← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 130

Sashe 19

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"For sure Aesh zan zo gareki, zan zo in ɗaukeki, please ki kula mun da kanki kin ji?". Ya faɗa yana aikin kai komo a cikin parlon, kamar ba lafiya ba. Ɗan tsagaita kukan nata ta yi kafin ta ce. "Zan kasance mai dakon ganinka, please Yah Ramish kada ka jinkirta wajen zuwa, domin akwai zuciyar da bata san komai ba face sonka a kan gaɓar mutuwa wanda kai kaɗai ne zaka iya cetarta".

Ba ƙaramin daɗin kalamanta ya ji ba, dan haka sai ya ce. "Tabbas zan zo in ceci wannan zuciya ba tare da ɓata lokaci ba, ki faɗawa mama Haulat cikin satin nan zanzo".

Ƙasa sosai ta yi da murya, kamar mai raɗa ta ce. "Idan ka zo zaka ɗaukeni in kasance tare da kai?"......... "Kina son hakan ne?". Ya faɗa yana zama saman sofa. Kai ta gyaɗa tamkar tana a gabansa, tana daga kwance saman bed ɗinta, wayar Zash ta ɗauka ta ɓoye number, dan bata son ya san da number da ta kirasa, sannan bata son Zash ya san ta kira, shi ne ta ɓoye number a zuwan idan sun gama waya zata goge kiran in ya zo kada ya gani, ta gagara jure rashinsa ne, hakurinta ya kare yau.

"E ina son kasancewa da kai, ka zo kawai ka É—aukeni". Cikin zolaya ya ce. "Amma kuma ba da kuka kike mun har da cewa ke mama zaki bi ba zaki zauna da ni ba?".

Tamkar tana a gabansa tasa hannu ta rufe fuska tana dariya ƙasa-kasa. "Kai Yah Ramish kai ma ai kasan miji daɗi ne da shi, kuma musamman ma mijin da ake so kuma yake sonka, ya fi komai daɗi a duniyar nan".

Lokaci guda kalamanta suka saukar da Musulmin daɗi a zuciyarsa, amma sai ya ce. "Meyasa kika ce hakan?". Cigaba da ɓoye fuska ta yi kafin ta amsa da. "Saboda kai zaka bani abin da su mama ba zasu iya bani ba and soyayyar miji da mata dake kaunar junansu wani abu ne da babu irinsa a duniya, ai ha a banza ALLAH ya ce miji ya fi uba ba, muddin mace ta yi aure to mijinta ya fi mahaifinta, kuma mama ba za........".

Ƙasa karisar da maganar ta yi saboda nauyi da ya yi mata, shi kuwa tin da ta fara maganar daɗi ya lulluɓesa, ya rasa abin faɗe, yau Leesharh na neman dawowa wajensa, lallai ba shakka UBANGIJI baya taɓa yin ba dai'dai ba, ba banza ya fifita miji kan uba bayan aure ba.

ANYA JIKOKIN AKKA NAN BABU WATA AYAR TAMBAYA KUWA, DIK MACEN DA SUKA KASANCE DA ITA BATA IYA RABUWA DA SU, KU DUBI MAHNOOR DA JAISH, ITA DA TA CE YA YI YAJI ZATA KOMA WAJEN BAPPA, JAISH NA SANYATA A ÆŠAKI KUN SAKE JIN BATUN YAJIN NAN KUWA? GA CHUCHU HAR KIRAN WAYA TAKE YI A ZO A BATA AL'AMURRA. KAI KUZO MU JE AKKA TA FAÆŠA MANA ME SIRRIN, KUN JI LEESHARH NA NEMAN DAWOWA GIDAN MIJINTA DA KANTA, AMMA FA BAN GA LAIFINTA BA, HAKA KAWAI TANA CAN WATA TA YI MATA WUFF DA SHI, DAMA GA SHI GUYSON YA CE MATA MASU SON YAH RAMISH SUNA DAYAWA!.

Cike da kaunarta ya ce. "Dole in zo in ɗaukeki Aesh ɗina, saboda na ga alamar za'a iya samun matsala idan ban zo ba". Harshen damo ya yi mata a magana, wato daga ƙarƙashin harshenta ya gano tana sha'awarsa ne, amma bata san hakan ba, gara ya je ya ɗaukota kada a samu matsala, to sai dai matsalar ta yaya zai iya shiga kingdom ɗinsu lafiya ya fito lafiya? Uhm akwai cakwakiya dai kam.

---------------------🔥

Zaune Mahnoor take a saman sofa a parlonsu, Jaish ya tafi office yau, tana rike da É—ayar wayarsa tana buga game, Mahreen ta tada kai da cinyarta suna hira na tsakanin Æ´an uwa, cikin zolaya Mahnoor ta ce. "Gajin bappa kema fa yakamata ki yi aure, kinga Yah Jaish ya ce zamu je Jimeta kwanannan, to ki samu mijin da zaki je Jimeta da shi a É—aura aure in ba haka ba a baiwa Hamma Faisal ke a cika alkawarin".

Tab kamar Mahnoor ta sani, dan kuwa bappa ya tabka alkawari wa Faisal cewa ya bashi Mahreen, yanzu jira ake yi kawai su je, sai aurenta da shi, shi ma Faisal ɗin yanzu ya saduda ya karɓi Mahreen ɗin, dan yasan ya rasa Mahnoor kenan.

"Tab ni me zan yi da wani Hamma Faisal, kinga Adda Mahnoor ki dai'na bana so, wai baki ji Aunty Chuchu ta ce ni matar manya bane? Shi kuma Hamma Faisal ai yaro ne".

Uhm Faisal fa ya girmi guyson amma take ce mashi yaro to shi kuma guyson jariri ne kenan a gabanta, Chuchu dai ta kara lalata Mahreen da ta ce lallai matar manya ce ita, ita kuma bakauyar ana nufin manya masu daloli a hannun ta tsaya tana duba shekaru, ko uban me zata ci da shekarunsu?.

Mahnoor zata sake yin magana Mahreen ta rigata da cewa. "Adda Mahnoor kin san me wancan uncle Taheer É—in ya ce mun jiya?". Kai ta girgiza mata kafin ta ce. "A'a ban sani ba sai kin faÉ—a". Ta yi maganar tare da kashe wutar screen É—in wayar ta ajiye a gefe, sannan ta dawo da hankalinta a kan Mahreen É—in, yaran nan dik sun saje da larabawa, sun kara kyau abinsu, Mahnoor sai kara kiba take yi wuya na cikowa, Jaish na bata abin da ya dace ga kulawa ziryan da take samu, madarar soyayya babu mix, ita ma Mahreen ta É—an murmure kaÉ—an.

"Wai jiya ne da zan je part É—in su Aunty Chuchu na haÉ—u da shi a hanya, shi ne ya ce in zo, da na tsaya na ce mashi ni ba zan zo in da yake ba dan bappana ya hanani zuwa wajen maza, shi ne ya ce ai aureni ma zai yi gabaÉ—aya dan bayan Auta babu macen da ta kwanta a ransa sai ni".

Da sauri Mahnoor ta zaro idanu, cike da zolaya ta ce. "Bappa ya hanaki zuwa kusa da maza amma kike zuwa kusa da Yah Omar ko?".
Mahreen duniya kuke ji, kai tsaye ta ce. "Yah Omar ai yaro ne, bappa kuma manyan maza ya hanani, kuma shi ma Yah Omar É—in ai bana zuwa kusa da shi sai idan kwalliya zai yi mun"

ÆŠan girgiza kai Mahnoor ta yi, Mahreen akwai shegen son girma da rai'na mutane, yanzu Omar É—in ne yaro, kai wannan yarinya sai shirin ALLAH. "To yanzu ke kina son uncle Taheer É—in ne?". Mahnoor ta jefa mata tambayar tana shafa kyakkyawan gashin kanta da ya sha gyara sosai.

"E kinga ai shi babban mutum ne, kamar yadda Aunty Chuchu ta ce ni matar manya ce, kin ga yana da girma". A hanzarce Mahnoor ta ce. "A takaice dai kina son shi ko?".

Zata yi magana sallamar guyson ya karaÉ—e kunnuwansu, fuska a É—auke da fara'a Mahnoor ta kai kallonta kansa, ita ma Mahreen fuska ba yabo ba fallasa ta yi mashi sannu, kada ku manta yanzu ana bashi girma dan ya iya make up.

Hannunsa rike da kwalin sabuwar waya dal ya kariso in da suke, saman sofa ya zauna yana faÉ—in. "Good evening Aunty Mahnoor". Kallansa gabaÉ—aya a kan Mahreen. Ita kuma Mahnoor tana kallonsa, a ranta tana jin guyson son Mahreen yake yi, yaki fitowa ne kawai ya faÉ—awa kowa, dan haka ta kuduri niyyar faÉ—awa Jaish yau, dan in dai yana son Mahreen to ba zata barta ta fara son uncle Taheer ba!.

Amsa gaisuwar tasa ta yi tana cigaba da kallonsa, ko kaÉ—an ya kasa kawar da kallonsa daga kan Mahreen, ga shi ta yi kyau cikin riga da wandonta, kan dai babu É—ankwali,

"Mahreen wajenki fa na zo". Ya faɗa yana ɗan yi ƙasa da kai, wai kunyar Mahnoor yake ji. Da sauri ta miƙe zaune, binsa da kallo ta yi kafin ta ce. "To gani nan". Shiru ya ɗan yi ya gagara yin magana, saboda kunyar Mahnoor.

Ta fahimci hakan dan haka sai ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsu tana faɗin. "Ina zuwa".

Tana tafiya ya yi gaggawar dawowa kujerar kusa da Mahreen ɗin, muryarsa ƙasa-ƙasa sosai ya ce. "Zaki zama kawata please?". Ɗan zaro mashi idanu ta yi. "Kawa da namiji kuma?". Kai ya ɗan gyaɗa mata. "Kin ga ni dake ai yaya da kanwa ne, so zaki iya zama kawata kamar yacce su Auta suke kawayena".

Shiru ta ɗan yi kamar mai wani tinani, can kuma sai ta ce. "Iskanci dai ba kawa ba, ka taɓa ganin mace da namiji sun zama kawaye ne idan ba iskanci ba?".

ÆŠan zaro idanu ya yi, a bakin Jumma ta ji zancen wannan iskanci fa, amma har ta rike.

"Ba iskanci bane ga na gida, ga na waje ne iskanci, ni ba yayanki bane?". Harara ta É—an wurga mashi kafin ta ce. "Bafa ka fini da wasu shekasu masu yawa ba, dan haka kai ba wani yayana babba bane".

Jinjina kai ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Les say ni kaninki ne ma, ba zaki iya yin abota da kaninki ba?,". Jin ya ce mata kaninta ne shi yasa ta saki murmushi har sai da kyawawan fararen hakwaranta suka bayyana. "To idan zaka rinƙa ce mun Aunty Mahreen zan yarda mu yi abotar tun da ni auntynka ce kai kuma kanina".

Da sauri ya ce. "Na yarda Aunty Mahreen, zan rinƙa faɗa, yanzu ki yi alkawarin mun zama abokai?!". Ya kai karshen maganar tare da ware mata tafukan hannunsa ɗaya. Da sauri ta ɗaura nata tafin hannun saman nasa tana faɗin. "E mun zama abokai kanina".

Murmushi ya yi har sai da dimples É—insa suka lotsa. "To Aunty Mahreen É—ita rufe ido in baki wani abin". Haba ai wani Musulmin murmushi ta saki jin ya kirata Aunty, wayyo daÉ—i kasheta. Da sauri ta datse idanunta. Kwalin wayar hannunsa ya buÉ—e ya ciro wayar, hannunta ya kama ya damka mata wayar yana faÉ—in buÉ—e to.

Da sauri ta waro idanunta, ai tana ganin wayar bata san time da ta daka tsalle game da cewa. "Yanzu wannan waya ta ce?". Jinjina kai ya yi. "Kwaraikuwa Aunty Mahreen".
Chapter 19 · 0% Book details