← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 130

Sashe 123

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cigaba mammie ta yi da ƙoƙarin sosa azaban da take ji a kan fuskarta ko zata samu sassauci, tana kara kwaye namarta dake wajen. Sam babu alamar tausayi dede da kwayar zarra a kan fuskar Big Bro, hankalinsa a kwance ma ya dawo da kallonsa a kan King. "Daddy bana san sake ganinta a nan kuma". Ya faɗa tare da miƙewa daga kusa da ita.

Ya juyo da nufin ya yi wa Momma magana sai gani ya yi ta sume, É—an zaro idanunsa waje ya yi har sai da yasa hantar jama'ar parlon kaÉ—awa, da sauri ya nufi in da momma take, suma kaf kai kallonsu kanta suka yi, cikin zafa King ya riga Big Bro karisawa in da momma take.
"Ku bani ruwa". Shi ne abin da King ya faɗa. Dikka family kan momma suka yi har su Jaish dake kan guyson yanzu sun koma kan momma. Ita kuwa Mammie sai kururuwar azaba take saki amma babu wanda ya bi ta kanta. Wannan azaba da Big Bro ya yi mata ba karamar azaba bace, ya dafar mata da namar jikinta, ga shi bata mutu ba, haka zata yi ta fama da wannan azaba, babu maganin da zai iya warkar mata da wannan konewa, a haka zata yi ta fama har rai ya yi halinsa, daga nan ko shekara goma zata kara kullun ciwon zai kasance sabo ne, namarta ya yi ta fitar da farin ruwan azaba mai yauki da wari, fuska da hannunta dik zasu yi ta tsutsa ne, haka illar yawunsa take idan ya juya black heart ɗinsa ya tofa maka, ita dai tata ta kare, kuma ta samu karshe mai bakar azaba da wahala, ta cuci kanta a banza!. IZINA CE A GAREMU, DIK WANI AZZALUMI KARSHENSA BATA KYAU, TO ME AMFANIN MA KA ZAMA AZZALUMI KANA CUTAN ƳAN UWANKA FISABILILLAHI? WAI KO KA MANTA DUNIYA TAMKAR CIN KASUWA MUKA ZO YI NE ZAMU KOMA GIDA NA GASKIYA GIDAN SAKAMAKO?.

Wani irin dogon numfashi momma ta ja tare da saukewa a hankali, sannan ta waro idanunta da har ɗan kunbura suka yi waje. A natse ta miƙe zaune tana ta faman sauke ajiyar zuciya. Sannu suka hau yi mata kowannensu cike da damuwa a kan fuskarsa.

Jinjina kai kawai momma ta yi ta gagara yin magana. Miƙewa Big Bro ya yi ya ɗauketa cak suka bar parlon, dan baya son ta ga abin da ta faru da Mammie bare hankalinta ya kara tashi.

Warriors King ya kira suka fita da Mammie, ya ce su sanyata cikin kejin da suke sanya kananan masu laifi kafin a san irin hukuncin da za'ayi mata. Sannan yasa su Dr Raj suka É—auki guyson da su twins dik suka kwantar da su a saman sofa, Dr Raj ya hau yi mashi treating forehead É—insu da ya farfashe.

Mummyn Chucha and King ne suka rufawa Big Bro da momma baya, mama ta tsaya wajen Aneesa tana ta hawaye. Ronnie ya matso dan tasa Dr Raj aiki tin da dik aikinsu iri ɗaya. Sweetie kuwa da kyar ta iya miƙewa ta bi bayansu King, Smart da Jaish sai da suka tabbatar da guyson and twins sun samu kulawa hannun su Ronnie sannan suka bi bayan momma.

Zaune suka iskosu a parlo Big Bro yana zaune a gefenta, ya riko hannunta cikin nasa yana ƙoƙarin tausarta. A gefenta suka zazzauna suma, King da Mummyn Chuchu suna zaune saman sofa guda suna kara tausan momma.

Gagara hakura momma É—in ta yi har sai da ta ce. "Meyasa ka yi wa Æ´an uwanka irin wannan duka haka?". Ta faÉ—a tana kallon yatsun Big Bro É—in yadda yake É—an murza nata a hankali. Shiru ya É—an yi for almost 2 mins kafin ya ce. "Ba dukansu na yi ba, bama su na daka ba, shaiÉ—anin dake jikinsu na daka, shi na fitar masu".

Ai momma bata san lokacin da ta sauke wani irin musulmin ajiyar zuciya ba. Daidai lokacin Dr Raj ya shigo hannunsa rike da wayar king. "Daddy kira yafi kona ajere-ajere yake ta faman shigowa". Dr ya faÉ—a.

Karɓar wayar King ya yi tare da duba call ɗin, da sauri ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin bin number ya kira tare da nufar waje yana ce masu yana zuwa. Kira ne da Anti-Ballistic Missile Systems office ɗinsu na kasar. Wannan kira alamar babu lafiya ne, shiyasa ya fita waje.

Mummyn Chuchu macece mai fahimta sosai, ta fahimci tamkar momma tana son ganawa da ƴaƴanta kawai, dan haka sai ta miƙe tana faɗin. "Ina zuwa bari in duba jikin su Omar". Da to momma ta amsa mata, waje ta nufa da sauri.

Tana fita momma ta riko hannun Big Bro, idanunta a cike tab da kwallah ta ce. "Wai menayiwa mutane ne? Mena tare masu da basu son barina in zauna lafiya? Meyasa Æ´aÆ´ana ne kawai ake azabtarwa a cikin gidan nan? Kowani ciki na samu sai na sha azaba kafin ya zo duniya, ayi ta tsoratani ba'a son in haihu, idan ya zo duniya ba za'a barshi ba, na haifeku ku biyu, an rabaku tin ban san me na haifa ba, an É—aukeka daga gareni, ban sani ba haka yasa na maida hankali kan renon Omerish, shi ma aka sakoshi a gaba, har aman jini jariri da shi yake yi, muggan mafarkai a kansa ta yi mun yawan da ba zan iya jurewa ba, yaron nan yana jariri sai in ga nunfashinsa ta É—auke na Æ´an mintuna sai kuma in ga ya dawo daidai, wani lokaci ya yi ta fafutuka yana bubbuga kafafunsa da hannunsa alamar an shake mashi wuya baya samun nunfashi, sai na rungume shi a jikina in yi tai mashi addu'oi, naga abin ba mai karewa bane, na shirya shirin cewa ya mutu, na kaurar da shi daga gidan nan. Haka na sha kukan rabuwa da É—ana na farko a duniya dik dan ya rayu, na zo na sake haifan wani yaron shi ma kun ji ya daddynku ya yi da shi, baya ga haka, na haifi Jaish, shi a Dubai na haifesa shiyasa abin yai mun sauki, Omar tin yana karami yake fama da ciwon cikin da bamu iya sanin na menene bane, mahaifiyata ta sha fama kansa, tamkar ba zai rayu ba.
Haka dai ALLAH ya raya mun shi, Omaid da Obaid dama tin da suka taso a mugayen nan marasa jin magana da kiriniya nasan ba lafiya suke ba, na rinƙa yi masu addu'a wanda ina da tabbacin shi ne ma yasa abin nasu ya yi sauki, har Zunaira ba'a bari ba, an kasheta an jefar da gawarta a cikin ruwa, amma ALLAH yasa tana da rabon rayuwa, ta tashi, bansan meyasa ku kawai aka sakawa ido ba, wai menayi ne?".

Ta kai karshen maganar da kyar hawaye sun gama wanke mata fuska. Da sauri su Smart har suna rige-rigen goge mata hawaye. Cikin sanyin murya Big Bro ya ce. "Komai ya kare, babu wanda zai sake taɓa mun ƴan uwa na barsa, su Omar dik yanzu zasu samu lafiya, sannan zan gano koma wanene ya saka mun ƴan uwa a gaba, zan yi mashi hukuncin da sai kun gamsu ya biya azabar da yasakaki a ciki, but ki mun alkawari ɗaya". Ya dakata yana kallonta.

"Tin ban ji me kake so ba na yi maka". Ta faÉ—a yana riko hannun Smart da É—ayan hannunta. "Ki mun alkawarin ba zaki sake kuka ba kuma kome kike so zaki tinkareni kai tsaye ba ki ce kina tsorona ba". In a cool way sosai ya faÉ—i maganar. Da sauri ta jinjina mashi kai alamar ta yi alkawarin hakan.

Shiru wajen ya É—an yi na Æ´an mintoci kowa da abin da yake tinani, can ta katse masu shirun da cewa. "Menene sunanka? Tin da kazo nike son tambaya amma na kasa".

Ajiyar zuciya su Smart suka sauke saboda an taɓo in da yake yi masu kaikayi. Silent for almost 2 mins Big Bro ya yi kafin a natse ya kalleta sannan ya ce. "Tin da na tashi sunana Tiger, ban san wani suna ba, amma ki sakamun da kanki zan so hakan".......... Tabbas yana da suna, amma in baku manta ba da Duniyar Shaiɗanu suka sake shi ai komai da ya dangancesu ya shafe daga kansa, ya mance komai nasu, ciki har da sunan da suka saka mashi.

Shiru momma ta É—an yi, yana son tambayarsa waye ya renesa, amma tana shakka, dan haka sai ta ce. "Na baka suna Unays daga yau"........ Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya É—an jinjina kai yana maimaita sunan, shi kansa sunan ta yi mashi masifar daÉ—i, UNAYS WOW.

Dawo da kallonta a kan Smart ta yi. "Ina Æ´ata?"....... ÆŠan zaburs Smart yai tare da mikewa da sauri. Da kallo momma ta bisa, dama ta tambayesa ne dan ta tabbatar da zarginta, kuma ta tabbatar, dan haka sai ta ce. "Koma ka zauna bari in dubata".

Wannan magana da tai yasa Jaish da Big Bro suka fahimci karatu. Miƙewa momma tai ta nufi waje tana faɗin. "Unays ka jirani bari in dawo ina da magana da kai". Ta faɗa mashi hakan ne dan bata son ya tilasta Sweetie ya ɗauketa su tafi, so take tai magana da shi kan wannan issue.

Tana fita Big Bro ya dallawa Smart harara kafin ya ce. "Zo nan bari in bincikeka"......... Smart ya gane nufinsa sai ya ce. "A'a fa, yanzu ba É—aya muke ba, ka bini a han........". Bai karisar da maganar ba sakamakon capka da Big Bro ya kai mashi a gashin kai, ya jawosa jikinsa yana faÉ—in. "Bari in fara tantancewa tukun nan".

Jaish sarkin kunya da ya gane in da suka dosa sai ya miƙe sumui-sumui ya gudu waje abinsa, sun bashi kunya. Cike da zolaya Smart ya ce. "Za fa ka je ka tada abin da kasan kai ba samu zaka yi ba, sai dai ka rungumi pillow ka rungumi sorry, dan haka kada ka tono wanna lamari". Yana magana yana kara rike wandansa dan kada Big Bro yai mashi tsirara dik da yasan da wuya ya yi hakan, kawai dai tsantsar so da kauna dake tsakaninsu ne yasa Big Bro yake ɗan sakewa da shi har yana jansa da wasa.
Chapter 123 · 0% Book details