← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 130

Sashe 35

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan hankalin Smart ya yi dubu a wannan lokaci ya tashi, take zuciyarsa ta karaya da karanto addu'ar, kirjinsa na bugawa da karfi-karfi, ALLAH sarki bai san komai ba, kun ga da kamar Sweetie ce ta san da matsalar dama, da zasu san abin yi.

Tinawa da ya yi cewa dik karfin sharri addu'a na ruguzasa ne yasa ya cigaba da karanto suratul baƙara ɗin. A karo na biyu ya tofa mashi. Haba ai wani irin ihun da Big Bro ya kurma sai da gabaɗaya empire ɗin ta amsa, hakan kuma ya yi sanadiyar farfaɗowar Sweetie dake sume, Ronnie ya ɗaura kanta a saman cinyarsa yana tofa mata addu'oi, Pretty dai tana zaune sai ruwan hawaye take yi tana ta faman ambatar sunan Sweetie.

Tana waro idanunta waje ta fara tari mai sautin gaske. Cikin wannan tari take faÉ—in. "Ina Big Bro bro ina Big Bro?". Ta yi maganar idanunta a kan Ronnie dake kallonta. "Sis menene yake faruwa? Ke zamu tambaya ina Big Bro? Sannan me ya sameki? Meyasa twin brother É—in Big Bro ya ce kada mu sake mu fita?".

Da jin haka ta zabura ta miƙe zaune a tsakiyar gadon. Fuska jaga-jaga da hawaye Pretty ta rungumota tana faɗin alhamdulillah Sweetie ta farka. Ita kuwa tana zazzare ido ta zare Pretty daga jikinta. "Yazama dole in ga Big Bro a yanzu". Ta faɗa tana yunƙurin saukowa daga gadon.

Da gudu Ronnie ya riketa yana girgiza mata kai, cikin natsuwa ya ce. "Twin brother ɗin Big Bro ya ce kada mu fita". Ya faɗa yana kara ƙanƙame hannunta. Ai ina fisgewa ta yi, da sauri ta diro ƙasa, ƙafafunta suna kerma, da kyar take iya taka ƙasa, amma saboda dauriya da jajircewa na son cikar burinta haka ta nufi wajen. Kafin Ronnie ya diro kasa ya rikota tuni ta buɗe kofa ta fita.

---------------------🔥

Smart yana tofa mashi wannan addu'a a karo na uku, wani irin kururuwa mai doɗe kunne da ya zunduma har sai da yasa Smart ya ji kamar ya gudu. Lokaci guda ya kara kame jikinsa tamkar wanda ake zuba mashi wuta, da alama azaba yake ji sosai daga ta cikin jikinsa, yana wani irin numfashi tamkar gurnanin zaki, yana kara mimmiƙewa, daurewa Smart ya yi ya kara tofa mashi a karo na huɗu. Haba sai ga Big Bro ya yi watsa-watsa da sarkar da aka ɗauresa da shi ɗin, ya yi wani irin kururuwa ya tsinke sarkar. Kafin Smart ya ankara sai ganin mutum ya yi tsaye a kan kafafunsa a tsakiyar bed ɗin, a wannan lokaci babu mahalukin da yake iya ganin fuskar Big Bro, saboda arab hairnsa da ya rufe mashi.

Wani irin razana da Smart ya yi har bai san time da ya miƙe tsaye ba, sai dai bai gama farfaɗowa daga razanar ba Big Bro ya diro a gabansa. Gabaɗaya addu'a ce ta kwace daga bakin Smart, ya ji tamkar an shake mashi makogwaransa, dai'dai lokacin su Sweetie suka turo kofar suka shigo.

Zaro idanu Smart ya yi yana kallonsu, cikin É—aga murya ya ce. "Ku juya ku gudu tin kan ku rasa rayukanku". Girgiza mashi kai Sweetie ta yi, cikin muryarta dake ta faman sarkewa ta ce. "Kada ka gudu kuma kada ka ji tsoro, saboda shaiÉ—ani baya haÉ—uwa da ayar ALLAH, ni nasan ko su waye ne, saboda na yi mashi addu'a kwanaki na shiga tsakaninsu shi ne suka fusata, shi ne yanzu suka san ta hanyar da suka bi suka dawo jikinsa suna cutarsa da sunan wai shi nasu ne, tabbas zamu yi addu'a ba zamu gudu ba, kuma da izinin mai iko da ni da su, wanda ya halicceni ya haliccesu sai sun rabu da shi, sai ALLAH ya yi mashi katangar karfe tsakaninsa da su". Da kyar ta iya kai karshen maganar!.

Zuba mata idanu Smart ya yi yana mamakin jin waÉ—an nan kalamai nata, kenan dama already É—an uwansa ya jima da wannan matsala? Lallai kuwa lokacin rabuwarsa da su ya yi In Sha ALLAH.

"Ronnie Pretty ku kare kanku ta hanyar karanta addu'oi dan kada ya iya tinkararku". Sweetie ta faÉ—a hawayen da suka cika mata idanu suna gangarowa, a wannan karan duniyar shaiÉ—anu sun dawo a fusace, sun ji haushin abin da Sweetie ta yi masu, dama sun tsaneta tun time da ta ji mashi ciwo ta fitar mashi da jini a jiki, sai ya haÉ—e dikka suna son É—aukar fansa.

Jin kalamanta ya karfafawa Smart gwiwa a in da ya dage ya cigaba da addu'oi babu kama hannun yaro, take Big Bro ya kara rikice masu yana wani irin gurnani mai ban tsoro. Sun tsorata matuƙar tsorata, amma suka daure suka haɗa baki wajen cigaba da karanto addu'oi da karfi-karfi cikin ɗaga murya.

Lokaci guda Big Bro ya fara wani irin jijiga, kafin su farga sai ganinsa suka yi a jikin bango ta wajen balcony ba ta in da suke ba. Har Smart zai bi bayansa Sweetie ta ce mashi. "A'a kada ka je, ka cigaba da addu'a, in ka je zasu lahantaka ne.........".

Bata rufe baki ba sautin buga kansa a bango ya dakatar da ita, da karfi ya hau buga kansa da jikin bango yana wani irin ihu haÉ—e da gurnani. Sosai hankalin Smart ya tashi yana jin ba zai iya jure ganinsa a cikin wannan mawuyacin hali ba, amma ya sai datse idanunsa yana cigaba da karanto addu'oinsa.

Dikkansu datse idanunsu suka yi saboda halin da Big Bro yake a ciki ya kazanta ba zasu iya gani ba. Sai dai kuma a lokacin guda suka waro idanun nasu sakamakon jin sautin karar glass ya tarwatse a kasa da suka yi, a miliyan suka buɗe idanunsu. Bawan ALLAH buga kansa da jikin door glass da zai sadaka da balconynsa ya rinƙa yi sai da glass ɗin ta tarwatse, gabaɗaya goshinsa ta fashe rugu-rugu jini na ta malala tamkar an buɗe tap, har lokacin jikinsa na wani irin jijjiga mai matuƙar ruɗarwa.

Ai Sweetie da take cewa kada su je in da yake bata san lokacin da ta watsa a miliyan ta isa gabansa ba, dai'dai lokacin kuma ya zube kasa cikin glasses ɗin da suka yi rugu-rugu ɗin ya faɗi baya numfashi. Ihu mai sauti ta zunduma tare da kwala mashi wani irin kira tamkar maƙoshinta zai ɓalle.

Da gudu su Smart ma suka yi kansa, da alama abubuwan sun sake shi sun gudu, hegu sun ji addu'a. Kuka sosai Sweetie take yi tasa hannun tana tattare arab hairnsa da ya jike sharkaf da jinin da ya rinƙa gangarowa daga goshinsa, cike da tashin hankali take faɗin. "Koma meyafaru ni na ja maka, da ban yi maka maganar addini ba da dik baka azabtu haka ba, nina zama sanadin wanann ciwo da ka ji, dan ALLAH ka tashi kada ka mutu, ni na yarda zamu zauna da kai a haka ko babu addini". Cikin fitar hayyaci take sambatun nata.

Shi ma Ronnie kuka yake yi sosai tamkar ransa zai fita, saboda kun san dai yadda yake son yayansa tamkar ransa. A natse Smart ya ce. "Ku yi shiru yanzu zai samu lafiya ai". Ya yi maganar tare da gyara hannunsa, yasa karfinsa da kyau ya cicciɓi Black Tiger sama, ya ɗaura saman shoulder ɗinsa ya wuce da shi sai saman bed, gabaɗaya bawan ALLAH ya ji wa kansa uban ciwo, jini ne yake ta zuba daga jikinsa kamar an buɗe tap.

Da gudu su Sweetie suka biyosa kan gadan, Ronnie ya ce bari ya kawo kayan aiki ya yi treating na yayan nasa, ita kuma Sweetie a saitin kansa ta zauna ta cigaba da karanto addu'oi tana tofa mashi. A tare Smart da Ronnie suka taimaka mashi wajen gyara mashi fuska da ya ji ciwo da damatsan hannunsa, sannan suka bashi allurai.

A daren wannan rana dai babu wanda ya rintsa a cikinsu, a zaune suka kwana, batun party kuma dai ba'ayi shi ba, Ronnie ya dakatar da shi saboda halin da suka shiga. Wasa wasa har tsawon kwanaki uku Big Bro bai farfaÉ—o ba, kuma suna bashi kulawa sosai, ga zuciyarsa na bugawa dai'dai, amma shiru bai farfaÉ—o ba. Likitoci sun yi iyaka yinsu, sai dai suka zubawa sarautar ALLAH idanu.

A ranar na uku da sumansa ne wasu jiga-jigan jiragen sama suka dira a birnin, Smart ya ji saukarsu, to da yake bai san komai dangane da birnin ba sai bai wani damu ba. Bayan sauran jirage da kamar minti 20 Ronnie ya isko Smart zaune a balconyn Big Bro yana dube-dube cikin É—aya laptop na Big Bro É—in, sallama ya yi mashi a natse kafin ya kariso ciki, da kallo Smart ya bisa yana mamakin irin raman da Ronnie da Sweetie suka yi a sanadin kwanciyar Big Bro. NI KUWA NA CE DAN BAI SAN IRIN SHAKUWAR DAKE A TSAKANINSU BANE, BAI SAN IRIN SON DA SUKE YI WA BIG BRO BANE DA BA ZAI YI MAMAKIN RAMANSU BA!!.

Saman sofa Ronnie ya zauna, a natse ya ce. "Babban yaya Big Bro ya yi baki". Fuska a É—an É—auke da mamaki Smart ya ce. "Baki kuma?".

Kai Ronnie ya jinjina kafin ya ce. "Ka duba wayarsa ko laptop É—insa ina da tabbacin zaka ga appointment É—insu, dan Big Bro baki basa zuwa mashi haka kawai, sai ya basu izinin ganinsa da kuma dik abin da ya dace".

Jinjina kai Smart ya yi kafin ya bukaci da ya kawo mashi wayar Big Bro, a hanzarce ya tashi ya É—auko mashi, da fingerprint É—insa ya cire lock na wayar ya shiga ciki ya fara bincike, nan ya tarar da zancen bakin, ya É—an yi mamakin ganin waÉ—an da suke da zama da shi, ciki harda his excellency na Us, abin ya É—an sanya Smart shakku a kan me suke son ganin É—an uwansa? Sannan girman Black Tiger ya kai har su iya takowa zuwa wannan birni? Tab abin babba ne. Ga wakilin sarkin England ma har da shi.

Miƙewa ya yi tare da cewa. "Ku yi masu iso zan gansu a matsayin shi dik da ban san a kan me zasu tatauna ba". Ronnie bai ji komai ba, dan yana ganin abin da ya yi Smart shi ya yi Black Tiger, dan haka sai ya miƙe ya nufi waje.
Chapter 35 · 0% Book details