← Book details Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 173

Sashe 65

Ahumaggah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

take tana dan leko shi,bata ga meyake ba sanda ta fito sarari taga empty plate of indomie da remote a hannun shi yana kallo... Dan kadan ta turo baki ta shagwabe,abu kamar ba maita haka kawai kuwa indomien ya biya ranta,tsabn kiriniya ko sallama bata masa ba ta sulale ta zauna akan cushiob dake kusa da nashi,da gefen idon shi..he notice her silly pouts,sai yauqi takeyi ita kadai cikin ranta tana banbami ...duk ya gane damuwar ta. shi Jira yake tayi korafin indomie ya hada ya mata masifan,jikin nata dan baiso ace tana takura kanta. Baisan saukin nata har sosai haka bane,suna cikin kallon shiru saiga chef ya shigo da kwalayen pizza guda biyu ya wuce kitchen dashi anan ma take taji ranta ya biya akai. Alhamfullhi After 10minutes taga chef din yana jere akan table Wasu dadan hand made chicken shawarma,pizzan da aka siyo sai damammen oatmeal da madara mai dumi. A ladabce yace sir..the food is ready, Sai ya tafi yana dago kai suka hade ido da ita tayi saurin daukewa,kada kansa kawai yayi kamar bazai ce komai ba chan dai yace go and eat ur meal.. Toh Ranta ya riga ya biya Cikin basarwa Ta mike a sadade abunta ta nufi dinning,tana tafiyar bata sani ba duk jikin nata ya kafe da ido yana ta kallon dresing din nata wani siririn tsaki ne ya kufce masa sai ya dauke kai.. "Bata damu da rashin tahowar sa kan dinning ba ta bubuude abincin Ababu Ababu Babu abunda bata ci ma cikin ta awajen ba.. Cup ta jawo Tana kokarin zuba plain water...Wani phone call din daya da keyi ne yaso ya ja hankalin ta dan kiris ya rage ta gane cewa da mace yake maganan.. Bata gama tunanin ba taga ya tashi da wayar a hannun sa,wani package ne agefen sa tun wanda dazu ta gani amma batasan na miye bane but she kept suspecting that pack haka kawai,sai taga kuma ya sa ana biyo sa da shi cikin dakin sa ya nufa a alama har iyanzu bai gama ba.. Haka kawai taji walwalan ta ya yanke karshen cin abincin nata kenaan sai ta bar wajen ta dawo palour ta zauna,kallon take amma gaba daya hankalin ta bai jikin ta,she was not sure ko da macen yake magana ba amma yanayin daya ke ansawa wayar ya banbata da yadda ta saba gani,wani rau tayi da idanun ta kirjin ta na mata wani zafi she cant bliv that kishi mai zafi tajeji akan sa.. Tun tana basarwa dai har taji ta kasa hakuri rashin saukowar sa akan lokaci ya dada kara ma zuciyan ta uneaseness .. Shikuwa sanda a shiga dakin ya samu freedom din magana da ita yadda yake so.. Junnut Ta takura cewa zata dawo us cikin satin dan kuwa tana missing dinsa..so take tayi amfani da sauran hutun ta suje chan kingdom tare Sai yake gwada mata shi baida wannan lokacin Ayanzu haka ma tafiya zaiyi... Gifts din dake wajen ita ta aiko da shi tun daga hungaray ita kadai tasan me tasa masa aciki,.take cewa idan ya bude yagani tana so ya kira ta in yayi haka zata ji dadi cos har yau baya daukan hannun sa ya kira ta haka kawai sai dai ta kira shi ko ta zo dakan ta. Amma Duk iya wulakanci da iya basarwan sa inta kira kullum sai ta nace sun kai minti talatin suna wayan A yanzun ma Da kyar ta amince ta kyale shi yana sauke wayar a kunnen shi yaji an turo kofar,tuni idanun sa suka sauka akan bahi ita kanta bata san meya kawo ta nan ba... Duka Sunyi shiru ba wanda ya tanka,sai ta fara sosa gefen kunnen ta,wani noughty smirk yayi ya taho zai wuce ta...sai ya tuna da gifts din dawowa yayi zai kai hannu kai tayi saurin rigashi wani daukewa tayi da uban sauri tace let me help you...tana dana masa duka idanun ta akansa kamar wacce take da degree a masifa da kiriniya . No thanks...ya miko hannu zai karba ta ja da baya da bags din ta dauke kanta.. yayi karamin furzan iska yace Ok lets go down,nowww...sai ya fice Haka ta biyo sa da shi suka dawo palour bata bashi ba,kowa zama yayi ya tsime Daga Kan kujeran san in ta juyo anata sai ta kalle shi...wani kallon data ke mashi na dole a sai an bude mata pack din taga me aciki shi yasa shi ya kasa dena mamakin ta...is she mad? tsaki yake ja aransa yana lura da ita yana bambami shi kadai,..to ina ruwan ta da gifts dina,..tasan da kishi take barin jikin ta abude kowa yana gani..yayi tsaki ajere ajere cikin wuyar sa Yafi sau dari..itama ba abunda bata fada aranta ba,yanzu data tabbatar da mace yayi wayar tana tsaye abakin door dinshi ai taji ana cewa"she she"...slow take hararar sa da gefen ido...ita dai lallai tana so ya bude gifts bag din ai inma subaya ne tasan zata gane. Mikewa yayi a bazata Zai haura sama,sai ya ga bata ko kalle shi ba,gift in ta dada jawo tana jira ya haura ai ta bude da kanta,yana hawa kuwa ya labe as expected yaga ta dage karfin ta tana fincike seal tape din kamar wanda aka bata aiki. Thats very rude of you...ya fauce abunsa ta bayan ta yana mata masifa bata ma san yaushe ya lallabo ya sauko ba. Wayace ki bude min...naki ne..? Sai ta dan kalle shi a sanyeye bata masan meke tunzira ta ba,jinta kawai tayi ta Wani hade rai Sai tayi masa shiru har fushin nata sosai ya ke neman ya shashi dariya.....atleast na rama..ya ayyana hakan aranshi mirmishi yake aransa amma fuskn babu sauki..shegen kishin tsiya ai sai nayi maganin ki.. Ya kwace gifts dinsa,.yana haurawa sama ko budewa yaga meye aciki baiyi ba sabida ita ya kira mai aiki ya bada shi kyauta Washe gari da safe Wani heavy knock ne ya dago ta a bacci,ta bude door din hannun ta akan fuska tana mutsukawa,ta duba bata ga kowa ba sai manya manyan ledojin shoping kowanne da logon arabian designer masu shegen tsada kuma na yayi.. Lekowa da kyau tayi ko zataga wanda ya aje su amma sai shiru babu kowa awajen,wani mika tayi cikin salati tana kirgo yawan su da idanun ta,manyan guda uku sai kanana da dan dai dai guda biyar biyar,.. One by one take shigarwa cikin dakin,bayan ta idar da sallah ta kimtsa sannan ta zauna ta shiga duddubawa tana zarowa waje shoes,long skirts da gowns And Most of them are turkish gowns and Arabian jallabiyas guda daya ne ma tasame shi riga da wando da mayafin shi irin pakistani fashion din nan Komai awajen na yan mata ne kamar ta masu daukan ido kowannen su chic and decent ..Bakaken covers na Chador da burqan ne ma yaso ya sata dariya,tunani take wai itace zata sa masa wannan? Ko a mafarki bata kawo hakan ba. Wanka tayi ta dan kimtsa kanta with very slight make up,cikin kayan ta dauko wani gown mai fadi mai open button black and white colour an matse kugun da black belt kasan kuma anyi shi mai step step har sama. Hannun shi dogo sannan tsawon shi ya kai mata har idanun sawon ts Tsarin rigar yasa ta tattare duka suman kanta ta masa daurin donut ta tusa su gaba daya acikin black turban ta fesa turare Sosai tayi kyau. ita kanta data kare ma kanta kallo tuni ta gane banbamcin abunda yake son ya nuna mata tsakanin saka wayancan kayan da kuma wanda zai rufe mata jiki gaba daya sannan ya sa ta fito kamar sarauniya.. Cikin kadadi ta dada duban kanta Is not bad huh? .. islamic code of dressing is way better than any other.. Idan kaga ka rufe jikin ka bakayi kyau yadda kake so ba to lallai laifin daga kaine.. Koda ta sauko a hakan ta fannin shi taga sauyin fuska,smiles dinsa mai tsadan shi ya tare ta dashi,then koda ya mata tambayar me zata karya dashi data fada shi ya shiga kitchen din ya fara hadowa dakanshi Scramble egg,milkcustard da coissant...yana bugawa yana murmushi shikadai. Daya gama Hakan ya sata agaba ta cinye kuwa tass...after that day suka tafi dubai halartan wani islamic family gathering na iyayen babban aminin sa shahrul Koda suka iso shikansa shahrul baisan ita bace agefen sa sabida bayan plain bakar abayan daya sa ta kwama mayafin burqa shine ya rufe ko ina da inan ta Burqa,irin cover din nan ne na matan larabawa wanda yake kamar hijabi mai hade da niqab shi baya kama jikin mutum kuma zallan wajen idanun ta kawai akayi da black transparent Material agefen shi take tafiya,tunda suka gaisa shah yake ta lekowa ko zai gane gashi gogan ya tsime ya hanata kyakwan tari duk abunda zatayi yakanso tagaya masa.. Sanda suka je masauki,daya umarce ta da ta cire burqan ta ci abinci kafin shahrul ma yasan itace He was freaking out tsaban mamaki har sanda ya sata tayi dariyar sa.. Yace Pretty girl ashe kece,dama dazai tafi yace wata rana zata zo inda yake..Sai gashi yau khal dinsa ya kawo ta yaji dadi sosai Its a very big royal gathering hidaman addini ne ya hadu na zunzurutun ahalin sarauta da mulki na larabawa masu tarin dukiya. Kusan duka prince da princesess na daulan islamic nations daddaya ne basu wajen kowa da tawagar sa da kuma irin kalar kasaitar sa "Khaldun jinin sarauta ne gaba da baya amma ko da wasa abun bai dara shi ,shi yafi gane ma military stand dinshi dan haka ne ma saudi arabian emirate suka bashi matsayi acikin manyan sojojin da zasu na taimaka ma addinin musulunci underground.. Ya hadu da malamai dayawa wanda suka koyar da su islama,dan sanadiyar shahrul ya karanci addinin sa at age of 18 ya sauke qur'ani batare da kowa ya sani ba A da chan ya tashi ne yaga alaman kakan sa dilshad bata ko tunanin tana saka su akan wannan tafarki.. So Shiya koya sannan ya koyar da kaninshi kaamil tun a camp. ,..maids da masu kaikawo Nata famar fadanci,bahiyya tun tana wondering har ta fara sabawa da yadda ake worshiping din su ana binsu suna basarwa.. Ur highnesss..ur majesty..kadai zaka ji
Chapter 65 · 0% Book details