← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 173

Sashe 8

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

irin bright yellow skin mulmulalle mai haske da laushi irin marar fidda kurji ko tabo din nan. "Dama Abbu da ammu na farare ne,dan haka na dauko yalalen gashi mai tsayi irin na ammuh, tsayin ta da dirin jikin ta ma kai komai nata na halittar jiki ban bari ba. Idanu na ne kuma na dauko na abbu na dan shima kwayar idansa kalar ruwan tokace irin na aishwryr,gashi thy are well rounded and sunken su dai basu yi girma sosai ba, dan madaidai ta ne Wanda tsayi da cikowar eyelashes dina ya dada kawata su ya bani wani shegen fierce look. Nidai Na kasance wata madubin dubawa dan ko babu kwalliya nasan ni mai kyau ce. Anan kuma kyauna ya jawo na sama mana kasuwa sosai kamar ba nice aka ce aljanu sun Tsine min ba. sai dai bana da son cika magana, hasali ma Tsaban yawan shiru na da kamun kai yasa anty hanne ta yarda dani sosai,yanzu awajen ta nake samun kariya da cikakken tsaro daga komai, har da maza yan iska da kuma kawayen ta karuwai yan madigo. Anty hanne ba musulma bace anma tana da dabiar daraja dan adam, akalla dai she is in her late 40s tana da dan shegen data haifa sunan sa chris,to tunda ta haihun sai ta bar sana'ar karuwancin kwata kwata sabida tasa tunanin rayuwar dantan anan gaba. Amma sai bata bar bayan garin ba sabida sana'ar da ta bude na saida abincin domin anty hanne karshe ce wajen iya dafe dafen abinci,wani salon girkin abincin ma koya take yi a online kuma duk iya wahalar yinsa Sai ta koya kuma kaga ta iya tsaf Sana 'ar ya karbe ta,dan Akallah itake da babban shagunan dake ciyar da kowani mahaluki da zaizo wajen Dama chan Kowa yakan so abinci ta,Toh tunda nazo sai abun ya dada bunkasa,har daga wajaje daban daban ana shigowa neman abinci wajen ta," Tana mutun ta kowa amma Da zaran ka nuna kai mayen mata ne sai ta bata rai ta kora ka. dan kuwa har yau anty hanne bata gaya ma kowa cewa ni ba kowa bace illah marainiya. Asali ma cewa take ni yar uwan ta ne nazo daga kauyen su.. Itama tana da kyau dan kuwa cikakiyar shuwa arab ce daga maiduguri amma mahaifiyar ta yar garin katsina ce. Kamar uwa haka ta zame min,girki da sarrafe sarrafen abinci babu wanda take koyarwa fiye kamar ni. Idan muna aiki tare sai Tace min kar nayi samari har sai na tara kudi na nemi ilimi mai zurfi.. Hakan kuwa har fara saka wa araina sai na zage sosai ina aiki,ita kuma tana aje min kudin har na koma wanu makarantar gwamnati ina dan cigaba da karatu na. A ss1 suka sake maida ni,amma danayi term daya aka gane ina da hazaka sai aka cilla ni aji biyu na Kafin ace shekara ta zago na waye tar har turancin broken din nan na iyashi sosai kamar dashi aka haife ni Sai dai a rayuwa nafi bada aikin anty hanne muhimmanci dan ko makarantar na shirya zanje, inta aikin saisa abinci ta kama nakan iya ajiyewa na rana guda don kawai na kula mata da business din ta, Sosai ta rike ni kamar jinin ta,itace tayi sanadiyar kwace fuskan maraici da damuwa acikin zuciya ta Sai nake ganin to meye a duniya nan wanda bazan iya mata ba?. Gashi Yanzu Na kanje wajaje dayawa aika,banki, kasuwa da sauran tsabgogin business, domin a shekara guda danayi anan kasuwan cin anty hanne ya dada habakan da yasa ta bude shagon saloon na mata ana mata service din pedicure and manicure. Tsaban gatan da tayi min sai ta barni ina zuwa chan ina raba kafa ina tayata aikin manicure idan na kammala saida abinci na,musamman wekends da bani da makaranta Kuma duka aiki biyu tana biya na. At 15years jiki na ya dada bayyana kyaun sa na ban mamaki... Girman da ya dan bayyana a kirji na ya shiga ruda mazan banza har na fitan hankali A ciki kuwa harda saurayin anty hanne wanda ta kama da kyar kwara daya akan shi zai aure ta ya rufa mata asiri. Shikuwa brother felix tunda yaga na habaka sai ya samin kahon zuka. Tun abun baiyi tsamari ba har masu jin haushi na suka dauki wannan daman suna kai mata gulman cewa na fara girma zan kwace mata manemi. Kwance tashi har anty hanne ta fara sauya min fuska, .nikuma sai na dauke wuta ma saurayin nata dan ko gaishe sa banayi Yanzu Duk da haka ban tsira ba,don a ranar da ta gane cewa asali ma baiya da niyyar auren ta dan Kudin ta yake so yaci sai taji haushin sa har sukayi kaca kaca yaje ya sha giya ya bugu sosai.. Gashi dama shima a gidan mu yake kwana tare da anty.. To daya shigo Maimakon yaje ya bata hakuri sai ya taho dakina ya farmin da niyyar yimin fyade. Ihu nayi masa ina kwarwa Ita kuwa anty hanne data fito sai ta hada har da kishi da rudewar tunani ta hada harda ni ta kora mu a rayuwar ta. Ranar Nayi kuka sosai,dan kuwa na fahimce ta itama sosai ba a son ranta tayi min haka ba sai du su arna dama basu cika daukar qaddara mai muni a rayuwar su ba. Tasan babu laifi na,amma sai tasa aranta nice sanadiyar rabata da mijin data sha wahalan samo shi don ya rufa mata asiri ya aure ta Ni kaina na fahinta wato samun miji Ba abu ne mai sauki wajen tubbiyar karuwa ba Dan haka na yi tafiya ta uwa duniya a duk dama bansan ina zanje ba. Kaya na da kudin aiki na da anty hanne tabani sune kawai a hannu na danko wayar salula bani da shi. "Kwaryan Garin kaduna na shiga ina browsing ko ina da idanu na,Tun bana son kashe kudina har nafara tabawa Daga inci wannan sai inci wannan Wani abin ma da kudi na amma da kyar na samun wajen kwana mai mutunci. Kwana biyu kacal nayi ina gantalin neman mafita makaina kwasam ranar sai nayi dare a wani hanya.. Dama wani hanyar nake bi idan zan shigo gari to bansan cewa ana fashi awajen ba sanda nayi kuskuren shiga cikin su har hukumar tsaro suka kama ni cikin rundunar yan fashi.. Naci kuka kamar zan fidda raina amma babu wanda ma ya saurare ni Haka aka kulle ni har tsawon kwana 10 Wanda Da kyar da wahala na fitar da kaina,Anan kayana da kudi na suka salwanta suka bace na dawo daga ni sai ikon ubangiji na. Gefen wani dakali na zauna Damuwa sosai ya fara shiga raina Gashi Tunda aka sake ni a station ban ci komai ba ga yunwa ga tashin hankali gashi gaba daya na rasa gane ina zanje guda daya domin ataimaka min ko da na kwana koda zuwa gobe na nemi mafita. Haka na ta zaga garin kaduna da kafata ta karshen ta a wani babban masallaci mai site din mata da maza na dan rabe Juyi kawai nakeyi,kalar tausayi inda yunwa da bakar gajiya ya riga ya galabaita ni kwance tashi nake kamar taliyar dayaji ruwa, gashi ni sam ban iya roko ba. Duk sai na rasa meke min dadi A duniyan nan,baccin ma yaki zuwa sai dai nasha ruwa nayi sallah. Chan dai da yamma yayi sosai inata murkusu su saiga wata mata kanar daga sana ta taho da awarar ta leda mai zafi yana buso qamshin dadi sai kuma Tayi min tayi da fara'ar ta.. Ni kaina nasha mamakin kaina dan ko irin Ja din nan banyi ba n tsoma mata hannu na fara deba bibbiyu ina kaiwa bakina cikina dayaji saukar abu mai dumi har wani kugi yake shi kadai daga bisani matar sai ta tsura min idanu kawai tana min kallon anya lpya kuwan.. "Ban ma lura ba sai da na farga daga abun dana keyi,sikini na sauke kaina kasa cikin jin kunyar ta har Hawaye naji na neman kufce min,sai na maida su dai na yi controlling kaina cikin dabara na tsame hannu na pretending to be ok! Matar Ba yadda batayi dani nacinye ba amma haka naki fir harda mata karyan cewa zanje gida dama jiran lokaci nake yi.. Sai nayi mata godiya Tace toh bakomai hakan yasa na tattara kafata bayan isha'i na tsaga dare na cigaba da tafiya.. A Duk sanda na tuno da abun da ya faru dani a hannun polisawa da barayi sai naji tsoro ya taba ni sai nayi sauri na nemi gefe na zauna, Chan kuma sai na tashi na cigaba da tafiya kamar na mance Acikin daren har Wani unguwa na kai kaina bansani ba,wajen kuwa shiru ne babu hayaniya daga ji kasan anguwan manya ne. Normally nabi kan shimfidddiyar titin na dan sauka cikin wata siririyar hanyar data bi bayan anguwan ni kadai ina tsagawa kamar wata mayyyah don ko fargaba bana ji buri na na samu wajen da zan dan fake zuwa gobe amma har yanzu ban gani ba sai ma dada zilma kaina cikin ciyawa nake yi Ina dada kaiwa ciki bayan wani anguwa,sai naga duhun dake gabana ya dadu yayi yawa,tsoro sai yasa ni kawai na tsaya ina tunanin kar nabi hanyar nasake jefa kaina cikin wata masifa. Gefen wani old abandoned mtn stall na zauna na rafka uban tagumi.. Anan Ko minti biyu banyi wani rudadden kara ya firgitar da ni sai da na fada kasa na toshe kunne na. Karar kamar na bindiga ne amma banga kowa ba tukuna Wani rawa jiki na yakeyi shikadan sa Da kyar na dawo hayyacina anan ne ma na fara jin sautin Maganganu sama sama a kusa da ni,da wani uban speed kirji na ya kara bugun shi Sai nayi saurin labewa da kyau jikin shagon,nasa ido ina kalle kallen hanyar da zanbi na arce na bar wajen acikin hanzari Ina kuwa saka kafata zan gudu sai naji an dafa ni... Numfashi na ne ya dauke chak, Daga juyawa ta sai naga mutumin daya dafa nin ya sulale kasa ya fadi jikin shi da gefen kansa duk jini.. Da sauri na tsunguna akansa 'na tsura masa ido sai naga yana kwace idanunsa da kyar yana min alaman na taimaka mashi.
Chapter 8 · 0% Book details