← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 130

Sashe 53

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai Big Bro ya yi kafin ya ce. "Bani da wasu iyaye biyunsu ai".
Kamar Smart zai ce to kenan ya yarda daddynsa na nan ba shi ya haifesa ba, sai kuma ya fasa yin tambayar gudun kada ya ɓallo wata ruwan, tin da ALLAH ya ɗorasu kansa, addu'a bata faɗuwa kasa banza, ya aminta su Mommah ne iyayensa, to bai kamata a ɗauko tsohon zance ba, kada a lalata shirin kuma.

Matsawa ya yi ya rungumo Big Bro a jikinsa, har hawaye idanunsa ta kawo saboda farincikin Big Bro ya aminta da cewa shi ɗan uwansa ne, shikenan komai ya zo karshe a wannan rikicin kuma, amma fa an sha fama, sai dai daga karshe ya yi nasara, addu'ar mommah da nasa ta karɓu.

Hannu Big Bro yasa ya ɗan shafi arab hair ɗinsa kafin ya ce. "I really love you my blood". Wani irin musulmin daɗi ne ya kara lulluɓe Smart. "Love you too my blood".
Yanzu ta tabbata dama duniyar shaiÉ—anu ne basa son Big Bro ya yarda da su Mommah. Shikenan yanzu ya aminta.

Cike da farinciki Smart ya ce. "Kenan yanzu zamu iya komawa gida?". Kai Big Bro ya girgiza mashi alamar a'a kafin ya ce. "Ba yanzu ba, zuwa next week zamu je gida, amma zuwa zan yi in ga iyayena kawai".

Ba dan Smart ya so ba ya amsa mashi da okey, sai dan baya son su ja magana wata matsala ta sake faruwa, dan yana ganin kamar Big Bro bai gama samun lafiya ba, da yana da tabbacin ya samu lafiya ba zai yarda da cewa zai je ya ga su mommah ne kawai ya dawo ba, amma ba komai su je gidan, ya tabbata ba zai iya dawowa ya barsu ba, zai zauna da su ko da na É—an lokaci ne!.

Sun jima rungume da juna ta gefe guda while Sweetie tana kwance a kirjinsa ta gefe guda, kafin daga bisani Smart ya raba jikinsa da na Big Bro yana faÉ—in. "Bari a shirya maka lunch É—inka dan nasan kana jin yunwa". Ya yi maganar yana shafa lallausan fuskar Big Bro.

Hannu Big Bro yasa ya shafi nasa kumatun shi ma kafin ya ce. "Lokacin cin abinci ya kure, bari kawai mu yi dinner anjuma".
Ba haka Smart ya so ba, ya so ɗan uwan nasa ya ci abinci, amma tin da ya ce a bari bari su bari ɗin kawai, dan haka sai ya miƙe ya zauna a gefen bed ɗin suka cigaba da hira jefi-jefi cike da kaunar juna. Ya dai ki barin Sweetie ta rabu da jikinsa, ya ƙanƙameta gam, shi Smart dik tinaninsa suna da aure ne shiyasa sam baya yi masu shamaki a tsakaninsu.

A haka Ronnie da Pretty suka shigo suka samesu, suma saman bed É—in suka haye, Pretty ta matso jikin Smart ta kwanta, yanzu son kayanta take yi tin da Sweetie ta faÉ—a mata cewa Kamran yayansu ne, sai ta rungumi mijinta tana kula da shi.

YANZU SUN CURE SUN ZAMA ONE FAMILY!.

Shiru Ronnie ya zauna yana binsu da kallo, ya kalli Big Bro yana shafa kyakkyawan gashin Sweetie, ya juyo kuma ya kalli Smart da yake ta faman biyewa Pretty tana kashe shi da shagwaɓa. Lokaci guda tinanin budurwa ta faɗo mashi a rai, amma har yau bai iya sake tuna Floris ba, da alama yayansa ya yi mashi wani abin a kanta ne. Sai ya ji sha'awar budurwa, ya ji yana son samun budurwa shi ma, da wannan tinani a ransa ya yunkura zai sauka daga bed ɗin kenan Big Bro ya riko hannunsa, ya jawosa jikinsa ya haɗesu da Sweetie ya rungume a kirjinsa, yana jin wani iri a ransa, wani irin tsananin so na musamman yake yi wa waɗan nan halittu biyun, dan sun nuna mashi kauna over, basu taɓa nuna sun gaji da halinsa ba, almost 2 years da wani abin yana a tare da Sweetie, dik azabar da ya ganawa yarinyar nan bata taɓa nuna ta gaji da halinsa ko ta nuna ta tsanesa ba, tana da hakuri da juriya, shi kuma Ronnie kome zai faru yana nuna mashi zallar kauna kuma yana goyan bayansa, dede da second ɗaya bai taɓa juya mashi baya ba, waɗan nan mutane biyun sun cancanci fiye da haka daga garesa.

MY PEOPLE'S YA KUKE GANIN WAƊAN NAN FAMILY ZASU KASANCE? DA SAURAN KALLO FA, YANZU WASAN ZAI FARA ASUWAY, GA LOVE GA WAR! YANZU ZA'AYI ASALIN YAKI! MUN SHIGA RAWANIN ZALINCI ZABUWAR DUNIYA STEP ONE, AKWAI STRUGGLE FA!!.🤸

CROWN OF POWER🔥

"Kasan me?". Kai ya girgiza mata alamar a'a bai sani ba. "Daga yau kullum zamu rinƙa zuwa gym ɗin nan kana koya mun, sannan mu je ka nuna mun masu raina maka wayan in haɗa masu jini da majina". With her full confidence ta yi maganar.

Shi dai wani lokaci mamaki Mahreen take bashi, sometimes yana rasa ta ina take zaro magana, wai ta haÉ—a masu jini da majina, kai ALLAH abin godiya, gata kuma kamar a hure wlh, ba auki sai baki.

"Kada ki damu, sai zuwa gobe ko da daddare zan kaiki in da suke rainani in nuna maki".

Jinjina kai ta yi tana wani ciza laɓɓa kamar wata yar daba, ita a dole zata tare mashi faɗa. Hmmm bata san guyson bane, wlh yaron nan da balain zuciya, ga karfi da zafin rai, ciwon cikinsa da yake yi wa kuka abu ne da ya shafi iska da dole ya yi kuka, azabansa ta wuce yadda ake tunani, wlh ba dik kai ba zai iya shanye ciwon guyson, abin ba na wasa bane, ku baku yi mamaki ba, almost 20 years yanzu sauki taki samuwa, wai baku ga baya tsoron aljanu bane? To shi da kansa aljanin kansa ne, shiyasa ranar ya zage aljanar can, ai tare da su yake kwana, kune baku san labarin ciwonsa ba, amma a hankali zaku fahimci makasudin ciwon, da dalilin kukansa idan yana ciwon da kuma meyasa zuciyarsa ta ɗan zama mai rauni a yanzu, wlh da yana asalin Omar ɗinsa na tin farko in aka zo faɗa ko Jaish ba zai sha a hannunsa ta daɗi ba, baku yi mamakin meyasa Jaish yake dariya da aka ce Omar yana son Mahreen ba, ai gagarumin maganace a kasa, shi Jaish yasan Mahreen zata iya tunzura guyson har ta tayar da abin da aka sha wahalar kwantarwa, uhm abin babba ne, muje dai zuwa.

Bai sake ce mata komai ba har suka kammala gym É—in, ya riko hannunta suka dawo ciki, ya koma bedroom É—insa ita ma ta wuce nata, basu sake haÉ—uwa ba sai karfe 9 na dare, ya zo nemanta sau ba adadi baya samunta, tana can ta ci uwar kwalliya tana lambu, ta zauna sai hotuna uncle Taheer yake yi mata, saboda ya ce ta yi kyau, yaba kyanta yasa ta É—an saki jiki da shi, bata ita ta dawo cikin gida ba sai can mangariba, a can ta yi sallar azahar da la'asar.

Ko da ta dawo cikin gida bedroom n Mahnoor ta wuce abinta, bata koma nasu ba, hakan yasa guyson ya yi ta jelen nemanta har ya hakura. Karfe tara É—in ma yana zaune a bedroom É—in nasa cike da tinanin ina take? Ya kira wayar da ya saya mata baya shiga. Yana zaune a tsaiyar bed ta shigo bakinta a É—auke da sallama.

Da sauri ya miƙe, muryarsa a raunace ya ce. "Ina kika je yau?". Tana yamutse fuska ta ce. "Zuwa da safe zan faɗa maka yanzu dai zo ka bani jallabiyarka fari guda ɗaya". Ya ɗan yi mamaki amma sai ya ce. "Okey amma zaki zauna mu ɗan yi hira ko?".

Ka ta ɗan girgiza. "Akwai abin da zan yi, amma kila zan dawo bani da wuri". Kamar zai sake yin magana, amma jin ta ce a bata da wuri yasa ya diro kasa ya nufi closet ɗinsa. Sabuwar jallabi fara kal ya ɗauko mata, yana miƙa mata ta karɓa da sauri ta juya, bayanta ya bi da kallo yana ɗan mamakin me zata yi da jallabiya kuma?.

A gaggauce ta yi waje, bata zame ko'ina ba sai room É—inta, tana shiga ta cire kayan jikinta dikka, ta wate jallabiyar tasa ta sanya a jikinta, ya yi mata tsawo sosai, dan guyson yana da tsawo sosai, hannun ma ya mata yawa, amma dik bata damu ba, ta wuce gaban mirror ta zauna.

Ai zama ta yi ta fito da kanta a siffar aljana sak da farin hoda da kwalli, ko daga ina ta samosu oho mata, ta fito gwanin ban tsoro, ta ɗauko wani farin kyalle tas mai laushin gaske ta yi rolling kanta da shi, wlh ko mai jarumtarka ka ganta sai ka razana, ta banbaɗe fuska da farin hoda, ta wani mulka bakin abu a baki ya yi bakin kirin, har gemunta baki, ta ja gera har wajen sajenta, kasan idanunta ta ƙawata shi da bakin kwalli, yadda ta zana kwallin ta yi raun ɗin idanun nata, ta damɓarasa da kyau, sai gula-gulan idanun farare tas zaka iya hangowa a fuskarta, ga uban rolling da ta yi, jallabiya na jan kasa, haka ta kammala shirinta tsab ta ɗauki kwalbar turare ta tura a cikin aljihun jallabiyar tata, sai ta ɗauko wayar cazar waya, shi ma ta nannaɗe ta tura a cikin aljihu, sannan ta nufi waje.

Cikin sanɗa ta fara takawa ta nufi sauka ƙasa, ta bene ta bi. Kasa ta sauka ta nufi part ɗin uncle Abbas, sai ta bi ta kofar baya gudun kada warriors su ganta, ta saci hanya, ALLAH da ikonsa har ta shiga part na uncle Abbas kuma babu wanda ya ganta, da yake ta san ɗakin Sareena ta taɓa zuwa da Chuchu, sai kai tsaye ta nufi wajen.

Kun sa basa rufe kofa, dan haka a buɗe ko'ina yake, tana zuwa ta afka ciki, ta haye sama abinta, kai tsaye sai ɗakin Sareena. A hankali tura kofar ɗakin Sareena, kamar wata ɓarauniya haka ta shigo.
Chapter 53 · 0% Book details