← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 130

Sashe 46

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai ta yi. "Kuma haka ne, amma ni yakamata in rikeka ai ko?". Kai ya gyaÉ—a mata yana kara jin tsananin sonta a ransa. Juya hannu ta yi ta rikesa suka karisa gym É—in zuciyarta cike da tinanin irin fansan da zata É—auka a kansu Sareena a daren wannan rana, ta yi alkawarin ba zata bari gari ya waye ba tare da ta harhaÉ—a masu jini da majina ba, dan ma nan gaba su san Nigerians fa ba sa'an yin su bane, mun wuci nan!!

A hankali ya fara koya mata yadda zata motsa jikinta da sauran abubuwa, dik abin da yake yi ya shiga koya mata a natse cike da kulawa, yana yi yana kare mata kallo cike da zallar madarar kaunarta bawan ALLAH. Ita kuwa ta zage wai zata kara karfi.

CROWN OF INJUSTICE.🔥

Ɗakinsu ta faɗa ta murji kukanta son ranta, har barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Tana tsaka da barci Ronnie ya zo ya dubata, amma bai tasheta ba, ya kyaleta tare da ficewa. Ba ita ta farka ba sai around 2 na rana.

A hankali ta fara motsa idanun nata da suka yi mata nauyi, kun san kuka tasha kafin barci, so idanunta sun yi nauyi sosai. A hankali ta warosu waje tare da miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin, dik jikinta tsami ta ji ya yi mata, tinani ta fara yi a kan yadda za'ayi tasa Big Bro ya yi magana kan mom ɗinsu, tasan tin da ya faro maganar to ba shakka yasan wani abin dangane da ita, dole ta nemo hanyar sanya shi ya buɗe baki ya kora jawabi ko yaki ko ya so.

Da wannan tinani a ranta ta miƙe ta nufi toilet dan yin wanka. A gurguje ta shirya cikin wata shegiyar doguwar riga mai bala'in kyau zubin Italians, ta yi fitinanen kyau, perfumes ta zuba a jikinta kafin ta fito ta yi niyyar sallah, dama suna da agreement na zuwa shopping ita da Ronnie wanda Smart ne ya basu izini, shiyasa ta yi wannan shiga.

Bayan ta idar da sallah ta zuba addu'oi sosai kan ALLAH ya ɗaurata bisa wuyar Big Bro ya faɗa mata ina mom ɗinsu take, ta na shafa addu'ar ta miƙe ta nufo waje. ALLAH sarki, sam zuciyarta bata iya yin fushi da shi, kai tsaye room ɗinsa ta nufa tana wani kwaɓe fuska tana turo baki.

Buɗe kofar ta yi ta shigo, wani irin musulmin kamshi da ya daki kofofin hancinta ne yasa ta ɗan dakata da tafiyar tana wani irin shaka. Har da lumshe idanu na ƴan sakanni ta sake warosu waje, kai tsaye sai a kan kyakkyawan face ɗinsa dake a tsaye a tsakiyar ɗakin yana ƙoƙarin sanya botir na rigarsa, da alama yanzu ya kammala shiryawa shi ma, daga bayansa Smart ne yake tsaye a gaban mirror yana gyara gashin kansa, sun yi shiga iri ɗaya, komai nasu iri ɗaya, sai suka kara fitowa a identical ɗin nasu da kyau.

Kurawa juna ido suka yi, zuciyar Big Bro sai jinjinawa kyanta yake yi. Shi ma kuma ya yi matukar burge zuciyar Omaish Omranish. Sai suka mace da kallo juna, a wannan karan ma sai da Smart ya fara yi rapka masu tapi rap-rap-rap sannan suka É—an farga, a hanzarce Big Bro ya zare kallansa daga kanta game da wucewa ya nufi dining area É—insa.

A kunyace sosai ta ce. "Yah Omerish ina wuni?". Ba tare da kalleta kai tsaye ba ya amsa da lafiya, sannan ya bi bayan Big Bro izuwa saman table dan cin abinci.

Sai da ya kusa isa wajen ya ce. "Bismillah ki zo mu ci a tare, Æ´ar uwarki tana barci". Cewar Smart kenan.

Kamar zata ce a'a, amma sai ta tina yanzu fa yakin sanya Big Bro ya faÉ—a mata ina mom É—insu zata yi, dan haka dole ta je kusa da shi. Da sauri ta bi bayan Smart, ga mamakinta sai ta isko Ronnie zaune a wajen, da sauri ta karisa kusa da shi ta zauna tana sakar mashi cool smile.

Shi ma abin da yake ta faman aika mata kenan, tana zama ya kai hannu zai shafi kyakkyawan golden hair É—inta kenan unexpected idanunsa suka sauka kan na Big Bro, lokaci guda Black Tiger ya dalla mashi wata uwar hararar da bai san ya yi ba.

Zaro idanu Ronnie ya yi, dan ko da sunan wasa Big Bro bai taɓa harararsa haka ba, sai ya kasa karisar da hannunsa izuwa kan Sweetie, ya tsaya cak yana son fahimtar ma'anar wanan harara da yayan nasa yake aiko mashi.

Shi kuma Big Bro ganin ya zaro mashi idanu ne yasa ya farga da ashe ya hararesa ne, É—an kara É—aure fuska ya yi tare da kawar da kallonsa daga kansu izuwa kan Smart wanda tin da suka zauna yake kallonsu, a kan idanunsa aka yi wannan dirama dikka, ya gama gano cewa Big Bro ma dai akwai wannan É—an banzar kishi na jinin modarawan a jininsa, dan haka dole ya yi taka tsantsan da shi.

Ganin su Smart yake kallo yasa ya kara É—aure angry face É—in nasa tamau, sannan a natse sosai ya ce. "Kallan fa?".

Smart yana kokarin jawo plate na abinci da robot suka kammala zuba mashi a yanzu ya ce. "Laifi ne dan na kalli É—an uwana abin da na fi kauna a rayuwata kuma bugun zuciyana?".

Hararar Big Bro ya wurga mashi kafin ya ce. "Bana son kallo, idan ka cigaba kuma zaka rasa idonka ne"........ "Baka son kallo, amma kana son kalle mana sister ko? Kuma baka gajiya da kallonta, sannan ita baka gajiya da ko zata shekara tana kall.......". Bai iya karisa maganar ba ya dakata sakamakon wani irin damka sa Big Bro ya kai mashi a arab hair É—insa, da karfi ya ja gashin har sai da Smart ya yi yar kara game da cewa. "Am so sorry mafaÉ—aci kawai".

Kin sakesa Big Bro ya yi har sai da ya sake cewa. "Am so so sorry my pleasure".

Sannan ne ya sakesa yana mai da hannu ya É—auki spoon. Yana sakinsa Smart ya ce. "Kai dai ka canza hali da saurin fusata". Sweetie da Ronnie dai sai kallonsu suke yi suka faÉ—aÉ—a murmushinsu.

Ko kallon in da yake Big Bro bai sake yi ba ya fara cin abincinsa a natse.

"Na zauna da mutanen nan naka da suka zo mun kuma tattauna". Cewar Smart, ya yi maganar yana kallon fuskar É—an uwan nasa. ÆŠagowa Big Bro ya yi ya tsaresa da ido ba tare da ya yi magana ba, alamar yana jiran karin bayani.

Kora mashi jawabin yadda suka kare da masu jajayen kunnuwa Smart ya yi, daidai lokacin da ya kai karshe Big Bro ya ɗebo abinci a spoon zai kai ɗan baki, ai bai san time da ya yi wani irin jifa da spoon ɗin ba, a fusace ya sa hannu ya daki table ɗin har sai da gabaɗaya plates ɗinsu ya girgiza, cups na ruwa wasu suka faɗi, bottle na ruwa ma haka wasu suka faɗi, take fuskarsa ta canza kala, ya kara ɗaureta tamau, idanunsa sun kaɗa jajir cikin lokacin ƙanƙani, with harsh voice sosai ya ce. "Da can ubansu ne yake bawa birnina tsaro da za su ce zasu bani tsaro in basu haɗin kai? To ni sai dai in basu tsaro ba dai su bani ba!! Na fi karfin wani ya taimaka mun! Dan haka kada su bari in kara ganin kafafunsu a birnina, idan ba haka ba, labarin karshen rayuwarsu ba zai yi daɗin bugawa a mujallu ba!!".

Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zai bar wajen, cikin gaggawa Smart ya miƙe ya tari gabansa, zuciyarsa na bugawa da karfi, dan yana mugun shakkar ɓacin ran ɗan uwan nasa, amma ba zai iya kyalesa bai ci abinci ba.

Sweetie da Ronnie dik sun sha jinin jikinsu, hankalinsu ya tashi sosai, a zabure suka mimmike suna zare idanu.

"Gaskiya ne sai dai ka basu tsaro, ni kaina na shaida hakan, but please my pleasure calm down ka zauna mu yi lunch a tare, zamu yi farinciki da hakan, kada ka bari wasu su ɓata mana wannan moment ɗin, we really like it".

ÆŠago ido ya yi ya kalli cikin kwayar idanun Smart, ban da zallar kaunarsa babu abin da ya gani kwance cikin kwayar idon É—an uwan nasa, yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta ya ce. "Ni bana neman taimakon kowa, na fi karfin hakan, dole ma in gwada masu ni ba'a sa'an yinsu bane!".

Smart ya gama fahimtar cewa shi da Big Bro ya tsani ace ya gaza ko kaÉ—an ne, wato shi ya tattare dik wani ji kima da isa ta jinin sarauta, wato sai dai ace wasu sun gaza ya tallafa masu. SAI DA KAI LAST BORN OF EVIL WORLD, KUMA KING OF BLACK WORLD!.

"Tabbas ba zaka taɓa neman taimakon kowa ba In Sha ALLAH, sai dai ka taimaka masu, kuma ka fi karfin neman taimako, muma mun shaida, su ɗin banza".

Kalaman Smart sun sanya ya É—an ji sanyi a ransa, har da sauke ajiyar zuciya, da alama yanzu Smart ya fara gano yadda zai zauna da É—an uwan nasa.

Shiru bai amsa ba, yana cigaba da huci a hankali-hankali, Smart ya fahimci cewa lallai Big Bro mutum ne mai wuyar mika wuya a kan abu, wato yanzu ya hakura har ciƙin zuciyarsa ɗin ma ba zai yarda ya hakura ba, ba zai koma ya zauna ya nuna masu ya hakura ba, dik wuya mika wuya kai tsaye ne ba zai yi ba saboda balain taurin kai, dan haka sai Smart ya riko hannunsa ya mayar da shi ya zaunar yana kara tausansa ta hanyar zuba mashi kalamai masu sanyaya zuciya.

Da haka suka samu ya ci abincin nan da kyar, suna gamawa ya miƙe ya koma cikin room ɗinsa, kallon Sweetie Smart ya yi, a natse ya ce. "Idan kun dawo daga shopping ina son yin magana dake, da farko na ce ba sai na nemi taimakonki ba, amma yanzu na gano matsalolin ɗan uwana suna da mugun yawa sosai, dole sai mun haɗa hannu, yanzu ku je shopping ɗin ku dawo". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya bar wajen.
Chapter 46 · 0% Book details