Sashe 4
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fara min bayani a tsanake don kuwa yau babu fuskan wasa a tattare da ita. Tace"Yan uwan mama na ne daga chan wata kasar zasu zo,ummah surbajo tace awajen su zan koma zama na har abada, bahiyyah ance suna da dukiya da duk wani abunda zaisa buri na na rayuwa ya cika kinga bama sai na tafi da gado na ba,wai dama jira suke na kai sha hudu ko sha biyar sai suzo su tafi dani.. Ruwan daya taru min a idanuna na sake cikin sanyin jiki nace dagaske kike yi junnut? Gyada min kai kawai tayi Wasu zafafan hawayen Junnut ta fashe dashi ta rungumeni, sai gashi jikin ta duk yasaki yana neman fara rawa nima Bansan sanda na kankame ta na fashe da kuka ba. Rungume da juna Sai da mukayi mai isar mu kafin muka rarrashe juna,nan junnut tayi min alkwari cewa ko ta tafi bazata taba mancewa da rayuwar da muka gina tare ba Don sanadiyar burirrika irin na junnut nima naji ina son nayi karatun baturen nan ko dan na taimaki abbu na, a duk dama bani da buri masu yawa irin na junnut,Nima Alkawari nayi mata cewa bazan mance ta ba,haka ma nace ni zan zamto mata mafaka na farko wajen ganin ta cimma burin ta duk rintsi duk wuya. Tsananin amintar dake tsakanin mu yasa nake jin kamar duk wani cigaba ko karuwa da duk wani al'amarin rayuwar junnut nima nawa ne. Gani nake kamar mani zataje tayi sabuwar rayuwar data samu achan din. Haka dai muka waske da kyar muka goge hawayen mu cikin karfafa ma juna gwiwa har muka isa kofar filin wasan samari da yan mata da aka saba yi.. Da mamaki sai ba muga kowa ba don yamma ya fara rufawa sosai waje yana neman yin duhu Junnut ce ta yi tambayar meya faru taga nabu kowa a fili yau,sai ake sanar da mu cewa ai yau din nan sarki modibbo ya sake SABBIN samarin AHUMAGGAH a daji don haka ne yasa kowa ma ya shiga gida da wuri.. Tabe baki kawai mukayi muka juya muka dauki hanyar komawa gidan su. Muna tafe muna hira,nake cewa junnut ni Sam al'adan nan bata burge ni. Sai Tayi dariya cikin raha tace akan me? don sosai muke da samari kala kala masu crushing akan kyawun halitar mu,junnut farar fata ce,sai dai ita tana da pale brown eyes ba irin nawa daya kasance grey ba!..,sosai tsarin halittar mu ya kere idanun dul wani maigani,dan tun tasowar mu samari ke buga kansu akan mu wai suna son mu. musamman ma ni da ban cika son abun ba,muna cikin hirar ta mu sai junnut tace mon "kodai kin dade baki fito dandali ba ne gashi yau kin fito gayu basu nan ko? ....hade rai kawai nayi sai naga tayi dariya Tun kan na amsa tace kar ki damu tunda bamu samu wasa ba sai muje gidan ku na yi sallama da abbu halan gobe bazan samu zuwa ba. Dadin jin hakan da tace yasa ni murmushi kawai Sai Muka dora niyyar tafiya wajen abbu Hiran burrrikan ta take min nima Ina kan jadadda mata yadda raina yaki jinin al'adan Ahumaggah akan haka kuma dariya kawai take yi min. Wato shi AHUMAGGAH wani babban al'adace ta wasu jinsin fulani. wanda zaka ga yaro namiji tun yana jinjiri ba za'a mishi aski ko kaciya ba sai ya kai sha biyar ko sha hudu,ko ma sha shida. Nan sarkin gari,da matsafa da aljanun sa zasu tara wayannan samaruka a tsuma su da tsumin aljanu, sannan akai su jeji abasu jawadin tsawon kwana bakwai batare da sun fito gari ba. To Cikin wannan kwana bakwai din ake saka ran duk wani yaranta dake kansu zasu aje shi ajejin. Da zaran kwanaki bakwai ya cika sun fito sai ayi musu aski kaciya da aure. Sai dai kuma mummunan abu da samarukan AHUMAGGAH shine kwana bakwai ajejin nan da sukeyi babu abunda suke ayyanawa sai rayuwa iri na dabbobi da jahilai. Da rana zasuyi fashi ma duk wanda suka ci karo da shi. Idan budurwace haka zasu yi layi su kwanta da ita suyi mata fyade. Haka ma idan matar aure ce zasu zabi daya daga cikin su yayi zina da ita. Bayan nan yankin ance Akwai masu wannan al'adan Achan kasar nigeria cikin wani kauye a garin alkaleri a bauchi state. sai dai su al'adan su basu hade shi da dokokin tsafi da aljanu ba. a wannan jinsin fulanin kuma aljanu da bokaye kusan sune ma hukumar al'adan. Dan kuwa akwai doka mai tsanani na cewa. "Duk budurwan da ta ci karo da Ahumaggah har yayi mata fyade toh za'a shafe ta daga zuriar,a kuma a jefe ta da baqin cursed na aljanu. Thy believe idan saurayi bai fita a kwanakin Ahumaggan sa ba ya sadu dakai tamkar bada jinin ka ne ma shedanun aljanu ne. Matan aure da abun ya shafa ma jefe su akeyi ko akashe mahaifin ta a shafe ta a zuria.. ****** Ahakan Har muka iso gidan mu bamu bar musun hakan da junnut din ba. Ita kam ma abun bai dame ta sabanin nikam dana kejin da ina da iko da na sa an dena yin shi a doron kasa. Gani nake wannan jahilci ne da rashin tsoron Allah. No wonder sarki modibbo da bokayen sa,gaba dayan su basu shiri da iyayen mu, haka ma naga sun tsani umma surbajo sosai..har wani suna wai kadangariyar bariki suke kiranta da shi Sabida shi sarki modibbo babban jahili ne babu arabi babu boko sai tsafi da neman arziki wajen aljanu dan bunkasa mulkin sa da kasuwancin garin sa. amma iyayen mu sun nemi addini da ilimin bature dai dai misali a wajen larabawan egypts da kuma yan china dake shigowa kasuwanci ta boader somalia. Dan haka ne ma rayuwa ta nida junnut ba dai dai yake dana kowa ba.. Wayewar mu basira da ilimin mu a fili yake nuna kansa. Tun daga bakin kofa muka doka tagwayen sallama Muka shigo Amma sai Shiru kakeji tsakar gidan gaba daya babu bakowa,sai nace junnut ki shiga daki ki same abbu ni zan sa mana ruwan alwala Tace min toh ta saka kai Niyyata su gaisa idan tayi sallah Nake son na rakata bakin hanya ta koma gida Ina sane da cewa Umma surbajo bata son ta cika dadewa a waje musanman ma da naga har waje ya yi duhu yanzu magrib kuma ya shigo. Shigar junnut dakin keda wuya na kafa kai Ina famar hakar ruwa a tulun bakin rijiya.. Ko ajiyan numfashi ban yi ba wani irin firgitaccen karar ta ya dake kunne na wanda ya sani sake butar danake shirin kai hannu na na shigo cikin dakin mun aguje. Junnut lpya? Bata amsa ni ba A durkufe agaban abbu na same ta 'Abbu..abbuuu.... Abbbuhhhh..cikin firgicewa ta riko rigar shi tana fada kamar zata cire ranta da kuka,sai yanzu na na lura aman jini yake,duk yayi malala a a hannun ta tana famar jijjgashi Nima durkushewar nayi gaban ta muka shiga jijjgashi muna tallafoshi ba shakka ciwon zuciyar sa ne ya tashi gadan gadan. Kukan rudani duka muka farayi musamman ma junnut da shike tafi ni sanyin zuciya. da naga hakan bazai ficce mu ba,sake mata shi nayi daga bisani na mike tsaye na fito tsakar gidan neman maganin shi daya hada yake sha a kwana biyun nan. Kwaryan shan na rarumo Sai dai kashhsssss maganin dake ciki bai kai ko rabin cokali ba. Haka ma Duk iya bin cike munyi nida junnut amma ba muga ragowar sa ba. Haka muka yi cirko cirko akansa muna neman mafita,ga shi dare ya rufa ga shi Hankalin mu a matukar tashe yake ganin halin da abbu yake ciki dan aduk sanda yayi tari gudan jini ke fashewa yana kuma fetsowa.. Karshen ta barin san nayi da junnut adaki tana ta kuka sai nayi kokari na sulale a zuciye na fito na bar gidan na kama hanyar jeji. Tafiya kawai nake buri na naje cikin dajin ko zan samu na kalato magani abbuna ya sha ya rayu. Karewar Maghriba ya shiga sosai donko gaba na bana gani sosai danake tafiyar But I was so dertemined,ko ajiki na zuciya ta arufe take kuma duk wata alaman tsoro na kau dashi. Sai dai Ko rabin jejin ban tsaga ba naji takun mutum abaya na ina kuwa daga ido naga aminiyata junnut faca faca alaman biyo ni tayi. Abun ya bani mamaki,tambayar kaima nake anya junnut tasan hatsarin dake cikin wannan lokaci kuwa?.. A zuciye Nace junnut?baki da hankali ne zaki shigo jejin nan cikin dare?Idan wani abu ya same ki fa me zaki ce.. A take Tace min oho Share ta nayi na taho zan maidata gida ta fauce hannun ta Kallo na take yi Don Tsaban zuciyar ta ya karaya Cikin wani birkitaccen kuka Ta tsare numfashi na da cewa wai ena ruwan ki dan nazo,wato so kike na barshi ya mutu ko bahiyya? Abbu mahaifina na ne nima kuma Bazan zauna ina kallon shi cikin wannan azaba ba.. Kuma Dole ne na zo na taimake ki mune masa magani..hada ranta tayi ta kame Bance komai ba,dan Hawaye ne suka sauko minbina sharewa dana ganta ahakan sai naji na damu da safetyn ta sosai I wish dat bata zo gidan mu yau din ba ma,a haka ma ban bari ba duk iya musu munyi akan ta koma gida kan abbu Amma haka fir junuut taki. A haka na hakura mukaje cikin jeji neman maganin tare. Bamu samu irin ganyen da wuri ba dan munkai kusan rabin awa muna dubawa.. Sai da mukayi nisa bamu sani ba,Finally junnut ce ta gano shi ta nuna min,dan kwazazzabi ne yabi wajen sai na mika hannu ina tsinkawa tana tara min a fallen rigar ta "Mun ko debo isasshen a Kai hannu na na karshe sai naji an chapke ni,a tsorace na shiga fixgewa sai dai kuma lyaki sakowa.. Wani kara nasake Cikin radadin murdamin hannun da akayi Kafin Junnut tayo kaina,nadaga ido sai charaf mukayi ido hudu da saurayi AHUMAGGAH.. Wani uban Ihu na tsala nace junnut ki gudu ga Ahumaggah..cikin rudani da rawan murya tace Ahumaggah? Wani ihun na sake tsalawa..ko da junnut zata firgita ta gudu amma ina sai naga batayi hakan