← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 130

Sashe 61

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga ita har Smart sun sha mamakin ganin yadda bai nuna damuwarsa a kan fushin da ta yi da shi ba, ko É—ago ido ya kalleta baya yi, zaka rantse da ALLAH baya a empire É—in ma gabaÉ—aya harkar gabansa kawai yake yi, harta Smart ya daina kula, Ronnie kawai yake kula kuma yake magana da shi. Ana saura kwana biyu zasu tafi Crown of Power ma kwata-kwata daga ita har Smart sun daina sanya shi a idonsu, kuma yana a cikin empire É—insa sabo, sai dai basu sani ba, sun sha nemansa a nan har suka gaji, da suka tambayi Ronnie sai ya ce masu kada su damu zai dawo, shi Ronnie yasan in da yake sarai, amma ya ki faÉ—a masu saboda Big Bro ya ja mashi kunne.

Wai su suke fushi da shi suke ɓoye mashi sai ya gwada masu ya fisu iyawa da yake ɗan duniya ne, dik wani motsinsu a kan idanunsa suke yi, ya fisu sanin ya suke kwana ya suke tashi, dikkansu yana kula da su fiye da yadda yake kula da kansa, dan ko zamewa suka yi zasu faɗi sai ya taimaka masu, amma su basu samu damar ganinsa, dik sun shiga damuwa, harta Smart mai bada shawara ya sha jinin jikinsa, shi bai san cewa dik abin da zai faɗa mata Big Bro yana jinsu ba da ba zai bata shawarar ta juya Big Bro baya a fili ba, shi ya ɗauka sirri suka yi, to ga shi yanzu bata juya mashi baya ba shi ya ladabtar da su dikkansu biyu, suna kuka suna danasai.

Ita dai Pretty ko a jikinta tin da ba Smart bane ya ɓata, dan haka ta ci ta koshi ta kwanta ta yi barci, shi ko Smart sai fama yake yi yana neman Big Bro a yayin da Big Bro yake ganinsu. Siririn tsaki ya ja kafin ya ce. "Black Tiger bai yi lalacewar da karamun halitta irinka zai shiga gonarsa ko ya ce zai iya nemansa dan ya matsa daga idon mutane ba". Ya faɗa yana shafa kyakkyawan hair ɗinsa, yana daga kwance a saman wani irin mahaukacin bed wanda zaka yi zatan ba'a kan katsa yake ba, wai wannan ma fa ba'a kammala kyara sabuwar empire ɗin ba. Da zallar gold aka yi wannan bed ɗin, sai wani kyalli yake yi yana ɗaukar idanu, ga wasu kwayayyen lantarki dake haskaka headboard ɗin suke karawa gold ɗin kyalli.

Shi dai Smart bawan ALLAH ya yi sansanin wannan shawara wlh, dik ya shiga damuwa over, dik da ya kasance a ko'ina ana kiransa Smart, to fa birnin Black World da kuma Big Bro sun sa ya ji tamkar shi ɗin bashi da wani kaifin ƙwaƙwalwa, dan karamin abu yana gagararsa warwarewa a birnin nan, birnin tana da sarkakiyar da bai saba gani ba, yana shiga ruɗani wani lokaci, har yau ya rasa gane alkiblar wannan birni, shi dai ga shi nan ne yana ganinsu kawai.

A daren washegarin da zasu tafi Crown of Power dukkansu babu wanda ya iya cin abinci, saboda damuwar in da Big Bro ya ɓace, shi dai Ronnie ya ci ya ƙoshi abinsa, amma sun bashi tausayi har ya ji tamkar ya sanar da su in da Big Bro yake, sai dai tina cewa ran yayansa zai ɓaci idan ya faɗa ne yasa ya daure ya kawar da kansa.

Haka suka kwana da yunwa, da safe suka karisa shiryawarsu, suka tsala wanka, suka shirya cikin kayan sarauta irin na birnin wanda duwatsun jikin kayan kaf da É—anyar gold aka yi su, covers na kafarsu kawai zata bada amsar daga Black World suka fito, saboda gold dake a jikin takalman.

Shi kansa Big Bro ya shaida sun yi kyau sosai, sai dai Smart and Sweetie damuwa ce karara a kan fuskarsu, shi Smart tsoronsa shi ne kada ace Big Bro ba zai bisu ba! Ita kuma Sweetie damuwarta shi ne kewarsa, dik yana ganinsu kuma ya karanci dik tinanin dake a cikin zuƙatansu, sai dai ko a jikinsa, bai damu ba ya hau nasa shirin.

Sai around 11 na rana suka kammala, sannan wasu shirga-shirgan motoci suka zo suka É—aukesu zuwa BLACK TIGER INTERNATIONAL AIRPORT. Har suka isa airport hankulansu a tashe, dan babu Big Bro.

Like wow, gaskiya Smart ya kara sarawa karfin arzikin É—an uwan nasa, a lokacin da suka ga jiragen da zasu tafi da su Kingdom of Power sai da suka girgiza, wani dankareran jirgi ne wanda kana ganinsa kasan ya amsa sunansa, ga shi sabo fil yana ta kyalli, kun san dik jiragen birnin da tambarin Black Tiger a jikinsu ko? To haka shi ma wannan, da É—anyar gold aka yi zanen sunan. Ga wasu kananan drones na yaki guda shidda waÉ—an da zasu zama tsaro ga jirgin nasu, sai wasu jet biyu da zasu wuce gaba kafin jirginsu ya É—aga.

Smart ya kara jinjinawa karfin ikon da Big Bro yake da shi, yanzu ya kara tabbatarwa da kansa ashe dole Big Bro ya yi balain ji da kai da izza, ashe dai ba ƙaramin abin ya taka ba, a dole masu jajayen kunnuwa su ɗaga mashi kafa, sai sun jira wlh.

GabaÉ—aya ma'aikatan airport É—in robot ne kun sani, dan haka suka bubbuÉ—ewa su Smart kofofin motocin suka fito, yana rike da hannun Pretty da ta sha kwalliya tamkar wata gimbiya, ko da yake ita ce gimbiyar Crown Of Power, tab Pretty gimbiya, kamar yadda Mommah take gimbiya idan King ya sauka Smart ya hau mulki fa mommah zata koma Queen mother Pretty ta zama tauraruwa da ake ji da ita, to ALLAH yasa kafin wannan lokaci shirme da yarinta ya bar kanta ta natsu ta san kasa guda ce a hannunsu.

Rike da hannun Sweetie Ronnie ya fito suka nufi jirgin, an kammala komai, dan haka suna shiga basu wani ɓata lokaci ba ƙananan jet ɗin suka tashi da kamar mintuna 20, sannan drones na yaki biyu suka ɗaga kafin jirginsu ya ɗaga, drones na yaki huɗu suka rufa masu baya.

Smart ya kara shiga damuwa da tsoron rashin ganin Big Bro har suka tashi, amma Ronnie ya ce mashi kada ya damu In Sha ALLAH tare zasu ce Kingdom É—in ya kwantar da hankalinsa. Yasan yanda Ronnie yake da Big Bro, amma dik da haka hankalinsa bai kwanta ba har duka keta hazo.

To mu dai sai dai mu ce a sauka lafiya, hmmmm AN ZO IN DA NIKE SON A ZO, BIG BRO A KINGDOM OF POWER, YANZU LABARIN ZAI CANZA SALO, YANZU ZAMU DAWO TAFIYA KAN MUKAKKIYAR HANYA KAN LAYI GUDA, SHIYASA NA CE MAKU MUN SHIGA SABUWAR DUNIYA, SABUWAR DUNIYAR NE DA GASKE, YANZU KOMAI ZAI CANZA, YANZU WASAN ZAI FARA, FATAN SU ISA LAFIYA AKWAI KALLO!.

CROWN OF POWER.🔥🔥

Har karfe 9 na safe bata farka daga barci ba saboda jiya bata yi da wuri ba, tana a cikin barcin ta ji ana tattaɓata ana ambatar sunanta. A hankali ta waro idanunta da suka yi jajir suka yi luhu-luhu, kai tsaye sai a kan Mahnoor ta saukesu, ɗan tsuke fuska ta yi kafin ta ce. "Adda Mahnoor me haka zaki tasheni daga barci". Ta yi maganar tana miƙewa zaune.

"Tashi zaki yi mu je mu duba jikin aunty Sareena bata da lafiya". Siririn tsaki ta ja kafin ta ce. "To ni ina da wata alaƙa da ita ne da zanje dubata? Ta mutu ma mana". Ta faɗa tana ɗaure fuska.

"Ni kam Mahreen yaushe zaki yi hankali ne? Ta mutu fa kika ce?". Shiru bata yi magana ba, É—an É—aure fuska Mahnoor ta yi. "Tashi ki yi wanka mu je mu dubata, kowa yana part É—insu ban da mu".

Tana turo baki ta ce. "To wai me ya sameta ne ma?". Har ta manta É—anyen aikin da ta yi wai tana tambayar meyasameta. A natse Mahnoor ta ce. "Momma ta ce gamo ta yi, ba'a dai san me ya sameta ba, dan har yanzu bata farfaÉ—o ba, idan aka sanya mata ruwa ta farfaÉ—o sai ta fara ihu tana faÉ—in ta tuba, daga nan sai ta sake suna, an rasa gane me yake damunta, yanzu dai ankira Dr yana dubata".

Sai yanzu ta tina abin da ta yi, tamkar zata watse da dariya sai kuma ta daure da cewa. "Bari in yi wanka in yi sallah sai mu je in dubata".

Ɗan zaro ido Mahnoor ta yi. "Kina nufin baki yi sallar asuba ba?". Kai ta gyaɗa ba tare da ta yi magana ba, daga haka ta sauko kasan bed ɗin ta nufi toilet. Bayanta Mahnoor ta bi da kallo tana mamakin halin Mahreen, yarinya kamar rainon aljanu? Miƙewa ta yi ta koma bedroom ɗinta dan ita ma ta shirya.

A can ɓangare kuwa, Obaid ne zaune a tsakiyar gadonsu yana bin ƙafafuwansa da kallo, idanunsa a kan shatin bulalar da suka kwanta mashi sun yi ruɗu-ruɗu. Da farko da ya farka daga barci ya zaci mafarkin mala'ika ya yi, ya kuma yarda a kan mafarkin ne, sai yanzu da gari ya yi haske ya ga zanen mulala a jikinsa ne ya fara tantanama a kan mafarki ne, a jikinsa yana jin wani ne ya yi mashi wannan abin. Datse idanunsa ya yi yana ƙoƙarin tuna abin da ya faru, yana ɗan shafa kafar tasa a hankali-hankali.

Omaid ne ya shigo É—akin bakinsa da sallama, da sauri ya ja wandon jikinsa ya rufe zanen bulalar dan ma kada Omaid ya gani, saboda ya ce ba zai sanar da kowa ga abin da ya gani ba. A kusa da shi Omaid ya zauna yana faÉ—in. "Kazo mu je duba Aunty Sareena".

Wurga mashi kallo da waÉ—an nan shaggun idanun nasu ya yi kafin ya ce. "Love baka ji wani abin a jikinka ba?".

Kallo shi ma Omaid ya wurga mashi kafin ya ce. "Na ji like an zaneni da bulla daren jiya, kuma na ji kamar kirjina yana bugawa da sauri-sauri kamar ina cikin tsoro, amma beb ta É—auke mun hankali da yasa bai bi ta kan hakan ba, da wani abin ne?".
Chapter 61 · 0% Book details