← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 130

Sashe 6

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

One thing, ita fa Khadijah tana son shi sosai, kuma ba wai bata san tana son shi ba, ta sani, kawai abin da ya yi mata ne yasa ta ɗaura ɗamayar hora shi, sannan bata da tabbacin a matsayin me suke a zaune yanzu! Shin zina ne? Ko dai mata da miji na sunnah? Tana buƙatar wannan amsa kafin nan ta san kalar hukuncin da zata yi mashi! Dan ta ci alwashin ba zata rabu da shi ba, ya je ya ɗaukota a ranar da mahaifinta ya rasu, kuma a ranar babu tausayin halin da take a ciki ya yi dis virgin ɗinta, ta yi kuka bai taɓa rarrashinta ba, sai ma wahala da yake kara mata na kowani dare sai ya zo ya biya buƙatarsa, ba hira mai daɗi, ko mara daɗin ma bata samu ba, babu abin da ya iya sai ikon bala'i, to wlh yanzu dai bai isa ba, zai san da jinin arewacin Nigeriya yake yi!.

A gaban mirror ta tsaya ta gama shafe-shafen manta dikka. Tana yi tana satar kallonsa, ya tsareta da waÉ—an nan dara-daran idanun nasa tamkar zai cinyeta da ido.

Da ta ɗan ɗaga bathrobe ɗin zata shafa mai ta ɗan saman cinyoyinta tana ganinsa har wani irin yawu ya haɗiye, sai da ƙashin makogwaransa ta motsa da ɗan karfi!.

A ranta ta ce sai ma na tabbatar matsayin me muke zaune zaka gane shayi ruwa ne, sai ka biya kuncin da ka sakani a ciki. Sai dai kuma kafin ta iya tabbatar da irin zaman da suke yi dole sai shi É—in zata tambaya, dan bata jin akwai wanda zai iya bata wannan amsa idan ba shi ba!.

Tsabar neman magana irin tata ta jima tana shafa mai a cinyoyinta kafin ta koma kan hannayenta. Shi dai bai ce mata ko uppan ba, dan ya lura kamar bata a cikin mood mai daÉ—i, da alama yanzu ya fara iya tantance a wani hali take a ciki! So ya fara gane lokacin da yakamata ya yi mata magana da akasin haka.

Da yake tasan tana da kaya a gidan sai ta wuce closet É—insu.

Ta sha madarar mamakin ganin yadda side ɗinta yake nan ba'a taɓa komai ba, sai ma uban tulin kayan da aka karo mata, hakan na nufin tana a cikin ran mai ɗakin, kullum tana a cikin tinaninsa. Uhm kun tina time da ya je gidan Smart ya sameshi a ranar da zasu fita yawo da su Pretty? Ai wannan rana ɓata ran da yake yi dik sabosa ita ne, damuwa da tinanin ina take ne ya yi mashi yawa, baku ji Smart yana ce mashi komai zai wuce ba, to kullum su suke rarrashinsa, dik kuma a kanta, shiyasa nace maku yana sonta, iskanci ne ta yi mashi yawa, yo iskanci mana, ai tin da Smart ya iya rarrashin ƴar tsana babu wanda ba zai iya kula da mace ba sai dai in iskanci ne ya cika mashi kai.

Yana dai zaune har ta fito shirye cikin wandon jeans and shirt, daka ta saman wandan ya kamata ya fitar mata da shape sosai, daga ta kasa kuma kafan wandan ya buɗe sosai, rigarta kuma mai ɗan dogon hannu ne wanda bai ƙarisa kai mata karshen hannunta ba, kuma rigar da kaɗan ta wuce cibiyarta, irin shigarsu dai na wajen shi ta yi, kuma dikka kayanta dake a cikin wajen irinsu ne kawai ya saya mata.

Ta ɗaura boyfriend Jacket a saman kayan, sannan kafafunta na sanye da safa ash color, ta yi kyau sosai, true beautynta ne ya ƙara bayyana without make up.

Ai malam Bobo kara rikicewa ya yi, ALLAH ya gani yana kewarta sosai, zuba mata idanu ya yi sosai, ita kuma ta É—aure fuska tamau tana wani basarwa ta nufi waje. Har zata fita ta tsinkayo voice É—insa a sanyaye sosai yana faÉ—in. "Ina zaki je kuma?". Tamkar ba da ita yake yi ba, ta wuce abinta bata amsa ba.

Wani irin yawu mai karfi ya haÉ—iye sai da makogwaransa ta yi sama ta sake yin kasa, har sautin haÉ—iyar yawun sai ka ji, tamkar ba lafiya ba!.

Kasa ta sauko, su mom suna nan a zaune yacce ta barsu. Ba tare da ta É—ago ta kallesu ba ta karisa gaban mom, cikin girmamawa ta mika mata hannu a kan ta bata baby Ahmad zata je ta yi mashi wanka!.

Wani irin mugun kallo mom ta bita da shi, matar nan babu kunya bare tsoron ALLAH a ranta wai bata son Khadijah ta taɓa mata jika, yau ga ikon ALLAH, uwa da ɗanta wai ba za'a bata shi ba, har da wani cewa da ga yau ba zai sake shan nonon Khadijah ba, wanda ya sha a baya ma bata yafe ba da Khadijah ta shayar da shi, shi ba kalar Khadija bane, dan haka yanzu madara zai cigaba da sha. Abin dai is like mom bata da cikakken hankali, yo idan ba rashin hankali ba saboda kin tsani Khadijah sai ki ce yaro ba zai sha nono uwarsa ba? Haka ake rayuwa? Karfi da ya ji zaki raba shi da uwarsa saboda ke gaki uwar mugaye!.

Siririn tsaki ciki-ciki Khadijah ta ja yanda ba za su jita ba kafin ta ce. "Mom bana son irin wannan wasa, and sauri nike yi, ina son kwanciya in huta gajiyar wahalar da ni da ɗanki ya yi na kawoni nan". Ta kai karshen maganar tare da sanya hannu ta karɓi baby Ahmad da ɗan karfi. Wato Khadijah ta karo walaƙanci, sai ta nuna tamkar bata san nufin mom ba, ta mayar da abin wasa kawai ta karɓi ɗanta...... AKWAI CASE A WANNAN GIDA!!.

Sake baki cike da mamaki mom ta yi tana kallonta, amma bata tanka mata ko ta yi ƙoƙarin kwace Ahmad daga gareta ba, saboda Bobo yana nan, ta kuma san halinsa, idan ya birkice masu ko mahaukacin zaki albarka, baya ji baya gani in ransa ya ɓaci, and tasan irin balai'n son da yake yi wa Khadijah, a kanta zai iya yin komai, lokacin da ta ɓata haukace masu ne kawai bai yi ba, dik wani security na gidan sai da ya ɗanɗani azaba, shi kenan kullum yana zarya a tsakanin Nigeria da Paris dan nemanta, ya rasa dik wani sukuninsa, har ciwo ya kwanta, dan haka tasan komai, ta kuskura ta yi wa Khadijah wani abin yana nan asirinta ne zai tuno, Bobo zai gane ita ta sanya aka mayar da Khadijah Nigeria, dan haka gara ta ja bakinta ta datse har zuwa lokacin da Bobo zai fita ya basu waje.

Ita dai Khadijah upstairs ta nufa da baby Ahmad dake ta zuba barcin. Da ido su Pinkish suka bita da kallo, suna son É—aukar Ahmad amma suna shakkar mom, sai suka yi jugum-jugum.

Lokacin da ta dawo É—akin Bobo ya shiga wanka, hakan yasa ta shinfiÉ—esa a saman katafaren bed É—insu ta wuce izuwa wajen closet É—insu. Manya-manyan towels guda biyu masu laushi farare tas ta É—auko, ta dawo cikin room É—in, a kusa da baby Ahmad ta kwanta tana daka hamma, barci sosai take ji. Jiransa take yi ya fito sai ta yi wa baby Ahmad wanka su ji daÉ—in yin barci.

After 25 mins da kwanciyarta sai ga shi ya fito sanye da wani bathrobe É—in, fari kal tamkar wanda ta sanya É—azun, a lokacin barci ya yi awon gaba da ita. Bai lura da ita a saman bed É—in ba, da yake bedroom É—in yana da girma sosai, toilet na da nisa da in da bed yake. Closet ya nufa dan shiryawa.

Jim kaÉ—an ya fito sanye da hoodies milk color a jikinsa, saboda sanyin da ake yi, ya yi bala'in kyau a cikin kayan, ya zura hannunsa a cikin aljihun wandan kayan, sannan ya sanya hular hoodie É—in a kansa, sai tashin fitinannen kamshi yake yi. Tsakiyar room É—in ya tsaya, tin da ya kyalla ya ganta shinfiÉ—e a saman bed É—insa ya kafeta da kallo babu ko kyaftawa.

A hankali ya taka zuwa wajen bedside drawer, a natse ya zauna a wajen idanunsa gabaɗaya a kan shape ɗinta, ga shi irin kwanciyar da ta yi a miƙe hakan ya baiwa komai damar bayyana, barcin unexpect ne ya ɗauketa. Wani irin yawu ya haɗiye har sai da makogwaransa ya harba, ya yi sama ya kuma yin ƙasa.

ÆŠan limshe idanunsa ya yi, almost one year ake nema yanzu rabonsa da ya jita a jikinsa, gaskiya ya yi kewa kuma ya yi hakuri da juriya. ÆŠan rankwafowa kanta ya yi kamar zai haÉ—e fuskokinsu, sai kuma ya tsura mata idanu yana mai cigaba da haÉ—iyar yawu.

Da yake barcinta bai yi wani nauyi ba sai ta ji saukar numfashinsa a saitin in da tata yake fita, hakan yasa numfashinsu ya gauraya, tana shakar nasa shi ma yana shakar tata. Jin hakan yasa ta waro idanunta waje a razane. Ai tana ganinsa a miliyan ta yunƙura zata miƙe tana wani ɗaure fuska.

Cikin zafa yasa hannunsa ya mai da ita dole ta kwanta, ba don ya yi niyar hayewa kanta ba ya miƙe ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa, sai ya haɗe hannayenta dikka biyu ya rike da hannunsa ɗaya bayan ya mayar da hannayen nasa ta saman kanta.

Ai a fusace ta ce mashi. "Ni ka sakeni, kuma kada ka sake taɓani!". Tana magana tana ƙoƙarin fisge kanta daga garesa haɗe da binsa da wani mugun kallo......... Ɗan bakinta ya bi da kallo, idanunsa ne suke kara rikiɗewa sosai izuwa jajir tamkar wuta, murya tamkar wanda yake a cikin maye ya ce. "My wife, why are you avoiding me? Don't you know that i love?". Yadda ya yi maganar sai ka zaci ba shi ya yi ta ba.
Chapter 6 · 0% Book details