← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 130

Sashe 36

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Toilet shi kuma Smart ya nufa, amma kafin nan sai da ya kara duba Black Tiger, bawan ALLAH har yau bai motsa ba. Wanka ya yi a gurguje tare da zuwa ya shirya cikin É—aya daga cikin mafiya tsada da haÉ—uwan suit a cikin kayan Big Bro, sannan ya yi amfani da wayar Big Bro É—in ya kira daddynsa na Paris ya sanar da shi cewa ga kawayensa fa sun kawowa Black Tiger ziyara, kun san France, England da America kawaye ne, kada ku manta daddynsa na Paris kuma shi ne his excellency mai ci a yanzu.

Ba tare da nuna wata damuwa ba daddyn nasa ya ce. "Nasan sun je wajen, amma su sun ɓoye mun basa son in sani, but ka bar wayarka a kunne bari in saurari abin da ya kaisu". Jinjina kai Smart ya yi tare da ciro wayar daga kunnensa. Kasa ya sauko, already daddynsa na Paris ya san waye Big Bro, Smart ya faɗa mashi komai.

Wlh idan ka kalli Smart ba zaka taɓa cewa ba Big Bro bane, ya fito sak shi. Time da ya sauko ƙasa Sweetie na zaune a saman sofa ta yi shiru tana tinanin Big Bro, ta yi rama sosai, dik wannan ƙayataccen murmushin nata ya kau, ta zama wata iriya da ita, kullum tana a cikin bad mood.

A zabure ta miƙe tsaye dan a tinaninta Big Bro ne, sai da ta kura mashi idanu har ya kara matsawa kusa da ita, sannan ne ta gane Smart ne, komawa ta yi jiki a sanyayye sosai ta zauna, tamkar zata yi kuka ta ce. "Babban yaya sannu da fitowa".

Sosai ta baiwa Smart tausayi, shi fa har yau ƙalilan matar Big Bro yake yi mata, shiyasa ma yake tausaya mata sosai. "Kin sha maganinki ne?". Smart ya faɗa yana nufota, ita ma magani take karɓa saboda azabar da ta ci ranar da kuma rashin lafiyar Big Bro da ya haɗe mata, satin nan dikka bata je school ba.

Kai ta jinjina mashi. "E na sha". "To ya kike jin karfin jikin naki?". Ƙasa ta yi da kai kafin ya amsa da. "Alhamdulillah". "Masha ALLAH, UBANGIJI ya baku lafiya yasa kaffarace".

Da amin ta amsa tana jin zuciyarta na kara yi mata zafi. "Zai tashi In Sha ALLAH, ki cigaba da tayasa da addu'a". Ya faɗa yana wucewa zai nufi kofar fita. "In Sha ALLAH ba zamu taɓa gajiya da addu'a ba". Kai kawai ya jinjina mata tare da ficewa.

Kai tsaye ya buƙaci Ronnie da ya kwatantana mashi room na tattaunawa da manyan baki na Big Bro. Har wajen Ronnie ya rakasa, sai dai dab da zai shiga wajen Ronnie ya ce mashi ai Big Bro kullum da mask a face ɗinsa yake tattaunawa da baki. Wani irin Musulmin daɗi Smart ya ji, dan dama yanayi tinanin yadda za'ayi abokan daddyn nasa ba zasu ganesa ba, dik da dama ba wani saninsa suka yi, amma in baku manta ba a baya nemansa suke yi dan aikinsa, amma yaki ko in ce daddynsa yaki basu shi.

Juyawa ya yi suka koma Ronnie ya fito mashi da mask na Black Tiger, ya sha mamakin ganin irin mask masu É—auke da zanen bakar damisa, lallai yanzu Smart ya kara jinjinawa karfin ikon Big Bro, ashe ya kai haka? NI KO NA CE SAI MA KA JI ME YA KAWO MUTANEN TUKUN NAN, AI BIG BRO YA WUCI NAN! SARKI NE MAI KARFIN IKO!.

Da shigowar Smart cikin room ɗin sai ya iskosu a tsaitsaye basu zauna ba. Ba karamun mamaki Smart ya sha ba na ganin irin haɗuwar wannan ɗaki na tattaunawar, gabaɗaya tsala-tsalan kujerun dake cikin room ɗin da ɗanyar gold aka yi su, sai wai kyalli suke yi, ga sofarsu mai bala'in laushi, ɗaki ne wanda yake da views guda biyu ta ɓangaren hagu da dama, sai kuma curtains masu bakain kyau, a tsakiyar ɗakin wani katan gold table wanda tsala-tsalan chiar guda 24 suka kewaye shi, daga can jefe luntsama-luntsan sofas ne masu bala'in haɗuwa da ɗaukar ido, ga wani fitinannen kamshi dake tashi sosai. Gaskiya Big Bro na daban ne, komansa cikin tsari da ɗaukar hankali, ga tsantsar madarar natsuwa.

Jiga-jigan bodyguards har huÉ—u ne suka rako bakin cikin room É—in, baki uku ne dikkansu fararen fata tas, dikkansu kuma Smart ya sansu, ya gane fuskokinsu. Ko da bai san a ina Black Tiger yake zama idan ya yi baki ba, kujerar Big Bro da kanta ta bashi amsa, domin kuwa tsarinta daban yake, kwalliyar saman kayin kujerar ma ta suffar damisa ce.

Dan haka wajen Smart ya wuce ya zauna yana binsu da kallo, dama yasan jira suke yi ya zauna kafin suma su zauna, dik da bodyguards É—insu sun caje masu kujerun dama É—akin bakiÉ—aya babu wani abin cutarwa, amma basu yarda su zauna ba har sai mai wajen ya zauna.

Yana zama suka zauna, cikin mutumta juna suka gaisa kafin wakilin Sarkin England ya korawa Smart bayanin abin dake tafe da su, wato sun zo ne kan kasuwanci da suke san kullawa da birnin, har da cewa zasu zuba makudan kuɗaɗensu, suna son haɗa alaƙa mai karfi a tsakaninsu da birnin, daga ƙarshe suka yi alkawarin karawa kasar kafin soji da tsaro na ban mamaki idan Big Bro ya yarda da su!..

Smart ya yi matuƙar mamakin jin wannan abin, a ransa ya ce lallai dole wannan birni tana da wani abin da ba kowa yake da shi ba. Sai dai gudun kada ya ɓata ran ɗan uwansa yasa ya c masu zai yi tinani a kan buƙatarsu, idan ya yanke hukunci zai sanar masu, ya yi masu hakan ne kuma saboda baya son yi wa Black Tiger kutse a cikin al'amurransa, bai sani ba ko ɗan uwan nasa yana da ra'ayin karɓar turawan yamma a birninsa ko akasin haka, kun ga kada ya je ya yanke mashi hukuncin da zai ja Black Tiger ya yi ta jin haushinsa a banza, dama ya ya lafiyar giwa? Dama basu samu ya aminta ya karɓesu bama.

A kan wannan matsaya suka rabu, Smart ya dawo sama, nan fa ya fara binciken me birnin nan ta mallaka da turawa suke son yi mata kutse har haka?. Ba ƙaramin razana Smart ya yi ba a lokacin da ya ga irin ɗinbin dukiyar da ɗan uwansa ya mallaka, yanzu ya yane cewa dole ne turawa su yi tururuwan kutsowa cikin al'amurransa, lallai ya mallaki abin da dole ne ma ayi mashi ca a kansa, wow bayan zallar gold da birnin ta mallaka, ga crude oil, bugu da kari ga kuma red gold, suna da aluminum kala-kala, ai lallai in kuwa haka ne dole Big Bro ya yi gagarumin shiri, ashe gara da bai basu amsa ba ya yi shiru, tab akwai case..

-------------------------🔥

CROWN OF JUSTICE.🔥

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
No editing 🤗😇

CROWN OF JUSTICE.🔥

Kafin ta kai ƙasa ya yi amfani da magic ɗinsa wajen dawo da ita, Auta bata san ya aka yi ba sai ganin kanta ta yi a saman bed, ihu ta shiga kurmawa da karfin gaske wanda bata san cewa babu in da ihun nata yake zuwa ba, dan ita kaɗai take jin ihun, dik yadda ta kai ga waje baki babu mai jiyota. Ƙoƙarin tashi daga saman bed ɗin ta yi sai dai ina, tamkar an ɗaɗɗaure mata jiki, ko motsawa ta gagara yi.

Ganin haka yasa ta tina babu mai kuɓutar da ita UBANGIJIN da ya halicceta ya halicce shi, ya halicci aljani da shaiɗanu, dan haka sai bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen fara kwaranyowa kanta addu'ar neman tsari daga shaiɗanin aljani dama shaiɗanin ɗan adam.

Shi kuwa ya tsaya sai ƙoƙari zare kayan jikinsa yake yi, gabaɗaya fuskarta ya yi wani irin jajir da shi saboda kukan da ta rinƙa sha, hancinta kamar an goga mata manja, fararen idanun nan nata dik sun kara jajir da su.

Gabaɗaya ya koɓe kayansa ya yi tsindir a gabanta yadda take a kwance, datse idanunta ta yi tana cigaba da ambato sunan ALLAH subhanahu wata'ala da ya kawo mata agaji.

Gadan-gadan Ude ya haye saman bed ɗin nan domin farmata, sai dai kuma yana ƙoƙarin kai hannunsa jikinta ya ji ana murɗa handle ɗin door. Kasancewar yasan ya datse kofar da magic ɗinsa sai abin ya yi mugun bashi mamaki kan wanene wannan da zai iya shigowa? Koma wanenen lallai na daban ne.

Bai ankara ba sai gani ya yi anturo kofar za'a shigo, ai a wani irin miliyan ya ɓace daga ganin mutane ɓad, amma bai fita daga ɗakin ba, ya kuma saki Auta da ya girke a saman bed ɗin. Bakinsa a ɗauke da Musulmin sallama ya shigo cikin ɗakin, da alamar gajiya a tattare da shi, har wani lumshe idanu yake yi tamkar yana jin barci. Sai dai kuma yana sako kafafunsa cikin ɗakin ya yi wani irin wastsakewa saboda kukanta da ya dira a cikin dodan kunnuwansu. A miliyan ya zaro idanu waje.

Ganin da gaske ita ke zaune tsakiyar bed tana rera kuka ne hasa shi yin zafan ƙarisowa wajen, saman bed ɗin ya haye tare da riko shoulder ɗinta, a ruɗe ya fara faɗin. "Hoonairata lafiya? Meyasame kike kuma? Waye ya taɓaki? Ina Aunty Rishma?". Yana magana yana goge mata hawaye da ɗayan hannunsa.

Ja baya ta yi daga rikon da ya yi mata, saboda dik da ta ji bugawar zuciyarta, bata yarda shi bane, ALLAH sarki an rigada an tsorata ta ne. Baya ta ja sosai tana bin fuskarsa da kallo, haba ai tana gane cewa shi ne na gaske ta yi wani irin zafan faɗowa jikinsa tare da saka mashi kuka mai sautin gaske, kara ruɗewa sosai ya yi, ya rungumeta sosai yana ƙoƙarin tambayarta me ya faru?.
Chapter 36 · 0% Book details