← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 173

Sashe 64

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin tunanin yadda zata je ta lallabosa. Tasan bazata iya gaya masa komai ba,muddin basu cimma burin su akan sadatt ba..she knew she cant risk it..amma kuma dole ta gaya masa abunda xaisa hankalin sa ya kwanta sosai.. Mikewa tsaye tayi ta tattara wajen duk broken glass din tayi disposing,rigar data sa akan jean din tayi sallah shi ta mayar ta hada da mayafi ta fito a sadade tana neman inda zata gansa. Data murda kofar ta fito sarari ajikin step na karshe Tayi tsaye kusan Minti 10 tana kare ma gidan kallo evrything all white hakan ya dada haskaka mata idanu har ta hango wani chef dake tahowa gaban ta da tray din abinci.. Har ya karaso batace mishi uffan ba,shikuwa yana isowa gaban ta ya dan risina kaii ya gaishe ta,..yace khaldun ya bada oder cewa asake kawo mata abinci.. He dint forget that anyi mata alluran cin abinc i,sai tace mashi yakai dakin ya aje mata Dan kwafa tayi cikin tunani,ohhhh duk wannan fushin da akayi dani ba a dai mantawa dani... Chef na fitowa tayi sauri Tace pls excuse me... Sai ya juyo.. Tace Pls where is he..? Ganin kamar ita din sam bata da dirin wulakanci Sai ya sa shi ya mata nuni da wani kofa dake daff da inda take tsaye,dakin yana kallon juna ne da wanda ta fito aciki yanzun. Ta dan kwakwalo murmushi tace thanks,chef da wuri ya sauka ita kuma ta isa bakin kofar dakin... 20minutes tana knocking da kyar ya bada izini aka shigo Kwance yake yayi luff ya lunshe idanu akan gadon sa ya kuma bada kofar baya He is literally upset,jira ma yake ya bude idanun shi ga wanda ya shigo ya sauke masa bala'in masifa ...yana kuwa juyowa yaganta tsaye daga bakin kofar tayi shiru ta dauke kanta tana dan wasa da yatsun hannun ta,he feels better dayaga babu hawaye akan fuskan ta yanzu amma shirun datayi ya sa ya kau da kansa ya bata keya... Wani lumshe idanun sa yayi,yana kokarin Rokon ziciyar sa ya sauko dan yaga ko hala zai iya lallabataamma ina,kowani five minute baiyi ba yaji inuwar mutum daf dashi.... A slow ya juyo ya bita da wasu razanannun looks,idanun shi babu wasa a ciki...hawayen dake shirin cikowa ta mayar ta matso daf inda ya kwanta tana binshi da kallon itama,cikin marairacewa da sanyin shagwaba slowly ta zuba gwiwan ta akasa tace.. "Dan Allah Kayi hakuri. .. Wani sanyi yaji aranshi,amma bai ce uffan ba ya dauke kansa .. Ta fade hakan sau uku yayi kamar bai ma san da shi takeyi ba sanda ta dan kara sautin crack voice din ta Sannan Ya juyo da kyau.. Dan Allah kay...yace stop nan ya dakatar da ita da wani irin kallon kulawa.. Kinci abincin dana tura maki? Sai Ta dago grey eyesballs din ta kadan Nan suka hade ido,cikin sanyi jiki ta girgiza mai kai tace ah'a banci ba shi kansa baisan meyasa shi tsaki ba, mikewa yayi ya mata nuni da hanyar waje.. Nan ne hawayen da take dannewa suka fito,..rabon ta dataga ya tsime haka tun lokacin datake matsayin maid dinsa,..bata jin tana da karfin daukar fushin sa ayanzu dan haka ta mike a sulale ta nufi bakin kofar niyar ta inta ci abincin saita dawo,..bata hankara taji shi daf,karasa turata wajen yayi ya slaming door dinsa gaban idanun ta... Shock ya bar mata bakin ta a bude,sam bata san meyasa yake da fushi sosai ba,...goge tears din tayi tana sauke ajiyayyun ajiyan zuciya...tasan bazata iya jure hakan daga wajen shi ba...jikin kofar ta koma kamar zata sake knocking amma batayi ba sai ta jingine bayan ta cikin nitsuwa ta fara rokon shi achan cikin wuyar ta... Pls open the door... Da kyar take furta hakan, i want to tell you evrything..pls open...very weak hands dinta ke bubuga kofar lighy tamkar bata san metake ba After 10minutes of silence taji kyat alaman budewa.,wani disashen murmushi ne ya kufce mata sai tayi saurin goge hawayen sannan ta tura ta shigo,,dashi ta cikaro gumm a gaban ta bata kara one step ba inuwar sa ya dakatar da ita ,..a tsaye ta same shi abakin door din ya rungeme hannayen sa a kirjinsa.. Wani irin quick and passitionate looks sukayi exchanging sannan ta sauke idanun ta kasa a hankali ta shiga rero masa labarin data shirya. Tafara ne da bashi hakuri,a cewar ta itama bata san sunan ciwon dake damun ta...Ta kuma tabbatar masa da cewa babu abunda ta nema ta rasa na kudi... Wasu nannuyan hawayen suka kufce mata Sai tace ina ga fa mafarki ne.... A slow yace mafarki? Sai ta gyada masa kai kaman dagske .. Ai kullum inayin shi,I kept seeng it... I think im scared...ni fa tsoro nakeji Yace tsoron waye? Ta dan yi shuru,sanda ta sauke wani ajiyan zuciya tace,ni bansan shi ba,shine sai yana tsoratar da ni..kusan kullum yana zuwa min bana iya bacci...i dont know what to do..i keep getting sick...kuma ina fada babu mai yarda dani,.a hankali ta karashe karyan nata cikin sautin kuka Wani lumshe idanunshi yayi cikin jin tausayin ta,a baya cikin hankalin sa ya jawo ta jikin sa ya wani rungume ta sosai saida ta aje kanta akan kafadun sa itama tana sauke wasu fitinannun ajiyan zuciya... Its ok...ya fada very calmly agefen kunnen ta yana dada kamkame ta itama zagewa tayi tana lumewa jikin shi tana dada sauke ajiyan zuciya A tsaye dai sun kai mintina talatin, sanda ya tabbatar ta dawo hankalin ta kafun ya tattaro fuskan ta da hannyen sa ya shiga kare mata kallo ,..sauran tears din dake fuskan ta ya goge,yace zakici abincin?wani waek smile ya kufce mata sai Ta gyada mashi kai suka fita.. Agaba ya sata tana cin abincin chef din rashin lpyar yasa take taunawa very slow har ya fara tunanin ko abincin baiyi mata bane Cikin sanyin kallo ya tambaye ta me kike shaawar ci,kamar zata ce babu komai but ganin idon shi yasa tace mashi mint tea... Toh Shi dakansa ya hado tea din y kawo tana gama sha tayi kwanciyar ta shi ya fita..bata sake ganin sa ba sai da asubahi. Doc zai sake dawowa dan haka ya taimaka mata ta yi sallah. . Magungunan bacci dana cin abincin daya dinga samata har na tsawon kwana uku shi yake dada rike mata jiki. Cikin kwanakin kaamil ma ya kira shi but sabida halin datake ciki sai yace masa kawai yana london ar yanzu bai dawo ba. Tana jin cikin wayar nasa,ya sauya mata suna zuwa"twinkle" Kaamil ya so ace an bashi ita sun gaisa amma sai dai ya dube lumshashun idanun ta yace masa tana bacci.. Da haka tension ya fara raguwa mata Sometimes idan tana bacci bata cikin hayyacin but takan ji duk hidimar da khal yake mata na kulawa. Toh Tunda doc ya dena zuwa Da dare inzatayi bacci shi yake yawan zama kusa da ita ya karanta mata alqur'ani.. Sometimes anan kasan kusa da gadon yake zama yana gadin ta har asubahi baya runtsawa,cin ta da shan ta duk yana lura sosai.. Kowa waya baya cika son amsawa idan yana tare da ita After 1 full week agidan,ta mike ranar asabar da safe ta farka dawani karfi da nishadi tana jin jikin ta ya warware tasss alaman sauki ya samu.. Shikuwa da ya lura da hakan sai yaja jikin sa,trouh out the wekend bai wani je inda take ba. Ba laifi takan fito dakanta tsakar gidan tayi ta zagaye zagaye,ranar bata ganshi ba gashi kuma tana mugun kwadayin noodles Da taimkom chef ta nufa Kitchen ta shiga hada wata garnished indomie mai dan karan qamshi,dan rabon ta datayi girki yakai fiye da wata guda. Tsaban yadda take jin yawan cin abinci yanzun tun kan indomie yagama hucewa take famar zara tana kaiwa baki,.. Budewan kofar kiitchen din ya sa ta farga wani gurd tagani sanye da plain army uniform yace mata ta taho khal ya dawo yana neman ta a falo Ba bata lokaci ta fito dauke da plate din indomien ta,riga da wandon jean da hular sakar ta baki ne ajikin ta,tsavan qamshin idomine na bugata bata ma lura da abunda ke gaban ta Tun a saman yagama kare mata kallo Da wani mugun ido ya sallame duk wayanda suke wajen,harda wanda ya kawo masa aikan da bai ma saurare sa yaji ba.. Tun Akan step na karshe data dora kafar ta zata karaso taga ya mike tsaye ya hade ranshi yana kallon ta Wai mene ne wannan,..? Baki a bude Ta tsaya tana dan dube dube ta gama daukawa ko ba agirki agidan ne ita taje tayi,..wani shegen naugty face ta bashi wanda tuni ya dada ruda zuciyar shi da kishin ta Looking at her up and down yace wai baki da kayan sawa ne sai wannan,ni baiyi min ba..and u cant wear this in my house... He sound weird to himself,amma sai Ya dada hade rai ya karaso ta gefen ta zai wuce ya haura dakin sa..."go and change"a iska ma ta jiyo . Bayan ta dauke idan ta akanshi Tabe baki tayi tana kare ma jikin ta kallo ta ko ina bata ga aibun ta ba,ita dai tun nigeria big sis ta sabar mata da saka kananan kaya na english gowns materialz gowns ko jean da top,tasan baison barin kai abude kam kuma dama ita duk tsiya bata fita babu rifin kaii Amma yanzu sam bata fahimce angern sa akan saka jeans din ta ba,..kyabe baki tayi ta karaso tayi zaman ta akan cushion din tana cin indomien kadan kadan tana wondering,to ita wani kayan zata sa masa bayan a jakan ta inbanda jeans din babu wani kaya na daban sai simple jumpsuits shima daya kawai ta dauka.. Ko rabin plate din batayi kusa ba taji karar rufe door Jin motsin saukowar sa kasan yasa ta ta mike a gurguje tare da aje abincin da sauri ta hauro kan step, din tun anan ta rakube tana dan satan kallon shi bai kula ta ba ya sauka,she is left with no other choice than ta cire kayan jikin ta ta saka jumpsuit din duk dama yadan rike ta shima But is beter when she cover it up da veil din nata.. Bayan ta sauya kayan Saukowa
Chapter 64 · 0% Book details