← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 130

Sashe 111

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momma da karfin hali dik da ta san ransa a ɓace bai hana ta sake cewa. "Ko ba komai akwai aure a tsakanin Omerish da Omnish, dan ALLAH ka duba wanna lamari.......". Tsawar da ya daka mata ne ya sanyata haɗiye sauran maganar bata karisar ba. "Keeeee Rahilarh! Baki san komai dangane da gabarmu ba, kin ji abin da kika ji ne kawai, dan haka kada ki sake yin magana a kan jinin Omranish!!".

Ya ilahi, gabaÉ—aya parlon ya koma kallon kallo, yau momma ake yi wa tsawa, lallai ba shakka dad ya kai kololuwa yau.

Poitining momma da yatsa ya yi. "A kan Omerish babu abin da ba zan yi ba, dan haka ki iya bakinki!!"......... Tsit parlon ya yi kowa ya sha jinin jikinsa jin yau faÉ—ar fa ta manyan kai ce.

"Jaish ku tattare mun waÉ—an nan tsiya daga gabana tin kan in sanya takobi da kaina in sare masu wuya!!". Dad ya sake faÉ—a........... Cike da shakkarsa da tsoron faÉ—arsa momma ta sake cewa. "Meyasa za'a haÉ—a da Omaish bayan babu sa hannunta a ciki? Omnish kawai ake zargi.........". Hannun da ya É—aga mata ne ya sanya ta dakatawa. "Komai kankantar jinin Omranish bazan barsa a gidan nan ba, dole dikkansu biyu za'a rataye!"...... Dum!! Dum kirjin momma ya buga saboda ta tina cewa ta kira Hoorain yana zuwa da Auta, ga shi shi ne first born na Omranish, dama ga kwantacciya a tsakaninsu da king É—in, watau akwai balai sabuwa kenan.

Daidai wannan lokacin Ronnie ya shigo cikin parlon shi ma, dan ya jiyo hayaniyar ne ya ce bari ya zo ya duba. Yana ɗaura idanunsa a kansu ya yi gaggawar nufarsu, abinku da jini ɗaya, take ya ji ransa ta yi mummunar ɓaci saboda kukan da yaga suke yi, tin ma bai ji laifin me suka yi aka sakasu kuka ba. Da gudu ya karisa wajen nasu tare da riko Sweetie yana tambayarta me yake faruwa kuma waye ya sakata kuka.

A wannan lolaci Jaish ya iso wajen dan ya cika umarnin mahaifinsa, hannu yasa zai kama Sweetie Ronnie ya rike hannun nasa, fuska a É—aure tamau ya ce. "Malam lafiya?!".

Nan fa parlon ya koma kallon kallo, King gyara tsayuwa ya yi yana kallonsu, yau ga ikon ALLAH, wai basu san suma su Sweetie da gatansu bane? Kamar yadda suke taƙama da Big Bro and Smart su ma su Sweetie suna da zakunan brothers da suka fi nasu yawa ma, ga sadauki Rishan, Hoorain, Kamdan and Ronnie, bugu da kari in baku manta ba Zarina tana da wani dakakken mayaki commander daga cikin mayakanta mai kama da Hoorain sosai ko? Kun tuna shi ya taɓa kashe Auta? To yana nan labari zai zo ta kansa, shi ma dik jininsu ne, kunga kuwa ai suma suna da gata da masu tsaya masu, ai ina ga da Kamran ne ma a wannan waje suka sanya mashi su Pretty kuka da ya zubar da maza goma kafin ya ji me ya samesu!.

Riko Ronnie Pretty ta yi tare da fasa mashi kuka mai sauti tana faÉ—in. "Wai cewa suka yi a kaimu prison, wlh ni bana son zuwa kada ka bari a tafi dani".

"Me kuka yi da za'a kaiku can?". Ya yi tambayar yana kallon Sweetie da banda kuka babu abin da take yi. Kasa bashi amsa Pretty ta yi sai kuka take yi mai taɓa zuciya. Rikota ya yi yana ɗan shafa bayanta alamar rarrashi kafin ya ce. "Babu wani mahalukin da ya isa ya kaiku prison idan ina raye, ku yi shiru!". Ya faɗa yana jefa da hannun Jaish da ya rike, sanan ya tsaya a gaban Sweetie and Pretty tamkar wani zaki yana fuskantar jama'ar cikin parlon.

Nan dai ran kowa ya ɓaci, wai kalaman Ronnie ya kona maru rai, tayaya zai ce bai ga mahalukin da ya isa ba, kenan ya raina har King?. Shi kuma ba wai raini bane, ransa ne ya ɓaci, kun san jini ba wasa ba, kuma yayansa Big Bro ya renesa ne ta hanyar da zai yi magana da kowa cikin jarumta ba tare da shakka ba, shiyasa ya faɗi hakan.

Nan fa izzar sarautar ta motsa, King ya ce a haɗa har da Ronnin dikka a tattare mashi su zuwa prison. Haba aikuwa Ronni gyara tsayuwarsa ya yi, jinin sarautar nan dai shi ma ita take gudana a jikinsa, cikin nuna jarumta ya ce. "Babu wanda ya isa ya taɓa mun sisters, ni dai zaku iya kaini, amma su babu wanda ya isa ya taɓasu!".

Uncle Abbas ne ya miƙe tsaye cikin fushi yana faɗin. "Kai yaro ka iya bakinka, hattara dai, yakamata kasan a in da kake!".

Sweetie and Pretty laɓewa suka yi a bayansa, suka rirrike shoulder ɗinsa suna cigaba da kuka......... "Kai kuma waye karan kaɗa miya? A kansu ba zan yi hattara da komai ba, na faɗa babu wanda ya isa ya kui su prison Ina raye!". Ya faɗa yana kallon tsakiyar idanun uncle Abbas babu ko shakkarsa.

Komawa gefe king ya yi yana jinjina kai, saboda yana ganin Ronnie yaga alamar jinin su Omranish a jikinsa shi ma.

Nan fa su Jawad suka miƙe dan dakatar da Ronnie, kowani ɗa na halak ba zai taɓa bari yaga ana cin mutumci iyayensa ba. Sai dai kuma Ronnie ba kanwan lasa bane, shi a yanayin tarbiyar da Big Bro ya bashi ko ina ya je shi sarki ne mai ji da kansa, dan haka da Mummyn Chuchu ta ce mashi a gaban sarki yake ya iya bakinsa, sai ya ce mata. "Idan shi sarki ne a nan, to nima sarki ne a Daular mu, kuma yayana ya ce mun ko'ina na je ni sarki ne!!".

Babu tsoro ko shakka a maganarsa, zallar jarumta da karfin hali. Su Dr Raj tsoron faÉ—a da Ronnie suke yi yanzu, dan suna tsoron ALLAH suna tsoron Big Bro, ga Bilal da uncle Taheer har yanzu suna asibiti basu san in da kansu yake ba, ina ai bazasu yarda su salwantar da tafiyarsu ba, dan haka sai suka ja baki suka yi shiru.

King ya fahimci dikka ƴaƴansa dake cikin parlon suna shakkar Ronnie, bai san shakkar taɓasa suke saboda balain Big Bro ba, dan haka sai yasa a kira mashi warriors guda biyar kan su zo su tatattare mashi harda Ronnie su yi prison da su, ya umarci su Mama, Mummyn Chuchu, Momma da su shiga ciki kada warriors su samu ganinsu, kun san killacesu ake yi.

Kallon King momma ta yi zata yi magana ya yi saurin É—aga mata hannu alamar baya son jin komai daga gareta, dole ba dan ta so ba ta nufi cikin room É—insa tare da su mama tana addu'ar ALLAH ya yayyafawa wanna cakwakiya ruwan sanyi.

Wasu dakakkun jaruman warriors guda biyar ne suka shigo cikin parlon, tamkar wasu bujuman zakuna. Kai tsaye king ya umarcesu da su fita mashi da Ronnie yanzu .

Su Dr Raj dik baya suka ja suna kallon ikon god. Ronnie ya so gwabza faÉ—a da su, sai dai kuma ina ba zai iya ba, dama dai su uku ne ko su biyu zai iya kwatar kansa, amma su 5 ba zai iya ba, and mayakan Kingdom of Power ba wasa ba, sun samu horo iya horo, dan haka sai suka damke Ronnie, uku suka rikesa gam, É—aya ya damki Pretty É—aya ya danki Sweetie, suna wani irin taku ma jarumta suka nufi waje da su.

Pretty da Sweetie sai kuka suke yi tamkar ba zasu rayu ba, sai ƙoƙarin miƙewa juna hannu suke yi, suna son rungume juna amma warriors ɗin nan sun hanasu.

Suna ƙoƙarin buɗe door na parlon su fita unexpected sai ganin mutum suka yi a gabansu, dik jarunta irin na warriors ɗin Kingdom ɗin nan sai da suka razana ganin yadda face ɗin Big Bro take babu alamar taushi. Dik cikin parlon guyson ne kawai ya ga shigowar Big Bro daga part na momma, amma saura dik hankalinsu na'a kan su Pretty.

Wani irin shaka ya kaiwa warrior da ya rike hannun Sweetie, ya shake mashi wuya da karfin gaske, hakan yasa dole ya saki Sweetie, da gudu ta tafi ta rumgume Pretty suna cigaba da kuka.

Saura warriors dake wajen dik suka yi gaggawar sakin su Ronnie suka ja da baya. Shi kuwa Big Bro hannu yasa zai zari takobin dake waist na warrior da ya shake dan ya datse mashi hannun da ya taɓa Queen Of His Heart da shi, sai dai king ya yi gaggawar shiga tsakaninsu yana ƙoƙarin tausan Big Bro ɗin.

Da kyar suka samu ya saki warrior ɗin, yana sakinsa warrior ɗin ya zube gwiwowinsa a kasa yana haki ya ji shakan manya. Shi kuma Big Bro cikin fushi ya ce. "Wani mai karan kwana ne ya sanya wani banza ya taɓa Omaish?".

Dik da shakkarsa da suke ji bai hana uncle Abbas daurewa ya ce. "Yana da kyau ku rinƙa sanin in da kuke, gaban sarki kuke, dan haka wajibi ne a kanku ku rinƙa tauna kalamai.......". Wani irin kallo da Big Bro ya dannawa uncle Abbas ne ya sanya shi haɗiye bakinsa cif.

"Babu wani sarki da zai kasance da sarauta idan ina waje, ni kaÉ—ai ne sarki, dan haka ku bani amsata". With harsh voice sosai ya yi maganar.

Uncle Abbas ya buÉ—e baki zai sake yin magana Jaish ya rigasa da cewa. "Big Bro uncle Abbas ne fa? Second dad É—inmu ne shi"........ "Then so what? Koma wanene shi ya sani ni sarki ne a dik Daular dana kasance a ciki!!".

Fusata iya fusata uncle Abbas ya yi, cikin É—aga murya ya ce. "Ni fa tamkar uba nike a wajenku, kamar yadda zaka girmama mahaifinka haka zak.......". Katse shi Big Bro ya yi da cewa. "Tamkar Uba ka ce ba Uba ba ai, bana son na sake jin bakinka a cikin parlon nan, in kuma ka sake ina magana kana yi zaka rasa tongue É—inka ne, dan sai na datse maka shi!".
Chapter 111 · 0% Book details