← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 173

Sashe 171

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fara venting anger ta tana ihu tana kara gaya musu abubuwan da su kaji cikin jefo musu rudaddun tambayoyi Sosai jahan khatun ta firgita ga junnut ta dada fashewa da kuka tana bayyana alaman rashin gaskiyar su afili Wanda Hakan yasa Jahan khatun ta rasa bakin karyata komai kawai sai ta shiga kama kame Wani Kuka mai sauti da radadi da kaamil ya rusuna akan giwar sa yana yi shi ya dada hargitsa zuciyan kowa. ko shii alhaj hamood bari yake kamar inya shako mutum xai kashe shi Xaka sha mamakin yadda subaya take masifa untop of her voice tana wasu irin xagi da ihu ma jahan khatun ko bakin anmsawa bata samu ba Tuni wajen ya rincabe da koke koke,alhaj hamood sai ya daga kaamil kawai zai fita da shi. Dan yanajin kukan shin ne yake hana shi koda iya furta kalma daya Ai kuwa da gudu ta taho gaban su,xata rike kaamil..kaaamil ya fauce hannun sa alhaj ya korata da wani mugun wajen jahan Aarah ya kaishi tin kan ta tallafo shi taji menene ya faru numfashin shi ya kwace ya zube ajikin ta sumamme Alhaj yana hawaye yana bada jahan Aarah labarin komai Itama kukan ne ya subuce mata tana salati da mugun xaucewar zuci ta fada jikin kaaamil ta kankame shi Fita alhj yayi kafin kace kobo ya taho da manyan dattijan masauratar daular daga dayan bngaren magadan mulkin kasar Dama yasan jira suke su tabbatar da cewa da sihiri ake rike da daulan su Yau sai gashi ranan yazo.. Subaya ta gama da jahan ta haura kan junnut tamata tass tass akan saood da bahiyyya..tayi tirrr da halayen ta ta hada harda iyayen ta ta xage su tsaf Subayan ce ta tattaro kayan sihirin Yau haka aka futo da jahan khatun a tsakiyar dattijai Aka baje kayan gumaka kowa na fadar allbarkacin bakin sa akan ta. Dama shi shirka Babban laifi ne a masaurar musulunci musamman babban daula irin wannan Tuni aka rantaba doka akan zuriar dilshad kathun to the nearest 200 generation bazasu sake mulkann koda dan akuya ne daga daulan iran ba. Bayan angama case An kwace duk wani tattalin masauratr a hannun ta. Jahan khatun tana shock tukun bata iya yin komi sai kuka Gashi duk yadda aka so ayi maganan a sirrinace sanda ya fito fili har magana ya fara zaga gari Da ikon Allah cewar kaamil dan shege ne kawai bai fito a maganan ba,duk garin anfi bada karfin wajen magana akan sihirin da sukeyi Allah ya kama su A daren ranar jahan Aarah ta tafi da subaya da kamil nigeria..ko asibiti bata bari an kaishi ba ta rike shi a gida ita take komai akan shi ita kan ta tausayin shi ya gama nakasa mata jiki.. kaamil ba abunda yake mata sai kuka Yana mai mugun tausaya wa kansa da rayuwan sa Jiyan cikin dare Awajen baccin su jahan khatun ta birkice ma junnut tana xagin ta tana bata laifi akan komai Tace ai da ta san junnut ce ahumgga suka riske da tun da can bata bari an dauko ta ba Tace ma junnut ai tunda ta shigo gidan su babu abunda ke faruwa da su sai koma baya,meyasa xata boye mata cewa akai tsinuwan Ahumagga akan ta? Junnut tayi ta bayani amma ina.. dan sauran Abubuwan da suka bata na arxiki gida motoci kai har da kwagalai da kaya sai da tacee mata ta ajiye mata kayan ta,a daren ta kore ta ba tausayi tace tama bar masauratar dn itakam tasan baxa a barta ta fita ba Junnut tayi roko da magiya da kukan shiga dimuwa Amma jahan khatun tayi kamar bata taba sanin ta ba Gori sosai tayi ma junnut tana tuno mata da kyawawan halayen Mahaifiyar ta jahan xainobia wanda bata gaji ko daya ba. Junnut Daga kayan jikin ta sai takalmin kafarta ta fita a masarautar cikin dare bata san ina zata je ba Da safe Aka kai jahan khatun dark room wato wajen tsarewa na horo da ake yi a masauratar inda Alhaj hamood ya rubuta mata official takardan sakin ta.. Tare da mata nasiha akan cewa taje ta kai kanta wa hukunci akan zina datayi da auren kuma harta haifo dan. Faruwan Abun ya girgixa ta sosai amma haka ta kafe ta nuna mashi rasa komai bai dame ta ba.Akan kaamil kuma Kudi mai yawa ta bukata acewar ta yaje su rike kamil din shida matar sa Ta bar musu shi har abada akan kudin da xai bata. Alhaj yasha mamakin ta amma bai barta hakan ba yasa akayi oficiating takardu yasa ta saka hannu yace baxai sa kudi ya saya kaamil ba..xai bata kudi ne kawai dan taje alhakin kamil dinshi ma kawai ya ishe ta axaban duniya Yana tattara kayan shi ya aje mata cheque na kudi mai yawa Tun daga nan bata sake ganin kowa nata ba. Anan cikin garin laurestan junnut take xagaye da kafarta tana neman mafaka da abinci sak kusan irin rayuwar d bahiyya tayi a street din kaduna. Kafin Kwana biyu ta galabaita,sosai sabida wayanda suka santa agarin suke gulman familyn ta ana nuna ta cikin tsangwama na cewa zuriar masihirin ta Da kyar da fitina ta sami aikin wanke wanke a wani local arabian pub tana aiki kawai dan abata aron waya ta kira ko xata iya nemo taimako Nadama ya gama girgixa kurwan ta ta dawo abun tausayi sosai,kulum idanun ta da hawaye tana tuno da rayuwan ta. Da kyar dai Ta samu ta kira hilda,on the habit of gaya ma hildan duk abunda take ciki..hilda tace tabbb, ta tura dai an biya mata kudin jirgin komawa nigeria amma daga nan ita ma ta yanke hulda da junnut mai gaba daya. Junnut ta iso nigeria ko kudin motar da xataje kaduna bata da shi Anan ma cuku cuku tayi har Allah yasa tasame kudi ta isa kaduna da kyar tasamo umma surbajo wanda ra mugun shan mamakin ganin ta ahakan Ba wani boye boye junnut ta fade mata labarin duk abunda ya faru Umma surbajo ta tausaya ma junnut amma akan abu daya ne kawai bata hakura ba sanda ta mata tas tas ta tsine mata kafin nan ta sauko Anan ta dada jadadda mata karfin cin amana da butulci datayi wa bahiyya,sam ummah bataji dadi ba zama tayi Tana tuno mata waccee ita kuma wacece bahiyya Tsabar nadama junnut sati biyu tayi tana zazxabi mai xafi kamar wanda baxata rayu ba. A bangaren su jahan kuwa saida kaamil yy kwana uku ana jinya sa kafin zuwan alhaj hmaood nigeria inda yake tabbatar musu cewa sun wanye da jhan khatun kuma ya karbe kaaamil kenan na har abada Kaamil yy sigining adoption papers Har abun tausayi agidan duk sunkii su bashi bakin cewa shi ba jinin su bane,aka ci aka kare Har tsoron gaya ma sa'ood komai sukeyi Da kaamil din ya warware sai ya maida maganan kasan zuciyar shi ya danne komai duk sabida ya faranta ma iyayen shi rai musamman dayaga har xaxxabi jahan Arah tana yi akan shi.. Most time in taga yana damuwa har abinci bata iya ci,just for him not make things worst Ya yi hakuri ya karbi sauyin rayuwa da Allah ya bashi ya maida komai ba komai ba Bayan kwana biyu kaamil da kanshi ya kira saood yace su hadu a kano batare da sanin kowa ba Anan ne kaaamil yayi asalin kukan abunda ke damun shi game da asalin sa uwa uba da mahaifiyar shi,yaji sauki sosai daya fidda maganan yay sharin pain dinshi amma Duk da hakan sanda yyi regrting gaya ma khal dan kuwa ba karamin tada masa hankali yayi ba. Thy spend a day togther batare da kowa yasani ba suna famar tattauna matsalan rayuwar su kowa na fadan inda xaisa kafar sa nan gaba.. A dan Lokaci kalilan sai komai ya washe Hidiman bikin subaya ya sake dawowa da bonding din farinciki mai tsafta da xumunci mai karfi arayuwar su Khal yana dawowa daga rako jirgin amarya subaya ya marairace mata akan suma su tafi gidan su kin yarda tayi tace sai su jahan da kaamil sun dawo daga oman hakan yasa yamata wayo yace to ta shirya suje asibiti Kwalliy ta shiga ta caba ta fiito ta same shi yana tsaye binshi tayi kawai bata hankara ba sai ga su a jirgi dagnan ganinsu tayi kawai agidansu. Fushi ta dinga yi ko hutawa basuyi ba tawuce tayi kitchen abinta da sauri yabiyo ta yana dariya ko ta kula shi,.wani rungumeta yayi tabaya yace"to mezakiyi a kitchen din?" turomai baki tayi a shgwabe tace "ni girki zanyi" hannun ta y riko yace "no karki wahalan min da kanki ni zan mana banison kina gajiya" make mai kafada tayi tace "o,o i enjoyed taking care of u". sosai yaji dadin maganan ta hakan yasa ya tsaya ya dinga tayata wasu abubuwan dukda ma tayi tayi dashi yatafi yaki tafiya,french fries na pattoes mai laushi wanda yaji kwai sosai sa kayan hadi. tadafa musu gnshin sai tashi yake dan souce din da pepper chicken tai musu Fruti salad da orange juice shikam tun a kitchen yafara shan juice din Har suka sauko dinning murmushi ta dinga yimai yanda taga yake santi daga ya yadauko warmers sai akaro plates haka y dinga saka ta dariya da kanshi ya dinga bata abaki Wanda da kyar mataci spoons yakai bakwaai Xuciyarta n tashii amai ne ya dinga taso mata kyaleta yayi yana shafa mata gadon baya yana rarashin ta a hakan yasa batai aman ba tai lamo a jikinshi, cin abincin yayi iya cin shi kafin ya dagata yayi sama da ita dakin shi ya bude ya shiga da ita yace "bby bari naje masjid ankira salla kema kitashi kiyi" ta gyadamai kai ya shiga bayi ya dauro alwala ya fita da sauri jin antada sallan yasa ta tada niyya lallabawa tayi tafice daga dakin tai dakin ta magungunan da aka sake bata daga gida ta kwaso ta zuba madara ta sha sosai Atunanin ta suke hanata tashin zuciyan datake yawan yi,alwala tayi tayi salla sanan takoma bayin tayi wanka da ruwan mai dumi sosai tadade abayin kafin tafito ma har an kira isha,yan shafe shafen ta ta yi mai kayaytwa rigan bacci tasa daya kaimata
Chapter 171 · 0% Book details