← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 130

Sashe 78

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A natse guyson ya ce. "Alhmdllh, ya jima bai tashi ba ai ciwon". Jinjina kai Big Bro ya yi kafin ya ce. "Ya kusa daina tashi ma ai, ku yi barci zuwa da safe kazo mu yi magana ka ji?".
Kai suka jinjina a tare kafin su koma ciki, dadduma da Alkur'ani suka É—auka suka nufi wajen ajiyewa. Yana tsaye yana kallonsu har suka ajiye, sanna ne suka juya suka nufi saman bed. Sai da ya ga sun kwanta sannan ya juya ya rufo masu kofa.

Yana tafiya Ronnie ya ce. "Omar kana da budurwa ne?"......... "Mata dai nike da". Ya bashi amsa yana jawo bargo. Cike da mamaki Ronnie ya ce. "Mata kuma Omar?". Kai ya jinjina yana É—an lumshe ido.

"To yakamata ka haÉ—amu mu gaisa, sannan kuma kana da mata zaka kwana dani a nan? Ita fa da waye zata kwana?".
Kallonsa guyson ya yi kafin ya ce. "Ai ba'a É—aura mana aure ba, kawai za'a É—aura ne". Ajiyar zuciya Ronnie ya sauke. "Okey na fahimta, yanzu na gane, to ka haÉ—amu mu gaisa". Make mashi kafaÉ—a Omar ya É—an yi kafin ya ce. "A'a ba yanzu ba, bari sai bayan aurenmu zaka ganta da nikaf".

To shi Ronnie bai san me nikaf ba, dan haka sai ya ce to shikenan ALLAH ya kaisu lokacin. Da Amin guyson ya amsa, daga haka suka yi shiru kowa ya hau yin addu'ar barci.

A ɓangaren Big Bro ma yana komawa room ɗinsu saman bed ya haye ya kwanta, ya juyo da face ɗinsa suna fuskantar juna da ita, sai kallonta yake yi, dik yadda ya kai da baya son haske a ɗaki in zai kwanta yau sai da ya bar haske saboda ya yi ta kallon face ɗinta har barci ta yi awon gaba da shi..............ASUBA TA GARI.

-----------------------🔥

7:30AM.
A hankali ta motsa kyawawan idanunta ta warosu waje, da kyar ta iya miƙewa, barci bai gama isarta ba, da kyar ma ta iya tashi ta yi sallar asuba ta mayar da barci.

Yaye bargo da ta lulluɓa ta yi, sannan ta zuro kyawawan kafafunta kasa, ta saba da kwana a room ita kaɗai, so yanzu bata saba da su biyu ba, dan ko da Pretty ta je Black World kunga ai na koyaushe suke kwana a tare ba, da Smart take kwana, so ta saba ita kaɗai, mancewa ta yi yau su biyu ne a ciki shi da ita, miƙewa tsaye ta yi tare da rike waist ɗinta da hannu dikka biyu tana ɗan miƙa. Sai da ta gana sannan ta kai hannu ta danki kasar rigarta tare da yin sama da shi zata cire ta shiga toile unexpected idanunta suka sauka cikin nasa.

Ai bata time da ta yi ihu ta saki rigar a miliyan ba, zazzaro mashi idanu ta yi tana kallonsa, shi kuma tamkar wanda ya suma idaunsa a kan kirjinta da wuyar rigar ta yi kasa. Ganin ba fuskarta yake kallo bane yasa ta yi gaggawar bin in da yake kallon da ido.

Ai tana ganin tula-tulanta a waje bata san time da ta rarumo bargo ta kudunduna a ciki ba. Wata uwar harara ta dalla mashi a lokacin da ya É—ago da kallonsa kan fuskarta. "Me kake wani kallona?". Cikin tsiwa ta faÉ—a, bama ta san ta yi maganar ba fa.

Shiru bai daina kallonta ba, da sanyin safiyar nan ta motsa mashi bar gadon, dik sai ya ji ya kasa motsawa, dama so yake yi ya je wajen King, amma ta kara jefasa cikin wani hali. Ganin bashi da niyar yin magana ne yasa ta nufi toilet da bargon a jikinta. Binta da kallo ya yi yana jin tamkar ya jawota jikinsa ya rungume ko zai ji sanyin abin da yake ji, amma babu hali.

Haka ya zauna a wajen shiru har ta fito É—aure da towel a kirjinta, a karo na biyu ta manta da mutum a É—akin ta fito É—aure da towel, kun san in baka saba abu ba sai a hankali, akwai wahala.

Ai a wannan karon yana kallonta sai da ya ɗan yunkura kamar zai miƙe, dan yadda ya ga skin ɗinta yake wani glowing, kun san yadda skin na Koreans yake, abin ba'a magana.

Yunkurwan da ya yi ne ma yasa ta farga akwai mutun a É—akin, da sauri ta juyo da kallonta a kansa, yadda kuka san zai cinyeta da ido haka yake kare mata kallo. Harara ta dalla mashi kafin ta juya da sauri ta koma toilet, bargonta ta É—auko ta fito, ta kudundune jikinta a ciki ta dawo cikin É—akin.

A gaban mirror ta tsaya, lotions ta fara shafawa, sai kuma ta ga dik in da ta yi sai ya bita da ido, hakan yasa ta fasa shafawar ta nufi closet É—insu. Kaya ta fitar riga da wando, rigar mai doguwar hannu ce, ita ma wandon haka doguwa ce, very silky haka, sai ta É—auko headband na kayan. A cikinsu ta shirya, ta yi balain kyau sosai, sannan ta fito ta koma shafa lotions É—inta.

Dik wani motsinta a kan idaunsa. Dryer da ta gani a wajen ta jona zata busar da gashinta. Unexpected daga bayanta ta ji an karɓi dryer, tasan shi ne dan haka ba tare da ta juyo ba ta ce. "Ka manta ba zaka taɓani ba?"

Shiru ya yi bai yi magana ba har ya karɓi dryer ɗin sannan ya ce. "Ban ce ba zai taimaka maki ba ai". Ya faɗa yana watsa gashin kanta da hannunsa, ya hau busar mata da shi. Har cikin ranta ta ji mugun daɗin hakan, sai dai bai kai ga karisar mata ba Smart ya yi masu knocking a kan ya zo su je wajen King su gaida shi.

Ba dan ya so barinta ba ya bi Smart suka nufi part na King, sun manta jiya ya ce su fara duba Akka kafin shi.

Yau dai zauna suka isko king a saman shinfiÉ—ar dake a room É—insa, yana rike da cup of cappuccino yana sha, gefensa momma ce zaune, É—ayan gefensa Ramish ne a zaune.

Suna shigowa King ya saki murmushi yana kallonsu kafin ya ce. "Omerish rufe kofar gabaÉ—aya dan ma kada wani ya sake shigowa". Da alama iya su da suke wajen King ya yarda da su, da momma, da Ramish and Big Bro da Smart.

Datse kofar Smart ya yi suka kariso ciki. Dikkansu a gefe da gefen King suka zauna suna É—aga mashi gaisuwa cike da tsantsar so da kauna. Big Bro ya zauna a kusa da Momma, shi kuma Smart ya zauna a gefen da Ramish yake.

Fuska a É—auke da fara'a King ya amsa. Abin ya yi mugun É—aurewa momma da Ramish kai, su sun san King bashi da fara'a sosai wlh, ana jimawa kan ya yi murmushi, to meyasa tin daga daren jiya zuwa yau yake da faman murmushi ne?. Ta jefi kanta da tambayar da bata da amsarsa.

Shiru É—akin ya yi na É—an lokaci, King ne ya katse masu shirun da cewa. "Na yi alkawarin faÉ—a maku abin da ya faru a baya jiya, amma fa ku sani zaku sake rasa kannenku guda biyu a karo na biyu". Ya É—an yi shiru yana kallon fuskokinsu.

"Tabbas zaku sake rasa Omar da Aneesa in har na buÉ—i baki na faÉ—a maku gaskiya". King ya sake faÉ—e.

Dik cikinsu Big Bro ne kawai kirjinsa bata buga ba, saboda shi kalamai basa razana shi, amma Smart da Ramish and Momma sai da kirjinsu ya buga da karfin gaske.

Ta maza Smart ya yi wajen cewa. "Dad mun yarda ka faɗa mana kawai"................ kallon king a kan momma ya ce. "Rahilarh ki yi hakuri da abin da zaku ji, na ɓoye maku sawon lokaci ba dan komai ba sai dan gudun ɓacin ranku, amma yau zan faɗi komai, zan yi fatan ku yafe mun".

Shiru dikkansu suka yi, sai momma ce ta daure ta ce. "Babu komai, In Sha ALLAH zamu fahimceka".

Gyaran murya king ya yi kafin ya ce. "Ramish ka yi hakuri da abin da zaka ji, dan nasan ba zai yi maka daÉ—i ba, sannan nasan ban kyauta maka ba, babu yadda zan yi ne yasa".

Shiru suka É—an yi, Ramish da zuciyarsa ke bugawa da karfi tamkar zai fasa kirjinsa ya fito ne ya ce. "Dad tin ma ban ji me ka yi mun ba na yafe maka wlh".

Jinjina kai kawai King ya yi kafin ya tsaida kallonsa a kan Smart, sannan ya ce. "Omerish zan amsa maka buƙatar ka, wacece mahaifiyar Ramish, to hakikanin gaskiya ni kaina ban san wacece takamaiman mahaifiyarsa ba, abin da na sani kawai shi ne Ramish ɗana ne, kuma ba ɗan Aleezarh (Mama) ba ne".

Dum!!! Dum Ramish da ya ji maganar tamkar saukar aradu ne ya yi gaggawar sanya hannu ya dafe kirjinsa dake barazanar tarwatsewa. Hannu Smart yasa ya dafa shoulder É—insa, dan dik sun lura da halin da ya shiga. A hankali Smart ya fara shafa gefen bayansa alamar rarrashi da kwarara mashi gwiwa.

Kawar da kallonsa daga kan Ramish King ya yi sannan ya cigaba da cewa. "Da Rahilarh, da Aleezarh, da Umaiyya sun haihu ne a rana guda, wanda dama na yi wa Blood power alakawarin zan basu jinin ƴaƴana guda biyu su shanye sai in yi amfani da kashin bayan ƴaƴan nawa biyu in kera makullin spender dan rufe blood power, to shi ne a ranar da suka haihu sai na ɗauki biyu daga cikin yaran, na san dai na ɗauki ɗan Aleezarh, to cikin Rahilarh da Umaiyya su ne ban san ɗan waye na bada a ciki ba, Rahilarh ɗanki da kika haifa a tsakanin Omerish da Jaish a kansa nake magana, batu na gaskiya ba mutuwa yaran suka yi kamar yadda kuka zata ba, ni na bada su saboda in dakatar da ɓanar da su daddyna suka faro".
Chapter 78 · 0% Book details