← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 130

Sashe 110

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da tashin hankali ta ja hannun Pretty suka nufi parlon King. Nan ta isko su mama, kusan dai dikka family suna a wajen, ga King yana zaune a saman sofa, kun tina zaman da jiya ya ce yau za'ayi? To shi ne ya fara haÉ—o kan family dan ayi wannan zama, ita ma Momma É—in sau biyu yana kiran numbarta dan ya ce tazo tare da su Smart amma bata É—aga ba.

Kasancewar Pretty na kuka ne yasa dik suka kai kallonsu a kanta. Jaish ne ya miƙe yana tambayar momma ko lafiya. A tsananin ruɗe ta ce. "Ina fa lafiya. Ranka ya daɗe anyi poisoning Omerish". Ta faɗa tana kallon King.

Ai yana daga zaune bai san time da ya miƙe a miliyan ba, har yana haɗe word wajen cewa. "Ban gane anyi poisoning Omerish ba?".

Bayani momma ta shiga yi masu yadda komai ya wakana. Salati gabaɗaya parlon suka saka, guyson dake a zaune kusa da mummyn Chuchu, ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta yana zuba mata shagwaɓar da ya saba ne, in baku manta ba dama ɗan ɗakin ta ne. A miliyan ya miƙe yana zaro ido cikin tashin hankali. Obaid and Omaid dik a razane suka mimmiƙe suna salati.

Jaish, King, Mummyn Chuchu, guyson har suna haÉ—a baki wajen cewa ina Smart É—in yake a kaisu wajensa..

Nan fa Momma ta sanar da su Big Bro ya rufe kofar suna cikin É—aki da shi, dan haka dole a jira fitowarsa kawai.

Mama ce ta É—an ja siririn tsaki yadda kowa ba zai iya ji ba, a ranta ta ce in ya mutu sai na fi kowa murna, a fili kuma ta mike tsaye ita ma tana binsu one by one da kallo wai dan kada ace ita bata damu ba.

Ciza laɓɓa King ya yi kafin ya ce. "Dama ni hankalina bai kwanta da waɗan nan ƴaƴan Omranish ɗin ba, kawai saboda bani san rigimar Omerish ne yasa na yi shiru, amma ni nasan barewa ba zata taɓa yin gudu ɗanta ya yi rareafe ba".

Cikin rashin fahimtar in da kalamansa suka dosa momma ta ce. "Ban gane nufinka ba". Cike da manaki ta yi magamar. Nan fa kallon gabaÉ—aya jama'ar parlon ya koma kanta.

Cikin kakkausar murya king ya ce. "Har kuna da bakin zuwa neman wacce ta yi poisoning É—insa bayan kuna tare da mugun iri a waje!!". Ya yi maganar yana kallon Pretty dake ta faman shessheka tamkar zata haÉ—iyi zuciya.

Daidai lokacin Sweetie ta shigo parlon da gudu, dan ta ji hayaniya, to ta zaci faÉ—a ake sake yi da Ronnie shiyasa ta zo. Ai Pretty na ganinta ta kwace rikon da momma ta yi mata, da gudu ta tafi ta faÉ—a jikin Sweetie tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Rungumeta Sweetie ta yi, a ruÉ—e take faÉ—in. "Lafiya Pretty, meyake faruwa?". Cikin kuka tamkar ranta zai fita ta ce. "Sweetie ki ce Yah Omerish ya tashi, dan ALLAH ya tashi kada ya mutu"...... Cikin rashin fahimta Sweetie ta ce. "Ban gane ya tashi ba? Akwai abin da ya faru ne? Ina yake?".

Kara rungumota Pretty ta yi, cikin kuka ta zayyano mata dik abin da yake faruwa. Salati Sweetie ta saka kafin ta kara rungumeta ita ma suka rushe da kuka a tare.

Zuba masu ido dikka jama'ar parlon suka yi, wasu sun basu tausayi wasu kuma haushi, wasu na tayasu jimami wasu kuma suna tayasu kukan, wasu kuma suna ALLAH ya kara.

"Jaish bana son ganin waÉ—an nan Æ´aÆ´a a gabana ko a cikin gidana, suna kara mun bakiciki kan wanda nike ciki, ku fitar mun da su, kuma ba zan yafe kashe Omerish da suke son yi ba, dole su fuskanci hukunci!". Cewe King kenan.

Idan hankalin Momma ya yi dubu to ya tashi, cike da damuwa ta ce. "ALLAH ya kara maka tsawon rai, amma dai kasan waɗan nan yara ba zasu iya aikata wannan laifi ba ko? Ina da tabbacin ko kaza ba zasu iya kashewa bare kuma mutum, mutum ɗinma mijinsu, kai a'a, akwai dai abin da ya saɓa.......".

Hannu King ya É—aga wanda ya sanyata dakatawa da yin maganar. "Rahilarh kina raina makiya, kin san jinin kiyayya kuwa? Ai idan mutum baya sonka baya sonka ne, na tabbata su suka shirya wannan abin".

Kallon kallo ya koma faruwa a cikin parlon, su Sareena kansu ya shiga duhu suna son a warware masu shi, burinsu kawai su ji meyake faruwa dallah dallah. Su uncle Abbas wannan ya kalli wannan, wannan ma ya kalli wannan, Jaish and Jawad dik da basu san su Pretty ba sosai ba, amma sun ji a ransu ba zasu iya aikata wannan laifi da ake zarginsu da shi ba.

Uncle Jahiz ne ya katse kallon-kallon nasu da cewa. "Yaya, ina da tabbacin abin da aunty Rahilarh ta faɗa gaskiya ne, waɗan nan yara ba zasu taɓa aikata wannan babban laifi ba, kada ka manta yanayin yadda tsarin tsaron abincin ƴaƴan gidan nan yake, a kicin kawai Cameras sun fi goma, kai ba karamin kwaro bane ya shirya wannan abin, waɗan nan yara wayansu ba zai taɓa kaiwa irin wanna plan ɗin ba".

Uncle Abbas ne ya karɓi zancen da cewa. "Tabbas ba zasu iya aikata wannan laifi ba, sai dai kuma in shiryawar aka yi tare da su, ma'ana aka shirya masu, amma wannan laifi sun yi kakana wajen iya shiryasa".

Mummyn Chuchu ce ta karɓi zancen da cewa. "Please ranka ya dade ka duba wannan magana, wlh ina da tabbacin waɗan nan yara basu yi wayon da zasu shirya wanna shiri ba, kada ka manta ita Omaish tare da babban yayansu ta zo, in tana da niyar kashe Omerish ai da tin kafin su zo nan zasu kashe shi, ko baka san labarin irin rayuwar da suka yi a masarautar baban yayan nasu bane?". Ta tambaya tana kallonsa. Kun san mummyn Chuchu da Momma kansu a haɗe yake, to momma ta bata labarin irin rayuwar da suka yi a Black World tamkar yadda Sweetie and Pretty suka bata labari, to shi King bai sani ba, dan bai zauna da momma a kansu ba.

Jaish ne ya ce. "Dad ka duba please". Sun bawa Jaish tausayi ne yasa ya sanya baki, dan in baku manta ba shi Jaish baya shiga case na gidan, sannan yana ji tamkar Sweetie and Mahnoor suna da alaƙa saboda in ya ɗaga idanu ya kalli Sweetie a fusge wlh sai ya ga kamar Mahnoor, dikkansu suna da gurun wuya mai kyau da ɗaukar hankali.

Ni Queen of surprise na ce baku yi mamakin yadda aka yi suke da kamanceceniyar wasu daga cikin suffa ba? Kada ku manta yanayin kirar jikin koreans, ba'a cika samu masu dirin halittar good bye and welcome yadda yakamata ba, saboda yanayin su sirara sai shape, to su Sweetie ya aka yi suke da shi? E ba yadda ALLAH baya halitta a dik sanda ya so, amma akwai na gado, siffofin Sweetie banbancinsa kaɗan ne da Mahnnoor, fuskar Sweetie and Pretty da skin ɗinsu ne da ka gansu ka ga koreans, amma tabbas akwai kama ta jini a tsakaninsu da Mahnoor. Wayyo ni cakwakiyar RAWANIN ZALINCI zai soma kuma, kwana biyu kaina ya ɗan huta, to dai ku karɓi wannan surprise ɗin, Sweetie, Pretty, Mahnoor, Mahreen suna da alaƙa mai karfin gaske ta jini, shiyasa dik iskancin Pretty batai wa Mahnoor, ba banza ba Sweetie take balain son Mahnoor, ba a banza Mahreen ta makalewa Sweetie ba, jini ba wasa ba! NI KAM PRINCESS TEEMA yaushe zan yi rubutu dama ban baiwa kasata Nigeria power ba? Mugun ji da Nigeria ɗin fa nike in faɗa maku gaskiya to. Amma ta ina kuke tinanin Sweetie, Pretty, Mahnoor and Mahreen suka haɗa alaƙa? Bari in haɗaku da tinani a nan kuma ku ɗanɗana bye sai wacce zata warware maku cakwakiyar nan ta bayyana, dan bata bayyana ba.

Gyaran murya Jawad ma ya ɗan yi wajen cewa. "Dan ALLAH dad ka duba, wlh ba zasu iya wannan aiki ba, ka gansu mana, ko Zunaira zata fisu shekaru fa!". Ya faɗa yana kallonsu. Kun san shi kuma Jawad meyasa ya sanya baki a maganar? Saboda Sweetie tanai mashi yanayi da Chuchu, already ya jima yana ganin kamanceceniyar Chuchu da Mahnoor, magana ce kawai bai taɓa yi ba, ya ɗauka kawai kawancen da Chuchu and Mahnoor ɗin suka kulla mai karfi suka zama kamar hanta da jini ne yasa yake jinsu tamkar jini guda, kai bari in barku haka, gaba na sake warware maku hadda, ai surprise bata kare ba, masu zafi suna zuwa a gaba!!.

Shiru King ya yi bai tankasu ba, saboda bai ga dalilin da zai sanya ya É—agawa su Sweetie kafa ba. Wannan shiru da ya yi tafi komai É—aga masu hankali, dan wannan shiru da ya yi yana nuna masu alamar tin da sun fishi sanin abin da ya dace sai su yanke hukuncu, shiyasa dik suka sha jinin jikinsu suka koma gefe suka yi shiru cike da shakka da tsoron buÉ—ar bakinsa.

Good 5 mins ya É—auka yana binsu kallon kafin ya ce. "Jaish bana son in sake ganin waÉ—an nan yara a nan, ku zubamun su a kurkukun masarautar nan na ce!". Yana magana yana É—an dafe saitin kirjinsa, saboda yana tina baya kirjinsa na zafi.

Da sauri momma ta sake cewa. "Dan ALLAH ka yi hakuri, wlh ni na tabbata ba zasu iya aikata wanna laifi ba ko da wasa! Ka tsaya a yi bincike".

"Rahilarh, waÉ—an nan jinin Omranish ne, babu abin da ba za su iya aikatawa ba, ni nasan waye ubansu, ni nasan bakin hali da zaluncin Omranish! Dole su yi gado dama, shiyasa na tsani jininsa da shi da Abdul Raof, dan haka yaki yanzu aka fara, kuma wlh ba zan É—agawa kowa kafa ba! Ku jefa mun su a Prison tare da horo mai tsananin gaske da sai sun gwammaci mutuwa!!". With harsh voice ya yi maganar, ya yi ta kuma yana pointining É—in su Pretty da suka rungumi juna suna kuka.
Chapter 110 · 0% Book details