← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 130

Sashe 96

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya nisa tare da matsar da face ɗinsa dab da tata. "Waɗan nan sun mun kanana, ke kanki kin mun kaɗan, ba zaki iya ɗaukata ba, amma ita soyayya babu ruwanta da girma ko kankanta, a lokacin da ta so kawai zata shigeka ne, ba dan haka ba ni nasan kin mun ƙankanta, sai na yi renonki kin girma in ba haka ba a ranar farko mutuwa zaki yi, in baki mutu ba kuma ba zaki sake moruwa ba, ni babbar mace nike buri, wacce zata iya ɗaukata ba ke yar karamar da sai na yi reno ba!".

Tin da ya fara magana tsoronsa da shakkarsa ya shigeta, ta natsu tsit tana kallon ɗan bakinsa, amma da ta ga yana ce mata yar karama, kun san ta da son girma, and mara kunya baya sake hali ko kashe shi ake yi, dan haka sai ta ce. "Wlh ni ban yi maka ƙanƙanta ba saboda ni ba yarinya bace, a kanka ne zan mutu? Irinka goma ma zan iya ɗauka ba tare da na gaji ba". Murya na rawa ta yi maganar, and ta ce irinsa goma ma zata iya ɗauka ba wai tana nufin wancan kalmar ba, tana nufin nauyi, dan a haka ta fahimci zancensa, da ya ce ba zata iya ɗaukarsa ba ta zaci irin goyo haka ko ɗauka a kafaɗa irin wanda ake yi wa yara, shi ne dan ta gwada itama jaruma ce wai irinsa goma ma zata iya ɗauka, zata iya goyawa kenan. Watau kurici dangin hauka ne, bama fa tasan me miji yake nufi ba, bata san me ake a aure ba, sai rashin ji da rashin kunya ta iya.

Ai da jin kalamanta sake fusata ya yi har bai san lokacin da ya matseta da jikin headboard na bed ɗin ba. "Irina goma zaki iya ɗauka? A ina kika san hakan? Ko kin taɓa ɗaukar wani ne?".

A kule ta ce. "Sau nawa ma ina ɗauka". Ta faɗa tana ƙoƙarin kwace kanta, dikkan sun fahimci juna ne a baibai, ko da yake ita ta kwaɓe zancen, dan ita ce bata san ma'anar kalamanta ba.

Haba take kishin maza ta motsa, har wani irin huci yake yi ya ce. "Ban yarda dake ba, dama wasu mutanen kauyen ba kula da kai suke yi ba, dole zan duba virgin ɗinki yanzu, dole zan duba ko kin taɓa baiwa wani damar shiga gonata, no wonder, shiyasa kike da rashin kunya har haka, shiyasa idanunki suka bushe, shiyasa har kika san ki ɗauki goma irina, ba banza ba, ashe kin taɓa ɗauka a baya". Kusan cikin fitar hayyaci ya yi maganar, zafin kishi na neman yi mashi illah a zuci.

Ita dai da bakinta yaki mutuwa ne ta ce. "E na taɓa ɗauka ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, kuma rashin kunya ne na yi ɗin tin da ba ubana bane kai".

Wani irin tukukin zafi ne ya turnuke zuciyarsa, ji yake tamkar kansa zai rabe gida biyu, idanunsa suka tsananta ja, jikinsa har yana wani irin tsuma tamkar ya dawo Omar ɗinsa na ainahi. "Ban yarda dake ba, dole zan duba virgin ɗinki, kuma wlh idan har na tabbatar da abin da kika faɗa, kin taɓa bawa wani dama ya shiga gonata, wlh ba zan yi kaffara ba sai na kasheki da hannuna!!". Cikin kakkausar murya ya yi maganar.

Ita kuma da wauwata ya gama da kwakwalwarta sai ta ce. "Gona kam ba ɗaya ba ba biyu ba na sha shiga". Tana nufin ta sha shiga gonaki a kauyensu, dan ita a tinaninta faɗa yake yi a kan ta taɓa shiga gona, kun san har yanzu larabcinta da saura, shi ne take faɗa mashi ai ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ta sha shiga gona, amma nufinta gonan bappanta.

Datse idanunsa ya yi gam tamkar zai fashesu, da karfi ya daddage ya dalla mata wani gigitaccen marin da sai da ya turata hutun É—an lokacin. Fisgota ya yi da karfin gaske ya kwantar a saman bed É—in, Dr Omar zai yi bincike!. A farko bata san me yake shirin yi ba, dan ta É—auka dukanta zai yi, sai da ta ga yasa hannu ya keta rigar jikinta ya jefar ne ta fahimci kaya yake son cire mata, a hakan ma bata fahimci abin da yake son dubawa ba, ta zaci zai cire mata kaya ne ya zaneta tin da ta ga a kauye malamarsu Inna Rabi sai ya cire masu zani ko sai ta É—age shi sama take zane kafafunsu, to sai ta É—auka kaya zai cire mata ya zaneta.

Nan ta fara kuka tana faÉ—in kada ya cire mata kaya. Sai wani irin huci yake yi tamkar zai kama da wuta, cikin fushi ya ce. "Idan na sake jin bakinki sai na kashe ki!!". Yana gama faÉ—ar hakan ya damki kafafun wandan jikinta baya ya cire botir ta sama ya kuma zuge zip kasa, ya damki kafafun wandan da karfi ya rabata da shi. Ya rage daga ita sai pant.

Ai wani irin zabura ta yi zata sauka ta gudu, a miliyan ya danketa tare da kara kwantar da ita, ƙoƙarin kwace kanta ta yi domin ta rufe tsiraicinta, amma ina, ta gagara, nan ta fara ƙoƙarin yin ihu ko za'a kawo mata ɗauki, ai hayewa kanta ya yi tamkar wanda zai yi wancan abin, ya toshe mata baki da hannu ɗaya kafin ya jawo rigarta, ya daddaneta ya ɗaure hannunta da shi, sannan ya jawo veil ɗinta ya ɗaure mata baki da shi.

Ai sai yau ta tabbatarwa da kanta yana da shegen karfin da yake cewa yana da shi, dan kuwa da ya danneta ko motsi bata iya yi ba har ya ɗaureta, ga shi kuma yadda ya yage mata kaya ya razanata, ta girgiza da shi. Baya ji baya gani haka ya cire mata pant, zafin kishi yasa gabaɗaya ya fita a hayyacinsa. Kuma cikin fushi yake komai, tana ji tana gani ya cire mata kaya dikka kafin yasa hannu ya buɗe kafafunta, tsabar yana cikin ɓacin rai ko sha'awarta ma bai ji ba, abin da yake son dubawa kawai ya kafa kai a wajen.

Lokaci guda kuma ya É—auke wuta, tamkar wanda aka bugawa guduma a tsakar kai, cikin zafa ya É—ago da kansa daga kallon da yake yi wa gaban nata ya kalli fuskarta, hawaye sun gama wanke mata fuska, da sauri ya diro kasan bed É—in yana dafe kansa dake barazanar tarwatsewa. Waje ya nufa yana wani tangal-tangal tamkar zai faÉ—i, yadda kuka san yana cikin maye.

Har ya kai wajen kofa kome ya tuna sai ya yi zafan juyowa ya dawo, da sauri ya haye saman bed É—in. Yana É—an kawar da kansa ya É—auko pant É—in nata, kamar yadda ya cire mata haka ya mayar mata da komai, har riga ya sanya mata, gagara É—agowa ya kalli cikin idanunta ya yi, ita ma dai dik rashin kunyarta ta gagara kallonsa, ta yi kasa da kai tana kuka kuma ta natsu tsit babu hayaniya ko shirin guduwa.

Shiru ya zauna a tsakiyar bed É—in yana sauke huci a hankali-hankali, alamar yana hucewa kenan. "I'm so so sorry". Shi ne kawai abin da ya iya faÉ—e tare da yunkurawa da sauri ya diro kasa, bai sake waiwayota ba ya yi waje, zuciyarsa ce take bugawa da karfi-karfi, da sauri ya afka room É—insu, Ronnie na kwance a saman bed, ba ko sallama ya afko ciki, yana zuwa ya faÉ—a saman bed É—in shi ma, Ronnie mai bandeji a goshi yana tambayarsa lafiya, amma ina babu amsa sai aikin sauke dogon ajiyar zuciya.

(OMAR YA GOGE MUN HADDA. KO ME ZAI BIYO BAYA?🤔 ANYA MA WAI BIG BRO BAI KARYA MAGANIN DA SUKA BASHI YA KOMA AINAHIN OMAR ƊINSA BA KUWA? DAN DAMA KUNGA BIG BRO YA ZO HAR ƊAKI YA GANSA HMMMM.)

-----------------------🔥

Bayan ta kammala cin abincin nata, miƙewa ta yi ta nufo wani sofa one seater dake kusa da bed ɗin, dik wani motsinta a kan idanunsa ne. Saman sofar ta zauna suna fuskantar juna, kuresa da kallon soyayya ta yi, shi ma kallonta yake babu ko kyaftawa.

Almost 5 minutes for silent ta katse masu shirun da cewa. "King of heart wai kai baka gajiya da kallo ne? Ko kyafta idanunka fa baka yi". Cikin ɗan madaidaicin shagwaɓar da ba zai tada hankali ba ta yi maganar.

Almost 2 mins ya ɗauka kafin ya bata amsa da. "Kin taɓa ganin inai wa wani wannan kallo bayan ke?"...... Kai ta girgiza alamar a'a tana sakin murmushi. Ɗan jinjina kai ya yi. "To kallon naki ne ke kaɗai".
Haba ji ta yi tamkar an bata aljanna, ta É—an kwantar da kanta jikin hannun sofar tana binsa da wani irin musulmin kallo kafin ta rungumo hannayenta a kirjinta.

Gera ya É—an É—aga mata alamar ya ne?. ÆŠan girgiza kai ta yi kafin ta ce. "Yadda na zauna haka ina jin tamkar na zauna a jikinka ne, yanda na rungumo hannayena a kirji ina jin tamkar kai na rungumo, ina fatan mu yi aure mu mallki juna dan in yi maka irin soyayyar da na tanada maka".

Tin da ta fara magana yake kallon É—an bakinta har ta kai aya, nisawa ya É—an yi kafin tamkar mai raÉ—a ya ce. "Why sai mun yi aure? Yanzu ma ai kina da dama".......... Taso dakatar da murmushin dake kan fuskarta, amma sai ta daure ta cigaba da yi dan kada tasa ya ji babu daÉ—i, abin da yasa murmushin nata ya so dakatawa shi ne wannan magana da ya yi yasa ta tuna ashe fa ba musulmi bane, abin ya yi mata zafi, daÉ—in soyayya yasa ta manta ba musulmi bane.

Bai san addini ba shiyasa zai ce yanzu ma tana da dama. Jin ta yi shiru ne yasa ya miƙo mata hannunsa a kan ta zo jikinsa. Ji ta yi jikinta ya kara yin sanyi, da kyar ta iya cewa. "King of my heart, ka bari sai mun yi aure ka ji? Zan zo jikinka har sai ka gaji". Cikin raunin murya ta yi maganar.
Chapter 96 · 0% Book details