Sashe 33
Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ta dan kalle ni tace are you alright? Uhmm kawai nace Na gyada kai kafin na sunkuyar da kai ina tare hawaye na. Jira ni anan Ina zuwa...kafin na dago ma ta haura sama ta bi bayan sa. Kofar dakin shi ta nufa Tayi knock bai kula ta ba,sai ta turo door din ta shigo mamaki ma ya bata da taga gansa A Zaune hankalin sa nakan wayar sa yana latsawa Sau daya ya daga ido ya kalle ta ya dauke kansa ya cigaba da abun da yake yi Kallon 2 seconds tayi mashi tare da sauke ajiyan zuciya sai ta taho ta zauna kusa dashi cikin sanyin jiki Da taga bai kula ba,Wani irin marairace fuska tayi zata dafa shi ya ja jikin sa ya kau da kansa gefe ,..Khal...pleasse Aaaban..muryan ta yayi rawa tun kan takai gaba Yace ya isa haka subaya,meye ne kam kuke takura ni i realy dont want to be angry today. tace toh ka fada min mana? Whats going on ina nufin menene ya faru tsakanin ka da bahiyyan? Bai kalle ta ba Yace nothing. Tace and today? Khaldun,kowa yasan kai kadai kake cin breakfast,so why ..Hannu ya daga mata tun ma kafin ta karasa yana kallon ta cikin azalzalan masifa... Kin cika tambaya subayah,dole ne sai kin san komai?Ok fine she drank some mango juice,sai ya shake ta and then she faint shiyasa kika ganni da ita jiya and today we are just having Normal breakfast,kina da matsala da hakan ne?Whats wrong with that?. Adan tsorace ta dago ta kalle shi bakin ta har na missing step zatayi magana ya mike tsaye cikin bacin rai Wai Meyasa duk abunda nayi sai ya dawo miki fitina why...ya dan daka mata tsawa sai datayi hadiyan yawo Wani hawaye mai sanyin nuna razanar karar nasa ta sake mashi dan Gaba daya ta kasa motsi sai ta sunkuyar da kanta kadan cikin shessheka Tsaki yaja ya nufi bakin door ya bude "Look just Get out ya mata nuni da hanya Bata motsa ba tace toh Kayi hakuri dan Allah .. I just wanted to know,nan ta shiga gaya masa abunda sadaat yake dora ta akai tun jiya Juya kansa yayi yana cije labban sa cikin jin haushi, gashi Har cikin ransa ya tsani ya ganta a hakan,but he is so pissed right now ita kanta tana bashi haushi dan ya tsani janjana magana bare uwa uba yaranta. Kukan sa baiya so din take faman yi 2 seconds look ya bita dashi tana kan matso hawayen,tare da sauke boyayyen ajiyan zuciya ya dawo kusa da ita ya riko hannun ta cikin nasa"Come here... ya jawo ta ta mike tsaye kusa da shii wani kallon so da kauna ya bi cryng face din ta dashi yasa palms dinsa ya shiga goge mata yana binta da wani irin sanyin kallon kauna gaba daya sai da ya kashe mata jiki sai ya jawo ta jikin sa kadan ya rungume ta ya fara lallashin ta yana petting din ta. A kunne ya furta its ok ba fada nake maki ba,rainin ki ne ya ishe ni..ina duk kin gaji dani ne,to im going Subayah ni sam bana son fitinan ki. Wani cukuikiya shi take dada yi tana shiga kirjin sa da wani irin shauki ta yadda dukan gabobin sa suke amsawa da irin son data ke mashi Lunshe ido yay yana sauke ajiyayyan numfashi "Mutum Sai shegen son kuka kamar wata yarinya bayan kinsan bana so ko? Lafewa ta kara yi a shagwabe Tana share hawayen ta Cike da marairaicewa Tace im soryyy khal nifa bana son ranka ya baci ne..bai bari ta dora ba...yatsa yasa abakin ta yace shusshhh Duk abunda kike so a duniya zanyi miki shi Ina dai Kina so na karbe ta a matsayin sistar mu ne ko? Ta dada lafewa jikib sa Ta gyada kai Will you be happy if i do that? Tayi murmushi tace yeess "Dan karamin ajiyan zuciya yayi ya kissing hannun ta da goshin ta yace,its ok so be it; subaya I have accepted her komai ya wuce yanzu? Wani kankame sa ta da dayi ta gyada kai tana murna har cikin ranta tana masa godiya Tace I love you! Yace I love you too Go now,kijira ni a wajen mum akwai abunda zan fada miki Sai Ta tsaya kallon shi Murmushi mai kyatrwa ya mata cikin wasa ya ce no more tears? Tuni ta goge saura hawayen ta ta mayar masa faffadan murmushi tace ok am waiting sai ta fice. Dan karamin lumshe ido yayi kafin nan ya cigaba da abunda yakeyi Kan kace kobo ya shiga tattare tattaren sa,masu mashi aiki ne suke faman jigila suna fitar masa da kayan sa waje.. Lokacin nikuma har na tattara dishes din naje kitchen ina wankewa,sai dai gaba daya zuciya ta cike yake da tunani kala kala,bansan meyasa yau din kwata kwata bana jin dadi araina ba. Aiki na ma cikin qwiyuwa nake yinshi ,and I almost foget that jahan tace naje na same ta dazun,da abun ya fado min sai nayi saurin maida hankali kan aikin Dama so nake nayi wanka na dada tsaftace kaina kafin naje.. FOLLOW #SURAYYAHMS *Hmm sadat yau 10-0 but We need munafukai in our lives A rayuwa Allah yakan turo wani daban wanda ba jinin ka ba kuma sai kaga shi zaizo ya zama silar finciko munafuki ko mugu wanda tuntuni kana tare da shi amma idon ka ya rufe baka sani ba,idan zakuyi tunanin situation din sadat da bahiyya kusan haka ne,abu biyu ne ake tsammani ko shi yaci nasaran fitar da ita ko ita taci nasarar kawo karshen sa..lets hope for the best _TEAM KHAL SA'OOD dama nika daice Kar naji wata tace itama Share share and share AHUMAGGAH _A nigerian historical fiction_ *WATTPAD SURAYYAHMS*_ _Brilliant writers association_