake ballewa, sannan shii babban soja ne to inda yake shiga yayi karain sa ba waje bane na zuwan kowa da kowa. A us wani bin ko junnut bata iya binsa party,inta gansa da matan turawan nan somtimes she just wonder how And Why har yau kaamil baijin sha'awar yin aure. Anan dai tagama deban lectures dan ya gaya mata duk wani salon da zatayi muddin tana so tayi magana mai tsayi da khaldun. By 10 in the morning lokacin an tabbatar da kowa ya kammala breakfast din sa Kowa yana expecting yaga khaldun ya futo cikin dressing mai kyau da nuna kasaita ko burgewa,amma sai gashi ya fito cikin simple white jallabiya wanda hatta takalman kafar sa plain ne. Zaman sa yayi kusa da dilshad wacce already ta sa an kere wajen ya haska sosai ta inda duk wnda zai shigo zasu ji dadin kallon sa Chan sai ga kaamil shima ya shigo bayan ya gaishe ta direct ua dawo gefen bro dinsa wani murmushi suka sakar a tare don A ko yaushe suka jalle juna ji suke kamar mutuwa ce kawai zata iya shiga tsakanin su. Anan daki kuwa jahan ne a tsaye tana dada jaddada ma junnut abubuwan da ya kamata tayi domin ta samu karbuwa wajen khaldun Gashi har ta fara dagowa cewa junnut ta riga ta shiga zumudin soyayyar khaldun tun ma bata gansa a ido sa ido ba Toh aya kenan zata dauki wannan risk din auren wurin bayan tasan irin zaman da suke so junnut tayi a gidan khaldun Ba abu bane da zasuyi wasa da shi. Bisa ga wannan dalilin jahan ta yanke hukuncin dada ganat da junnut. Tun kafin ta fito da ita sai ta nuna mata cewa ita asalin burin ta akan ta shine sai ta kammala karatu ta rike abun kanta kafun ta shiga rayuwar aure da khaldun. Anan ma Sosai junnut ta fahimce ta sabida dama abun na ranta itama sosai kuma ganin bata kai inda take so takai arayuwa yanzun ba shiyafi saka mata fargaban fuskntar sa ayau Jahan khatun Tasan sarauniya dilshad tana mugun tsoron lamarin ne, Kar suyi sanya ne abun ya xo ya kufce musu shiyasa da chan ta matsa sai anyi abun yanzu . ****** Da asalin sumar kan junnut aka mata nadin kwalliyar jeweries din gold yan dai dai masu kyaun gaske. Kayan ta fitted mermaid gown ne brown mai tail har yana dan jan kasa dakansa sai dai kwalliyar manyan mata aka kwaba ma fuskan ta wanda yaso ya karkata kamannin ta baki daya. Sanda zata shigo har wani sanarwa jahan ta sa akayi,bayi shida ne suka rufa mata baya tana taku kamar bazata taba kasa ba,duk dai tayi musu kyau amma khaldun baiji abun yaje masa ba Tana zama tayi gaisuwa su jahan suna yabon ta,..duk dama kirjin ta dukan dari dari yake amma haka ta daure bata ko kalle sa ba Shikam idon sa ya zuba ya kare mata sama da kasa ...She's not bad huhn? Sarauniya dishad kuwa sai kallon sa takeyi tana so taga ko zata gane wani abuda da suka hade ido da shi Dan Yake khaldun din yayi sai jahan tayi gyaran murya. Nan ta gabatar masa da junnut matsayin wanda zasu aura masa,and right from tarihin ta da matsayin ta acikin su baa rage masa komai ba sannan ta nuna cewa a matsayin ta na uwa ce tayi masa wannan zabin kuma hakan shiyafi dacewa da shi. Shikam Ba tantama ya amsa tare da nuna biyayyar sa. Sosai dilshad taji dadi duk wani fargabn ta dai ya yanke Nan tayi umarni akan a basu waje domin su gana tsakanin su Kowa na fita Wani shiru ne ya dauki wajen tsawon minti talatin junnut bata dago kai ta kalle sa ba shikuwa ya sa wayar sa agaba yana latsawa kamar ma baisan da ita ba Hakan ya dada cusa mata fargaba a ranta amma sai ta fuske ta cigaba da shiru abun ta ...sai chan wani dan karamin tari ne ya shake mata wuya a bazata datayi sai taga ya dago ido ya dan kalle ta,... Wani dauke kan jiji da kai tayi da sauri tana jin nauyin idanun sa,and she honestly cannot believe that duk uban shirin datayi akansa zai zamo banza lokaci guda ba..hes is sooo hot and everything she eva eva dream of Data kare ma Kyaun shi da kasaitar sa kallo aranta sai taga kamar dama chan labarin karya ake mata 'The way she see him now,sai dataji ta raina ma kanta ga wani shegen mahaukacin kaunar sa mai zafi daya cakke kahon zuciyar ta ayanzu Gashi yaki cewa uffan ita kuma a yanzu ma kwakwalnta gaba daya ya shafe bata ma son ta furta wani abu ta kwafsa ta fiso sai ta sami cikakken nitsuwa. da taga dan tarin datayi dai ya ja hankalin sa sai ta cigaba da kwalowa cikin salon basarwa. Bata ma sani ba taga ya tashi ya fita,a bakin kofar fita yaga maid tana tsaye batare sa ya kalle ta ba yace get her some water daga nan yabar sashin bai sake duban inda take ba. Itama tsaye ta mike ta Wani sauke ajiyan zuciya,gaba daya damuwar ta bata sane zata ce masu jahan ba insuka tambaye ta,zaman kurame akayi sai dai kowa yasan fuskan kowa yanzu Haka dai ta cigaba time to time ana hada su suna ganawa amma iya haduwa in zatayi khaldun baiya ma kallon ta sau biyu bare ya tanka ,daga nan jahan ta samu daman saka nata ra'ayin,har dilshad ta soma daga kafa sosai musamman da junnut ta nuna kasawar ta wajen ja da hidimimon khaldun.. Ta dai yarda da shirin tsafin da su kayi,a duk dama bata fara ganin wani positive action ta fannin sa ba Jahan khatun tace Matsalan su rashin sabo ne Kawai sai akayi akan koda junnut taje schl a us in saood ya dawo zata na zuwa masa hutu kamar dai yadda take ma kaamil Kwanan sa tara a kingdom amma Da kyar junnut ta fara gane kansa,duk iya rigimar ta da iya kasaitar ta bata kamo setin tashan khaldun ba har sai da kaamil ya fara musu yar qwari qwari. Shi zai hada dinner ko wani game sai ya yi inviting dinsu su biyu yana dan ja su da hira Anan har tasan cikakkrn sautin muryn sa Da hakan har kaamil ya samu suka fara magana kadan kadan a tsakanin su,sai dai fa matsalan junnut shine tayi saurin zumudi wajen nuna cewa ita wata ce. Karama da ita amma She is always on high Fleeky Make up ko games zasuyi bazaka ga ta bar natural beautyn ta afili ba,ga fiye tsadadun kaya da son nuna ta waye bata san kuma hakan shi yake dada sa khaldun jan baya Da hidimar ta Dan kyau kam shima ya yaba,har yana jin alamun zai iya rayuwar aure da ita,da alaman kuma wannan wankan maganin nasu ya dan taba shi... 15days kacal sukayi anan din,amma sai ana saura kwana uku su zasu tafi kafin junnut tayo abunda ya dan bashi mamaki A ranakun sai ta aje girman kanta tana kokarin jansa da surutu ko yaki ko ya so,ranar har tasa shi suka je garden din ta tare Suna Zagawa sai yanzu ta samu daman amfani da duk wani strategyn da kaamil ya fada mata wajen magana da shi.. Akwai gajiyarwa dan kuwa bata taba ganin murdadden gaye kamar shi ba Da zai tafi Haka aka tsayar da magana cewa,khaldun na junnut ne and when the time is right za'a yi musu proper royal weding betrothal... A yanzu junnut tana da phone number sa amma da shike kaamil ne ya saka mata awayan shiyasa bata taba dialing ba, gashi tunda ta ganshi bata iya wani bacci mai kyau bata yi imagining din rayuwar aure ta da khaldun ba,hade da burirkan ta na nan gaba kuma sai take ga tafi kowace mace sa'a a duniya Bayan kwana biyu da tafiyar su A kullum sai ta tambaye kamil taji ko khaldun yace wani abu akanta amma sai shiru. Shikuwa khaldun yana sane da duk abunda take ciki,dan yana da wannan baiwar, iya kacin kure sa shine ka tafiyar da rayuwan ka batare da son nuna saika burge sa ba. Shidai bai wani damu ya aje contact din ta a wayar sa ba,don tun aranar da suka bar kingdom din kowa sai ya koma inda ya fito sauran ayyukan sa su suka sha masa kai kaamil din ne yakan tsula mata karyan cewa ai khldun yana kiranta baya samun ta ne shiyasa take jin sa shiru,a haka har ya sa ita da kanta ta neme shi a waya sau daya suka gaisa daga karshe ma Bai yi saving din ba Aganin sa muddin wani abu ya taso masa na dole ya kira ta,a ta wajen kaamil yake sa ran samun hadin kanta basai
Chapter 40 · 0% Book details