← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 130

Sashe 51

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabaɗaya sun jigata, amma babu wanda yake da niyar risinar da kansa ya baiwa ɗan uwansa hakuri, yadda kuka san babu zuƙata a kirazansu, shi Smart mai hakurin ma yau babu alamar za ɗaga kafa, dan kada ku manta kamar yadda suke identical haka komai nasu yake iri ɗaya sai ɗan banbanci da ba'a rasa ba, wannan banbanci kuma ita ce hakurin Smart, ya fi Big Bro hakuri, da alama Smart hakurin Mommah ya ɗauko, shi kuma Big Bro rashin hakurin King, Dan dai King kam mun san bashi da hakuri kuma baya yafe gaba! Kun tina King Al-Mustapha da ya tako har zuwa Kingdom ɗinsu ya yi mubaya'a ya bada hakuri? Amma me King ya ce? Ba zai hakura ba, baya yafewa abokin gaba kuma baya manta gaba! Ko ba haka aka yi ba? So shi King bashi da hakuri ga saurin fusata, in ya fusata kuma baya saukowa da wuri, kusan Big Bro ɗin dai, sai dai aka ce ɗan nagada ya fi ɗan na koya, shi ne kawai yasa Big Bro ya dame King a iya rashin mutumci.

-----------------------🔥

Wani irin shaka dikkansu biyu suka yi wa junansu, Big Bro ya shake Smart shi ma kuma ya shakesa, babu alamun zasu iya sake juna. Unexpected daga bayansu Ronnie ya kwararawa Big Bro wani ruwa daga cikin bokiti da ya shigo da shi a hannunsa. GabaÉ—aya jikin Ronnie kerma yake yi, idanunsa sun yi jajir, ga hawaye masu É—umi na tausayin yayan nasa da ya gama wanke mashi fuska! ALLAH sarki!.

Ai wani irin kururuwan ihun da Big Bro ya zunduma sai da yasa gabaÉ—ayansu suka yi gaggawar sanya hannu suka toshe kunnuwansu. A take Big Bro ya rikiÉ—e ya koma siffar Uncle Abbas sak, wanda hakan ba karamun girgiza Smart ya yi ba, sai a yanzu ya gane cewa waye Big Bro ya gani yake ikirarin shi ne mahaifinsa? BABBAR MAGANA!!.

Jikin Big Bro take ta fara wani irin girgiza, kan kace me wani irin abu ya fara fita daga kowa sassasa na jikinsa, tamkar hayakin wuta tamkar kuma turɓayar ƙura, haka jikinsa ya rinƙa fitar da wannan hayaki yana wani irin huci, idanunsa sun kaɗa jajir, wani irin jini ya taru a kasan idonsa, kai ka ce wuta aka kwantar mashi a wajen.

GabaÉ—aya babu wanda bai razana ba, harta Sweetie dake tsaye ta bakin kofa rike da hannun Pretty dik sun razana suka wani irin kankame juna, ji suke tamkar su juya da gudu su bar É—akin, amma suka daure.

A kan Sweetie Big Bro ya tsayar da jajayen idanunsa masu firgitarwa, cikin wata iriyar murya mara daɗin ji ya ce. "Tin yana karami a babin kaddararsa na san da akwaiki! Kece his destiny! Nasan labarinki tin ranar da Omranish ya yi cikinki, na yi tinanin zan iya canza kaddararsa in hanaki shigowa cikin rayuwarsa, shiyasa ban kasheki tin kina ciki ba, ashe na yi ganganci, na yi gangancin barinki ki rayu, amma dik da haka ban sare ba, na faɗa mashi ke zaki kawo karshensa domin in kin shigo rayuwarsa ya kasheki da hannunsa, sai dai kuma kash, kin ɗaure shi kin kuma saka hijabi a tsakanina da shi ta yadda ban san me yake faruwa ba, kafin na farga na san abin dake faruwa a tsakaninki da shi kin rigada kin yi nisa a cikin rayuwarsa, kin rabani da ɗana, kina tinanin zan barki kenan? Kin yi babban kuskure da dole ki karɓi hukuncin mutuwa mafi muni!!".

KARIN BAYANI, YA SO HANA SWEETIE SHIGOWA RAYUWAT BIG BRO, AMMA YA GAGARA YIN HAKAN, SABODA ALLAH YA KADDARA ITA ZATA SHIGO RAYUWARSA TA CECESA DAGA HANNUNSU, SANNAN DA YAKE IKIRARIN ITA CE KADDARAR BIG BRO ZATA CUTAR DA SHI, WANNAN CUTARWAR BA KOMAI BANE FACE CETONSA DA ZATA YI, RABA SHI DA SU DA ZATA YI SHI NE SUKE IKIRARIN CUTARWA NE WANDA KUMA MU MUN SAN TAIMAKO TA YI MASHI.

"Ba zan taɓa bari ki cigaba da rayuwa ba, zan dawo gareki, sai mun ɗauki fansa ki shirya!!". Yana kai karshen maganar ya yanke jiki ya faɗi kasa, yana faɗuwa ya koma ainahin siffarsa na gaske, take wasu irin bakaken kamar hucin wuta ya rinƙa fita daga jikinsa, a daidai wannan lokaci dik wani abin da ya danganci duniyar shaiɗanu ya fita daga jikinsa, kuma ya shafe daga ƙwaƙwalwarsa, dan ya yi mai kankat, ya rabu dasu gabaɗaya, harta fuskar baban nasa ya shafe daga kwakwalwarsa, sai dai magic ɗinsa tana nan, dan ita ba a duniyar shaiɗanu ya koyeta ba, a Black World ya koya, amma dik wani abin da ya danganci shaggun can ya fita daga jikinsa, yanzu ya zama sabon mutum cikakke mai cikar kamala, fuskar Uncle Abbas ya goge daga kwakwalwarsa, sai dai ALLAH da hikima da basirarsa sai da ya nuna wa su Smart uncle Abbas nada sa hannu kafin hakan ta goge daga kwakwalwarsa, yanzu Smart ya ga fuskar uncle Abbas, sannan ya ji Big Bro ya ce shi ne daddynsa, kunga dole zai tuhumesa ko? Akwai dai case.

Da gudu suka yi kansa, ALLAH sarki har shi Smart É—in da gudu ya yi kansa suna ambatar sunansa, sai dai ina shiru bai motsa ba.
A KARSHEN PAGE ƊIN NAN IDAN BAN MANTA BA ZAN FAƊA MAKU ABIN DA SUKA ZUBA MASHI A BOKITI YA RABU DA SHAIƊANUN NAN, RANAR MA AKWAI ADDU'AR DA NIKE SON RUBUTA MAKU A WANI PAGE NA MANCE, TO ZAN RUBUTA MAKU A KARSHE DA YADDA SUKA HAƊA ABIN DA SUKA ZUBA MASA ƊIN, DAN DIK GIRMA DA SHAIƊANCIN SHAIƊANI KO WANI SIHIRI KO ALJANI DA AKA YI MAKA SAI IN BAKA YI WANNAN HAƊI BA, TAKE ZAKA GA AIKI DA CIKAWA, DAN KO MAI BAKIN SHAIƊANCIN ALJANI SAI YA SHAFA MAKA LAFIYA, A MILIYAN ZAI YI WAJE, WAƊAN DA SUKE ZARGIN AN YI MASU SIHIRI TO KUMA GA DAMA TA SAMU DAN WARWAREWAR MATSALARKU DA KANKU, MATA MASU ZARGIN ALJANU A JIKIN ƳAƳANSU DIK A KARSHEN PAGE ƊIN NAN ZAKU SAMU MAGANIN BI IZININLAH.

"Yah Omerish kasa a gyara É—akin nan, dan in Big Bro ya tashi zai taso ne a sabon mutum, kuma ba zai san su waye iyayensa ba sai wanda mu muka gabatar mashi, kada ka bari ya taso ya ga É—akin nan watsa-watsa haka, shakku da tinani zata fara shiga zuciyarsa wanda kuma hakan ba zai yi mana daÉ—i ba!". Cewar Sweetie yarinya mai hankalin manya!.

Jinjina kai Smart ya yi, sannan ya miƙe tsaye, ya sanya hannunsa ya zare kwalbar dake wuyansa ya yi jifa da ita, ALLAH yasa bata shigesa har can ciki sosai ba, waje ya nufa yana dafe in da ya ji ciwon. Su kuma suka cigaba da tofawa Big Bro ayoyin Alkur'ani da addu'oi sunai mashi fatan tashi cikin koshin lafiya!.

After some minutes, Smart ya dawo tare da wasu manya-manyan robot masu ji da karfi, umarni ya basu a kan su gyare ɗakin nan cikin ƙanƙanin lokaci, cikin girmamawa suka karɓi umarni, ba tare da ɓata lokaci ba suka hau aiki.

Shi kuma Smart ya daddage ya É—auki Big Bro ya nufi balcony da shi. A saman sofa ya kwantar da shi, sannan ya ce Ronnie ya zo ya yi mashi treatment na wuyansa da kuma gefen cikin Big Bro. Da sauri Ronnie ya kwaso kayan aiki ya zo ya hau gyara masu. Pretty and Sweetie kuma suka koma saman sofa suka zauna suna cigaba da addu'a, har lokacin Ronnie bai daina ruwan hawaye ba.

Sai misalin ƙarfe 4 na yamma robot suka kammala aikinsu tsab, sun shigo da sabbin kaya, sun gyara ko'ina tsab, ba zaka taɓa zatan cewa an yi faɗa a cikin ɗakin nan ba, shi kuma Ronnie ya gyarawa ƴan uwan guda biyu raunikan da suka ji, sai kuka Pretty take yi tana cewa Smart sannu, ya bata tausayi ne, and Pretty tana da wani abu ɗaya, tana bala'in tsoron jini, har juwa ne yake ɗebanta idan ta ga jini, shiyasa take kuka da ta gani a jikin Smart.

Sai rarrashinta yake yi, a ransa ya ce ALLAH yana sonsa da rahama shiyasa jiya ya dasa mashi tausayinta a ransa over, yasa ya kyaleta bai yi abin da ya yi niyya ba, da abin ya kwaɓe masu over yau, da anyi ɓatacciya over.

Bayan sun kammala gyaran É—akin ya yi tsab, sun zuba tirarruka masu daÉ—in kamshi ne suka sanarwa da Smart sun kammala aikin nasu, a lokacin ya yi wanka ya yi sallar la'asar, su Sweetie ma dik sun yi sallar la'asar É—in.

Karfi ya sanya ya cicciɓi Big Bro sama ya wuce da shi cikin room, a saman bed ya kwantar da shi yana bin ɗakin da kallo, ya jinjinawa kokari irin na robot ɗin nan, da sauri su Sweetie suka biyosu ciki, tana sanye da doguwar riga wanda ya kara fito mata da coca cola shape ɗinta sosai, ta yi bala'in kyau, sai dai kana ganinta zaka san hankalinta a tsananin tashe yake, ta shiga damuwa over.

A gefen bed É—in ta zauna, daidai saitin Lion chest É—insa tana cigaba da karanto addu'oi tana tofa mashi. Smart kuma yana sanye da pjs na Big Bro, ya yi kyau over, ya riko hannun Pretty dake ta faman damunsa zata ci abinci, ya rikota suka nufi waje.

Shi ma Ronnie saman bed É—in ya haye suka cigaba da yi wa Big Bro tofin addu'a har around 5:30, sannan ne suka É—an dakata da yin addu'ar suka zubawa yayan nasu ido suna ta kallonsa.

-----------------------🔥

A hankali ya fara motsa idanunsa da suka yi mashi tsananin nauyin gaske, cikin wata iriyar natsuwa ya waro idanun nasa waje, kai tsaye sai a kan fuskar heartbeat É—insa in ji Smart, ta tsaresa da ido tana kallonsa.

Kura mata idanu ya yi tamkar wanda ya ga bakuwar halitta daga wata duniya. A natse ta É—an motsa bakinta wajen cewa. "Big Bro barka da tashi, akwai wani wajen da yake yi maka ciwo ne?".

Shiru bai amsa mata ba, tamkar babu shi ma a wajen, kallonta kawai yake yi. Da sauri Ronnie ya matsa dab da shi, cike da kaunarsa sosai ya ce. "Big Bro in kawo maka tea ne?".
Chapter 51 · 0% Book details