← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 130

Sashe 119

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya take yi a cikin dokar daji ta gefe-gefen ruwa, hannunta rike da wani ɗan sanda tana busa, abin mamakin shi ne ba tafiya take yi a kan kafunta ba, a kan iska take ta yi, tana busa tana juyo tamkar wacce ke yin rawa. Lokaci guda ta dakata da busar da take yi sakamakon jin alamar kukan jariri da ta yi, sai kuma ta sauko da fararen kafafunta kasa ta taka ƙasa, shiru ta ɗan kasa kunne tana wuwwurga eyesball ɗinta a wajen dan gano ta ina take jin wanna kuka.

Tabbas kukan jariri ne, da sauri ta tashi sama dan ta gano daga in da kukan yake rashi, wasu korayen ganye ta keta ta wuce cikinsu, take ta bayyana a bakin wani tapkeken teku mai girma wanda kuma shi ne dai wannan teku da ya raba Kingdom of Power da Kingdom of Justice, watau tekun da su Kamran suka rayu a kusa da shi.

Da sauri wanna mata ta karisa in da take hango farin towel tas a wajen. Tana zuwa ta kai hannu ta É—auki towel É—in, ashe jariri ne a kudundune a ciki yake ta kuka, ko cibiya ba'a yanke mashi ba, sannan jikinsa dik jini alamar yanzu ma aka haifesa. Juyawa wanna mata ta yi gabas da yamma kudu da arewa babu wani alamar mutum mai rai a wanna waje, hakan yasa ta rumgumi jaririn nan ta tashi sama da shi.

Tafiya ta soma yi a yanayin da mutum ba zai iya kallonta ba. Ta yi tafiyar da in da mota ne sai an kwashi awa huÉ—u masu kyau ana yinta, sannan ta dira a wani daji mai cike da tsaunika masu girman gaske, ga dogayen bishiyoyi masu duhu, sam-sam babu alamar halittar É—an adam a wannan waje, waje ne ma abin tsoro.

Cikin tsaunikan ta fara kutsawa har ta karisa wajen wani babban tsauni har sama wanda daga ta bayansa yake aman ruwa yana kwaranya ta gaba. Wannan tsauni yana da katafaren kogo daga ta katsa. Wannan kogo ta shige ciki da wanna jariri, wani sabon duniya ne a wannan waje, wanda in baku manta ba a baya na faÉ—a maku yadda tsarin Duniyar ShaiÉ—anu yake, to nan ne.

Kai tsaye fadar sarkinsu ta nufa, yana zaune a saman wani haÉ—aÉ—É—en kujerar da shi ma na gaya maku yanayin mulkinsu. So ba sai na tsaya dogon jawabi ba, mu je kawai.

Yana ganinta ya miƙe tsaye, shi ma sanye yake da fararen kaya har suna jan kasa, yana da dogon gashi har gaba da gwiwowinsa, kuma gashin kan nasa fari ne tas babu ɗigon baki, idanunsa gwanin ban tsoro, dara-dara da su.

Cikin matsuwa da son samun amsa ya ce. "Sarauniya Elvender ina kika shiga tun ɗazun nike ta nemanki". Murmushi ne kawai a kan fuskarta ta gagara rufe bakinta, gabansa ta kariso tana nuna mashi jaririn tana faɗa mashi yau ta yi tafiya mai dogon zango a nan ta samu wanna jariri. Da azama yasa hannu ya karɓi yaron yana kallonsa.

Shi ma take murmushi ta bayyana a kan fuskarsa, ya nuna tsantsar kaunarsa ga wanna jariri, ya ce ta jira shi bari ya faɗawa sauran muƙarraban fada cewa ya samu karuwar yaro.

King Lucian wato sarkin Duniyar Shaiɗanu mutum ne, while matarsa Elvender ta kasance aljana ce wacce suka yi soyayya mai tsanani, ta hana Lucian raɓar kowace mace, ta ɗaukesa zuwa duniyar aljanu suka yi aure a can, shiyasa kowa yake ta ce Lucian ya ki yin aure, idan ma aka yi mashi maganar aure a gida ɓatawa yake yi da kowa, dole aka rabu da shi.

Ba wanda ya san da Elvender sai mukarrabansa na Duniyar ShaiÉ—anu, su kaÉ—ai suka san da ita saboda kusan suna tare da ita ne, da sanya hannunta a wallafa Duniyar ShaiÉ—anu, da taimakonta, ba mutuniyar kirki yadda kuke zata bane, kawai dai tana son yara ne yasa ta zama mai sauki kan wannan jaririn da ta tsinta, ta kuma shayar da shi saboda son da take yi mashi, ta É—aukesa tamkar ita ta haifesa, dik in da zata je yana jikinta, ta soshi fiya da kanta.

Sai dai kuma da zuwansa Daular da kwanaki biyu suka fahimci wanna ba kamar sauran mutane bane, yana tattare da baiwa mai tarin yawan gaske, wanda a nan ne suka fitar da dokar killacesa kada ya yi mu'amala da kowa, tin daga wanna lokaci ta daina fita da shi, saboda dokace kada a sake bari ya ga hasken rana, daga nan rayuwarsa a cikin ɗaki ta fara, sun ce shi ne zai maye gurbin sarki, a yayin da Elvender ta bayyana shi a masarautar aljanu da cewa shi ne magajinta kuma shi zai hau kujerarta na sarauniya a wanna Daula, tin yana da kwanaki goma a duniya ya samu naɗin sarauta na masarautu har biyu, na aljanu da kuma Duniyar Shaiɗanu, har yau kuma dikka waɗan nan masarautu babu kowa a kan kujerarsa, suna jiran dawowarsa garesu ne kawai ya cigaba da mulkansu, aljanu na jiransa, Duniyar Shaiɗanu na jiransa, ba iya wanna ba, yana da muƙamai da dama, shi ɗin ba iya King Of Black World bane kawai, King Of Evil World, Kingdom of Ice Kingdom, masarautar iyayen king Lucian mahaifinsa kenan, suma suna da saurauta, sannan King Of Blue Kingdom (masarautar aljanu na su Elevender) kai muƙaman da yake da shi ba zasu kirgu ba, sai gaba, Blue Kingdom suna jiransa har yanzu, hakan ke haifar da tsananin kaifi a idanunsa da kallonsa yake razana mutane, su king dik suke shakkarsa, aljanun suna tare da shi, suna mashi kallon jikansu ɗa ga Elevender, kunga kuwa dole Big Bro ya kasance yadda yake, fin haka ma idan ya kasance ba abin mamaki bane, dole ko yawun bakinsa kawai ta zama wata abar, mu koma kan labari.

In baku a taƙaice yadda zaku gane Elevender ita ta shayar da Big Bro har ya kai shekaru biyu ciff, a ranar da ta yayesa a ranar aka naɗa shi sarautar last born of Evil World, daga kansa aka datse aihuwa, ba'a yarda wata ta sake haihuwa ba, idan mace ta samu ciki ma binneta da ranta suke yi ko su soketa yadda na baku labari a farkon da na kawo maku labarin Evil World ɗin.

Dan haka daga kansa ba'a sake haihuwa a Daular ba, sanna a wanna shekaru biyun nasa aka naɗa shi sarautar Ice Kingdom, suna mugun ji da shi, kuma har lokacin baya fita ko parlo. In takaice maku labari yana da shekaru huɗu Elevender ta kamu da ciwo, ta kwanta jinya sosai, amma ashe ciwon bana tashi bane, ta mutu, sai dai kafin ta mutu ta baiwa King Lucian wasiyar cewa ya ɗauke mata Big Bro daga Evil World, idan har yana sonta da gaske to ya je wani waje ya renan mata ɗanta, idan ya girma ya sanar da shi cewa mahaifiyarsa ta ce lallai ya mulki duniya, wanna ita ce wasiyarta a garesa, ko ta halin yaya ya zama sarkin da duniya dik zasu kasance masu yi mashi biyayya, wanna shi ne burinta, ta so ta renesa a kan haka amma mutuwa ya yi mata yankar kauna, dan haka lallai King Lucian ya bawa ɗanta saƙonta.

Bayan ta gama rubuta wanna wasiya a takarda, tasa Lucian ya kaita ɗakin da Big Bro yake killace, sannan tasa aka kawo mata wuƙa. Ta yanka hannunta, wani irin farin ruwa ya fara zuba daga in da ta yanka, Big Bro yana kwance yana barci ta matse bakinsa ta zuba mashi wanna ruwan, sannan ta ce har ya mutu ba zai daina sonta ba, kuma zai cika mata umarninta, and ba zai taɓa daina son Blue Kingdom ba koda iyayensa na gaskiya sun bayyana.

Ta yi mashi abubuwa da dama kafin mutuwa ya risketa, to fa daga nan ne King Lucian ya fara ƙoƙarin ɗaukar Big Bro su bar Evil World dan cika maganar masoyiyarsa, ya shirya komai da zai buƙata, ya bi dare ya bi rana ya ɗaukesa daga ɗakin da aka killacesa a ciki, ya raba Evil World da autansu, suka yi tafiya mai nisan gaske, sai da ya samu dajin da ta yi mashi kusa da wasu kauyoka, a nan kafa Daularsa, ya sassari bishiyoyin dake dajin, ya fara gina birninsa.

Da ya fuskanci Evil World suna neman Big Bro ido a rufe ne sai ya yi magic ya girke fadarda na Birnin Black World ta yadda ba zasu taɓa ganin Big Bro ba. Haka ya renesa a ɗaki matsayin zaki, ya renesa yadda Elevender ta so ya kasance, ya rura mashi wutar son mulkar duniya a zuciyarsa, da yake ya sha nonon Elevender sai ya taso da sha'awar magic da mulki, hakan yasa ya fara koya, yana karanta daga littafan baban nasa, babu wanda ya taɓa koya mashi, a hankali ya koyi komai har ma ya zo ya fi baban nasa iyawa. TO KUN JI DAGA IN DA YA SAMO SHEGEN SON MULKAR DUNIYAR NAN TASA KO?. A TAKAICE NE WANNAN, ZAKU SAMU WANI BAYANI DAGA BAKIN WANI DA BAI BAYYANA BA!. AMMA ME KUKE TINANIN YA KAI JARIRI CIKIN WANNA DAJI HAR ALJANA TA TSINCESA? MU JE ZUWA, MATSALAR DAGA CIKIN GIDA TA SAMO ASALI!.

Daga baya a hankali-hankali mutane suka fara cika birnin Black World wanda a hankali Big Bro zai baku labari da kansa ya aka yi suka mulki birnin. Dan haka mu koma kan labarinmu.

Shiru momma ta yi bata iya yin magana ba. Daidai lokacin Obaid ya shigo cikin É—akin da gudu yana ihun Yah Omerish zai kashesu.

A zabure momma ta miƙe tana tambayarsa lafiya?. Cikin kuka ya ce. "Yah Omerish ne zai kashe Omaid".

Cikin natsuwa momma ta ce. "Ina Omerish É—in?". Jikinsa har kerma yake yi wajen cewa. "Suna parlon daddy". Da sauri momma ta riko hannunsa suka nufi waje, bata tsaya jin doguwar bayani ba, gara ta je ta ganewa idanunta.

Suna shiga parlo suka isko gabaÉ—aya family kowa yana tsaye cirko-cirko, ga Sareena da Omaid suna zube a kasa saman gwiwowinsu, dik Smart ya farfashe masu jiki da dakakkiyar belt É—in hannunsa. Sai huci Smart yake yi tamkar zai kama da wuta.
Chapter 119 · 0% Book details