← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 130

Sashe 104

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumgumeta da kyau ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Dik mai rai mamaci ne, addu'a kawai take buƙata a wajenku kin ji?". Ya faɗa yana ɗago haɓarta daga kirjinsa. Kai ya jinjina mashi tana ƙoƙarin shanye hawayenta. Cigaba ya yi da cewa. "Yanzu na roki alfarma a kan bappa ya baiwa Omar ita, amma ya ce mun yarigada ya baiwa Faisal, idan har ya canza magana to fa bai yi adalci ba, dan ya baiwa Faisal ke, aka rusa maganar, kusan hauka ya yi, yanzu aka dannesa da ita ba zai iya warware alkawarin nan ba, amma shi kansa ya so mata Omar ɗin dan ta samu rayuwa mai kyau, sai dai ina da damar zuwa in samu Faisal, idan ya janye shi kuma a shirye yake ya bamu ita".

Shiru ta yi tana saurarensa, burinta kawai ta ji karshen zancen ya yakare. "Tin da Omar ya bayyana yana sonta to nasan da gaske yake yi, dan bai taɓa kwatanta hakan ba, kuma ni kaina ina san ya sameta ko dai ya yi farinciki irin wanda nike da na sameki". Ya faɗa tare da manna mata sumbata a kumatu, so yake ya mantar da ita batun mutuwar gwaggo da ta shiga damuwa a kai.

"Na taka har kofar gidansu Faisal, na je mashi da batun ya rushe auren Mahreen kome yake so zan bashi, da farko ya nuna gardama dan yana ganin wasa nike ba zan iya bashi ba, amma da na ce ya faɗi abin da yake so zan bashi ya janye buƙatarsa, sai ya ce to a bashi shanu guda ashirin zai janye, ni kuwa nasa aka nemo mun shanu guda ɗari a rugar na saya mashi da dollars na basa, take a wajen yasa aka rushe batun auren nasu".

Tsayawa ya yi yana kallon yadda ta fara sakin murmushi dan ta ji ba'a ɗaura auren da hamma Faisal ba. "A wajen bappa ya ce ya baiwa Omar ita, ni kuma bai ɓata lokaci ba na ce da bappa ba zan tafi a aura mata wani ba, sai dai a ɗaura aurenta a masallaci da anyi sallar azahar, dan ina tsaron Omar ɗina ya rasata, in takaice maki ban baro Jimeta ba sai da aka ɗaura wannan aure ta Omar da Mahreen, na biya sadaki, ko Momma bata sani ba sai yanzu da na dawo nike faɗa mata ai sun bamu auren, dama da zan tafi na faɗa mata auren zan je nema, tai mana fatan alkhairi sosai, ga shi addu'arta ta karɓu".

Ai wani irin kara ta saki tare da sanya hannu bibbiyu ta rungumesa, ta mance da damuwar mutuwar gwaggo. Rungumeta shi ma ya yi tare da jawo wayarsa dake saman bed É—in, number guyson ya dannawa kira. Yana É—auka ya ce. "Zo É—aki kasameni". Yana gama faÉ—in hakan y katse kiran ya mai da wayar gefe tare da gyarata a jikinsa sosai.

"I really missed you sosai, me kina tanada mun". Ya faÉ—a mata cikin raÉ—a. "Special abubuwa na tanada maka". Haba wani irin daÉ—i da ya ji bai san lokacin da ya sake matseta a jikinsa ba, daidai lokacin suka ji sallamar guyson daga waje. Da sauri ta sakesa tana shirin barin jikinsa tamkar wadda aka ce mata momma ce ko king or su Smart ne zasu shigo. A gefen bed É—in ta zauna tana satar kallonsa, while shi kuma ya yi wa Omar iso.

Ciki guyson ya shigo bakinsa a É—auke da sallama again. Da hannu Jaish ya nuna mashi saman sofa kan ya zauna zama ya yi yana faÉ—in. "Good evening Yah Jaish"......... "Evening how was your day?". Da Alhmdllh ya amsa kafin ya É—agawa Mahnoor ita ma gaisuwa.

Bayan nan shiru suka ɗan yi, a natse Jaish ya katse masu shirun ta hanyar fara yi mashi nasiha a kan ɓoye mashi yana son Mahreen da ya yi, ya ce kada ya sake ɓoye mashi dik abin da yake so, hakuri guyson ya bashi kansa a ƙasa.

Jinjina kai Jaish ya yi kafin ya cigaba da magana, ya zayyane mashi yadda komai ya faru har aka bashi auren Mahreen ɗin, yanzu sun zama mata da miji. Cikin tsananin farinciki ya zamo daga saman kujera ya durkushe kasa, sai da ya fara yi wa ALLAH sujada, ya yi godiya da irin brothers da ALLAH ya bashi masu matuƙar kaunarsa da son farincikinsa, sannan ya yi godiya kan mallaka mashi Mahreen da ya yi, first love ɗinsa, har idanunsa sai da suka cicciko da kwallah.

Murmushi Jaish ya yi kafin ya ce. "Babu komai, amma ni abin da nike so da kai yanzu kada ka nuna mata cewa kai mijinta ne, ka fara neman soyayyarta farko, hakan zai fi maka"....... Jinjina kai ya yi tare da kara yi wa Jaish godiya sosai.

"Kana iya tafiya, kuma ba wai na baka lasisin ka je ka yi ta takurawa sister ɗita bane, in ka yi mata laifi nai mata alkawarin hukuntaka"......... Jinjina kai ya ɗan yi, a sanyayye ya ce. "Amma zan rinƙa tsokanarta kaɗan-kaɗan ta hakance kawai zai sa muyi sabo har ta fara sona". A kunyace ya yi maganar.

Jaish dake murmushi ne ya amsa da. "E haka ne, amma dai kada ka rinƙa saka mun ita kuka, ɗazun ma ai ta kawo mun karanta". Ya faɗa yana binsa da kallo dan ya ga reaction ɗinsa, so yake ya tabbatar da abin da yake zargi a kan abin da ya yi mata, yana zargi breast ɗinta ya taɓa. NI KO NA CE BAKU SAN YA WUCI NAN BA MA, BABBAN SASHE YA TAƁA ƊAN ALBARKA, DAN MA DAI ABIN YA ZO DA SAUKI TIN DA A LOKACIN DA YA YI HAKAN MA AN RIGADA AN ƊAURA AURENSU TA ZAMA TASA, DAN HAKA KAYANSA YA GANI.

A miliyan Omar ya ɗago kansa, suna haɗa ido da Jaish sai kuma ya yi gaggawar sunkuyar da kai kasa yana faɗin. "Ka yi hakuri Yah Jaish ba zan sake ba, amma ai ita ce ta tunzurani ta ce mun ta taɓa ɗaukar maza sun fi goma, shi ne ni kuma na ce ban yarda da ita ba sai na duba virging ɗinta".

Ai saura kaɗan Jaish ya taune harshensa, saboda maganar ta fi karfinsa, har kamar zai ce ka duba ɗin? Sai kuma ya yi shiru, da sauri ya ce. "Tashi ka je sai da safe". Da alama Omar ya goge mashi hadda ne. Da sauri ya miƙe yana kallon Mahnoor dake ta yi mashi murmushi, dan ita bata gane kan hirarsa da Jaish ba.

Waje ya fito ya nufi room É—insh cike da murna, zai shiga kenan suka ci karo da su Omaid zasu shiga room É—in suma, in baku manta ba dama ya ce su zo su same shi a bedroom É—insa, to shi ne suka zo. Suna ganinsa cikin girmamawa suka ce. "Yah Omar gamu nan".

Kallon tsab yai masu kafin ya ce. "Kuje kawai sai da safe".... Yanzu yana cikin farinciki ne over, ba zai iya hukuntasu ba shiyasa ya ce su je sai da safe. Juyawa suka yi suka tafi shi kuma ya wuce ciki farinciki tamkar ya zuba ruwa kasa ya lashe.

AFTER SOME MINUTES.

----------------------------🔥

Sai da ya bari dare ta yi irin karfe 11 haka, ya fito daga room ɗinsu, already Ronnie ya yi barci abinsa, bedroom ɗinta ya nufa dan ya sake bata hakuri, tin da wannan abin ya faru bata sake yarda sun haɗu ba, in ta gansa gudu take yi, ashe dik wannan rashin kunya da tsiwar da take tsulawa akwai abin da take jin kunya, ya gane mata babban sashenta kunyarsa ya lulluɓeta over, ta so faɗawa Jaish ɗazun, amma ta rasa ta ya zata yi mashi bayani, tana jin kunya shiyasa ta danne abin a ranta, amma ta yi mashi ALLAH ya isa ya fi sau dubu a ranta.

Murɗa handle na door ɗin ya yi ya shigo bakinsa a ɗauke sa siririn sallama ƙasa-kasa. Tana zaune a tsakiyar bed ɗin, ta kifa kai da gwiwowinta kamar kuka take yi, abin da ya yi mata babu karya ya yi mata mugun zafi, kada ku manta dik rashin kunyarta bata taɓa yarda gwaggo kakarta ta yi mata wanka tin tana yar karamarta ma, ku tuna rayuwarta a kauye mana? Dik abin da zai bayyanar da babban sashenta bata shiri da shi, a kan kakarta ta yi mata wanka ta ga tsiraicinta gwara ta kwana da datti, shiyasa ta yi takaicin abin da ya yi mata, shi kansa da ya dawo hayyacinsa yasan bai kyauta mata ba ko kaɗan, shiyasa ma ya zo bata hakuri.

Ta yi nisa cikin kukan bata ji shigowarsa ba, hayewa saman bed É—in ya yi a natse dan yasan ita É—in yanzu mallakinsa ce. A kusa da ita ya zauna tare da kai hannu ya É—an É—ago da fuskarta da ya gama yin jaga-jaga da hawaye. A tinaninta ma Sweetie ce ko Zee or Pretty, dan sune suke shigo mata É—aki kai tsaye, sai dai tana É—ago kai ta ga shi ne.

A miliyan ta ja da baya tana kallon fuskarsa kafin ta sauke kallonta izuwa kyakkyawan silky pj's dake jikinsa, ya yi balain kyau, gashin kansan nan ya kara kwanciya luf har gaban goshinsa, ga wani sheki da yake yi, sai tashin wani irin daddaÉ—ar kamshi yake yi.

ÆŠan kura mata idanu ya yi kafin ya zare kallonsa daga kanta saboda wani irin kunyarta da yake ji, kayan jikinta ya bi da kallo, ganin abaya ne a jikinta yasa ya zargi anya ma ko abincin dare ta ci kuwa? Saboda yadda take yar gayu ya warhaka ba zaka sameta da wani kaya ba face na barci masu kyau tana tashin kamshi, amma wannan abaya tin da rana ita ce a jikinta bata canza ba.

Wani irin zafi ya ji zuciyarsa na yi mashi na ganin yadda hawaye ke gudana a kan fuskarta, ya yi nadamar abin da ya yi mata sosai. Cikin sanyin murya ya ce. "Meyasa kike kuka haka? Baki da lafiya ne ko wani ne bashi da lafiya?". Ba wai dan bai fahimci kukan me take yi ba ne yasa ya yi wannan tambaya, so yake yi ko kaÉ—an ne ta yi magana dan ya karanci girman fushin dake ranta ya san ta in da zai fara rarrashi.
Chapter 104 · 0% Book details