← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 130

Sashe 11

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina mata kai Sweetie ta yi, ai bata san lokacin da ta zunduma wani irin ihu ta daka tsalle ta haye jikin Sweetie ba, da yake Pretty ta fita kiba da nauyi sai suka yi baya gabaɗaya suka zube a ƙasa, ina Sweetie ba zata iya ɗaukar Pretty ba. Binsu da kallo cikin tsantsar farinciki Black Tiger ya yi, farincikin dake a kan fuskar Sweetie it make his day wlh, dik da baya murmushi kuma fuskarsa bata nuna alamar ya ji daɗi ba, amma daga ta ciki ya ji daɗin ganinsu suna farinciki, sai ya ji ya samu gamsuwa da karin natsuwa, har lokacin da Pretty ta haye Sweetie suka tafi zasu faɗi ƙasa tamkar shi ne zai faɗi har ya ɗan zabura kamar zai taresu, sai dai kuma sun rigada sun kai ƙasa, hakan yasa ya mayar da hannunsa da ya buɗe zai taresu izuwa saman kansa, ya ɗan shafa kyakkyawan arabs hairnsa yana binsu da kallo!.

(I wish Big Bro ya yi murmushi a wannan lokaci, amma yaki ya yi, fuska tamkar bai taɓa sanin me sakin fuska bama bare murmushi, wai a haka kuma ya ji daɗi, abin da ba zaka gane hakan ba saboda yacce face ɗin take a ɗaure tamau.)

Dariya dikkansu suka kwashe da shi Pretty ta sake haye jikin Sweetie tana ambatar sunanta.

Cikin tsantara farinciki Sweetie ta ce. "Haba mana my lutiya, kece fa babba, kuma kin fini kiba, ki bari mana ni in haye jikinki, amma sai ki hayeni zaki karyani, ko kin manta kece babba a kai'na ne?"..

Kuma kun manta cewa Pretty ce babba ko? To dik wannan iskancin nata ita ce nan babba, in baku manta ba mai black hair aka fara haifa, mai bakin kuka kuma acici ba, wato Pretty, Sweetie ita ce wacce taki yin kuka time da aka haifeta, shiru-shiru yanzu gabaɗaya Ronnie ya mai data rasa kunya ɓeran tanka!.

Kara hayeta da kyau Pretty ta yi tana faÉ—in. "Ai sai ki bari in ji É—umin jikin naki kafin nan, ko kin manta kema mom ta ce ki kula dani ne?".

Rungumeta Sweetie ta yi tana faÉ—in. "Ban manta ba, shiyasa ai kullum kike rai'na, kuma na cika magamar mom tin da na kula dake dik da bani da ido a wancan lokaci!".

Ai a zabure Pretty ta raba jikinta da nata tana faɗin. "You means yanzu kina da ido?". Kai Sweetie ta jinjina mata tana miƙewa tsaye.

A karo na biyu Pretty ta miƙe game da daka tsalle ta hayeta tana faɗin. "Wlh ALLAH shi kaɗai ne abin godiya, ni kam yau a ina zan sanya rai'na in ji saukin tsananin farincikin da nike ji ne?".

A wannan karon da Pretty ta hayeta ɗin ma sake yin baya-baya suka yi zasu faɗi ƙasa kamar walkiya haka Black Tiger ya taresu. Sweetie ba karfi sai baki da iyayi game da rashin kunyar da take yi wa Big Bro!.

Gabaɗayansu suka tafi suka faɗa jikinsa. Da sauri suka kai kallonsu a kansa, take Pretty ta canza murya izuwa na shagwaɓa da ta saba yi wa Smart, a sanyaye ta ce. "Ni kam wai yanaga ka canza dayawa ne? Ka kara haske da kyau sosai kamar ba mutum ba". (Kun san Black Tiger baya fita rana, kai ko inuwa ma baya fita yana ciki kullum, so dole skin ɗinsa zata banbanta da ta sauran mutane, dole su rinƙa ganinsa kamar ba mutum ba, kyansa zata banbanta da kowa, infact dole ya fita daban!!)

In baku manta ba ita Pretty bata san fuskar Black Tiger ba, a lokacin da ta suma akwai mask a face É—insa, so bata ga yana kama da Smart ba shiyasa yanzu ta ce Smart ne.

Dawo da kallonta a kanta Sweetie ta yi kafin ta ce. "Kin san shi ne dama?"...... Kai ta shiga gyaɗawa a kan e ta san shi. A maimakon Sweetie ta tambayeta a ina ta san shi domin su warwarewa juya cewa mutum biyu ne masu kama ɗaya, sai zumuɗin ganinta yasa bata tambaya ba, ta bar zancen tare da cewa ta zo su je ta shirya mata abinci. Ta kai karshen maganar tare da barin jikin Black Tiger, ta ja hannun Pretty suka yi waje.... Yanzu Pretty tana yi wa Black Tiger kallon Smart Tiger ne, ga shi dikkansu basu san mutum biyu ne masu kama ɗaya ba, me kuke tinanin zai faru? Ga Sweetie da kishi, Pretty da son jiki da shagwaɓa!.

Sai a lokacin Pretty ta fara bin ɗakin da kallo, mamaki ne ya kamata ganin irin wannan Daula da bata taɓa gani ba, kamar zata tambayi Sweetie ina ne nan, sai kuma ta fasa suka wuce kawai, kun san bata son yawan magana.

Da kallo Black Tiger ya bisu da shi har sai da suka kurewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke a hankali, lokaci guda tinanin Mommah ya faɗo cikin ransa, a fili ya furta. "Meyasa matar nan ta tsaya mun a rai?". Ya yi maganar tare miƙewa ya koma dining area ɗinsa. Ji yake yi tamkar yasa a ɗauko Mommah, yana tinanin Smart sosai, amma ya fi tina Mommah da dalilin dayasa yake kama da Smart over haka, shi da kansa yanzu zuciyarsa ta fara gasgata cewa su ne iyayensa, sai dai kuma ya yi ƙoƙarin ignoring hakan, yaki aminta.

Zama ya yi saman chair, take robot suka hau zuba mashi abinci. Cikin natsuwa ya hau ci, yana ci yana tinanin Mommah. Bai wani ci dayawa ba ya miƙe ya koma saman bed ɗinsa, zama ya yi a maimakon kwanciya, a ransa yake faɗin daga wannan sai wannan, shi da ya je neman Spender ya haɗu da abin da ya jefa zuciyarsa a tinani yake neman ɗauke hankalinsa daga kan burinsa na mulkar duniya, shin wai me yake damunsa ne? Dama ya ɗauko Pretty ne dan ya kawota ya bata farinciki ko kuwa dan ya kawota ta bashi Spender? Bai taɓa zatan zai dakata a kan neman cikar burinsa dede da second ɗaya ba a rayuwarsa, sai ga shi abubuwa biyu sun yi mashi kutse cikin burin nasa a lokaci guda, mutanen da suka yi kutse a rayuwarsa da sunan iyaye, da kuma burin da zuciyarsa take yi na son ganin Sweetie tana farinciki ko da shi ba zai yi ba, a dalilin haka ga shi ya gagara koda yi wa Pretty tsawa kan ta bashi Spender, dik saboda zuciyarsa taki aminta ya yi abin da zai sanya Sweetien kuka. WAI YA NE ZUCIYAR BIG BRO? YA KIKE NEMAN KAWO MANA WASU AL'AMURRA A LOKACIN DA MUKE GAB DA SAMUN CIKAR BURINMU NE? NA CE YANE? SWEETIE YANE? KI YI GAGGAWAR FITA RAYUWARMU DAN MU CIKA BURINMU NA MULKAR DUNIYA FA!!.

Ya jima zaune yana tinani kafin ya gyara ya kwanta, da kyar barcin huce gajiya ta yi awon gaba da shi. Ba shi ya farka na sai karfe 8 na dare, da kyar ya iya waro idanunsa, zuciyarsa cike tab da tinanin Mommah har yanzu, jikinsa dik a mace ya miƙe ya ƙarisa gaban mirror ɗinsa. Take ya juya magic eyes ɗinsa ya fara ƙoƙarin samo CROWN OF POWER ko zai kalli Mommah ya ɗan ji sanyi a ransa. Sai dai ya yi iyaka ƙoƙarinsa bai iya gano in da take ba a cikin kingdom ɗin, dan haka sai ya ce bari ya yi wanka ya watsake ya sake gwadawa ko zai iya ganinta.

Toilet ya nufa zuciyarsa tana tinanin ina Sweetie yau sam bata leƙosa ba, saboda ta samu ƴar uwarta, da haka ya shiga wanka. Ita kuwa Sweetie tana can, sai ɗurawa Pretty abinci take yi, tana barin bedroom ɗinsa kai tsaye ta wuce zuwa ta tashi Ronnie daga barci, sai murna take yi tana tsalle. Ai Ronnie sai da ya ji shocked lokacin da ya kalli Pretty, har ga ALLAH yaga kamarsa da ita, da alama jininsa ya fi karfi da ita a kan Sweetie.

Lokaci guda a ransa ya ji ya yi mata, tin da yana sa rai da fatan yayansa ya yi wuff da Sweetie, shi kuma ai sai ya yi wuff da Pretty, shikenan su haÉ—esu waje guda.

(Ni kuma na ce team Smart zaku yarda kuwa? Ronnie zai yi wuff da ƴar tsana, kun fa san Ronnie ya fi Smart iya love, dan haka zai iya sace zuciyarta🤸)

Hannu ya baiwa Pretty da nufin su gaisa yana sakar mata murmushi, kun san an ce blood is thicker than water, pretty bata taɓa yarda kowa ya taɓa jikinta ko da sunan wasa, amma sai ga shi tashi ɗaya ta baiwa Ronnie hannunta suka gaisa tana murmushin da a baya bata yi, ko Smart bata yi mashi murmushi, sai gata tana yi wa Ronnie, lokaci guda ta ji zuciyarta ta gamsu da shi, tamkar yacce ta yi saurin sabo da Kamran, haka ta ji Ronnie a ranta, sai take ganinsa kamar Kamran, kun san dik kamannin guda ne, Koreans ne!.

ÆŠan rungumanta Ronnie ya yi yana kara yi mata welcome, cike da zolaya ya ce da Sweetie. "Sis É—inmu ta fiki kyau, gashin kai kawai kika fita mai kyau da É—aukar hankali".

MuguÉ—a mashi baki ta yi kafin ta ce. "Ashe dai akwai abin da na fita kyau É—in da shi? To wannan gashin da kake gani mom ta ce shi ne kalar gashi mafi tsada a duniya, shi kaÉ—ai ma arziki ne, faÉ—a mun abin da take da shi mai arzikin rabin gashin nawa?". Tana magana tana wurga mashi hararar wasa.

Raba jikinsa dana Pretty ya yi tare da kai hannu zai capkota ya samu damar matse bakin da take murguɗa mashi ɗin nan, sai dai ina, ai yana kawo hannu ta watsa da gudu sai waje tana dariya mara sauti!. Hannun Pretty ya riƙo yana faɗin. "Zo muje in baki abinci, rabu da sis ɗin nan bata ji, kullum haka nike fama da ita".

Cike da mamakin kyawawan halayen Ronnie Pretty ta ce. "Amma kana da hali irin na Yah Omar É—inmu (guyson)". Hannunsa yasa yana cire password na door ya ce. "ALLAH sarki, to ki É—aukeni a matsayin shi ne kawai".
Chapter 11 · 0% Book details