← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 130

Sashe 34

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangarensa kuwa, tana furta wannan kalma wani irin juya mashi da kansa ya yi sai da ya ji tamkar an rotsa mashi glass a jiki, tsananta jijjiga daga ciki jikinsa ya yi, daga waje kuma wani irin tsuma ya fara yi, take jikinsa ta haɗa wata uban gumi mai rikitarwa, idanunsa suka kaɗa jajir tamkar wuta, tsabar jijjigar da yake yi ta ciki har yasa hannayensa suka fara kerma ya shiga daddanna laptop ɗin da karfi-karfi tamkar zai fashe glass dake wajen keyboard ɗin, dan irin laptop ɗin nan ne mai full screen wanda kai da kanka zaka fidda keyboard ɗinsa ka kuma lankwasa laptop ɗin gida biyu.

Bata lura da halin da ya shiga ba, sai ta sake cewa. "Musulunci akwai daÉ—i sosai...... Kuma zai taimaka maka..... Sannan zaka.......".

Maganar da bata iya ƙarisawa ba, cikin wani irin azama ta ja wata uwar birki game da haɗiye sauran maganar, ba komai ya ja hakan ba kuma face yadda ya ɗago da kallonsa yana zaro mata idanu. Kafin ta yi wani yunkuri ya daka wata uwar tsawa da wata murya ta daban wadda bata taɓa jinsa da irinsa ba. Bata farga ba sai gani ta yi ya yi watsi da table dake a gabansa, ya yi jifa da laptop dake hannunsa ta faɗi ƙasa ta yi watsa-watsa, lokaci guda dogon gashin kansa ya warware tamkar wanda aka sanya hannu aka warware mashi, haka ta tarwatse ta watso mashi har ta gaban fuskarsa, gabaɗaya ilahirin jikinsa wani irin jijjiga yake yi, yadda kuka san wani shaiɗanin aljani haka ya rikiɗe lokaci guda. TO FA DAGA MAGANAR MUSULUNCI?!.

Cikin wata iriyar dakakkiyar muryar dake bada amo tana amsakuwa mai razana zuciya ta rikita ƙwaƙwalwa ya ce. "Ke karamar halitta!! Kin jima kina tsallaka iyakarki muna zuba maki idanu saboda muhimmancin da ya baki a cikin zuciyarsa, ki sani yau you have been cross ur line know, babu wanda zai iya kuɓutar dake daga hannunmu a yanzu!!".

Tsabar zaranar da ita da wannan murya ya yi ai bata san lokacin da ta kai hannayenta ta datse kunnuwanta dan ƙwaƙwalwarta ba zai iya ɗaukar wannan murya ba, karfi da amonsa zai iya hautata, ga shi yana bada wani irin amsakuwa.

Take Big Bro ya rikiɗe ya zama tamkar wani bujumin zaki mai firgitarwa, cikin wata iriyar zafa da jijjigar da jikinsa ke yi yasa kafa ya take sofar da take a kai, bata san ya aka yi ta miƙe tsaye ba, shi kuwa sofar ya gangara can nesa. Dogayen hannunsa yasa ya capki wuyarta da karfin gaske, ji kake yi kas-kas-kas kasusuwan yatsun hannunsa suna wani irin amsawa.

Lamarin ya girmewa shekarunta, ai bata san time da ta saki fitsari a wajen ba, saboda azaba, jikinsa tamkar wani nau'i na wuta mai azaba ne, tsabar zafin da yake a jikinsa kawai ya isheta azabtar da ita ba sai ya haɗa mata da shaƙa ba, ga nails na yatsunsa wasu dogaye da su, bata taɓa shiga bala'i irin na yau ba, gabaɗaya kanta har juyewa yake yi tana ganin wani irin duhu-duhu mai ɗauke da hayaniyar wasu abubuwa dake gilma mata. DIKKA WANNAN FA SABODA TAYIN YA SHIGA MUSULUNCI NE KAWAI YA YI WANNAN BIRKICEWAR!! BABBAR MAGANA!.

Cikin wata iriyar zafa ya fara taku mai amon amsakuwa, dik in ya taka sai kasa ta amsa, da wuyanta ya ɗaga sama ya nufi karshen wajen da ita. Gabaɗaya ta fita a hayyacinta saboda azaba, zafin dake jikin hannunsa kawai yana azabtar da fatan wuyanta, ga shaƙa da ya yi mata.

A karshen waje ya tsayar da ita, cike da tsananin tashin hankali ta kalli ƙasa da wutsiyar ido kafin ta sake kallon cikin kwayar idanunsa da suka canza daga ainahin nasa.

"Ke a su wa da zaki shiga huruminmu? Wacece ke karamar halitta?". Wannan murya dai mai amo ta sake faÉ—a, dan ba muryar Big Bro bane sam-sam.

"Wannan ruhi ba'a haliccesa dan ya zama irinku ba, ba'a haliccesa dan ya musulunta ba, dik da yake ya fito daga tsatson musulmai, amma shi ba irinku bane ba! Na mu ne shi! Ba kuma zai taɓa kasancewa kamarku ko naku ba har abada!!". Ya sake faɗa cikin ɗaga murya. Lokaci guda ta ga face ɗinsa ya canza, fuskar wani mutum kyakkyawan gaske tamkar wani rafani ya bayyana a kan nasa fuskar, ya yi wani irin canzawar da ba zaka taɓa ganewa ba! Dik da bata a cikin hayyacinta sosai, ba shakka ta taɓa kallon wannan fuska da ta bayyana a kan nasa yanzu, bata da natsuwar da zata iya tinanin a ina ta taɓa kallan fuskar, amma ba shakka ta taɓa kuma a kurkusa ma kuwa.

Slowly idanunta suka fara rufewa tamkar ranta na barin jikinta, ta dai'na jiyo sautin komai a cikin kanta. "Babu wani mahaluki a duniya da ya isa ya canza mana dokoki ya zauna lafiya! Kin shiga huruminmu dayawa! Kin mana ɓarnar da zamu ɗauki lokaci kafin mu gyara cikin ƙanƙanin lokaci da bayyanarki, kin rusa mana dayawa daga cikin burikanmu! Harke wacece?!!!!". Ya faɗa da karfi tare da wujijjigata tamkar yana karkaɗa leda. Ina idanunta sun rigada sun gamasa rufuwa ruf, sai dai har lokacin tana breathing.

"Yanzu lokacinki ne na ɗanɗanar kuɗarki! Dole ki karɓi hukuncin ɓarnar da kika yi mana!!". Ya sake faɗa tare da kara jijjigata da wani irin karfi na fitar hayyaci, sannan ya sake wuyarta tare da riƙo kafarta da hannu ɗaya, ya juyata kanta a kasa ƙafafunta a sama, cikin wata iriyar bakar mugunta ya sake jijjigata zai wurgata kasa kenan daga bayansa aka rike hannayensa dikka biyu, sannan aka juyo da shi.
Wasu jiga-jigan robot ne daga cikin ma'aikatansa, Smart ya basu umarnin su karɓi Sweetie daga hannunsa.

Tun lokacin da Black Tiger ya daka tsawar farko Smart ya ji shi, hakan yasa ya hauro saman, ganin abin da yake faruwa ya sanya shi komawa ya zaɓo robot manya guda biyu game da basu umarnin su karɓi Sweetie daga hannunsa, dan a yadda yaga Black Tiger ya san ba shi kaɗai bane, dan haka zamar lafiya ta fi zama ɗan sarki, gwara mashi ya sanya robot da ya je Black Tiger ya kakkarya mashi kasusuwan jiki.........😅

Cikin wani irin fusata Big Bro ya juyo da idanunsa a kansu, da yake fuskarsa ta sauya robot basu ganesa ba, kai tsaye suka ɓanɓaro hannunsa daga riƙon da ya yi wa Sweetie, suka karɓeta. Cikin zafa Smart ya matsa ya karɓeta daga hannunsu, da gudu ya sauka da ita ƙasa.

Big Bro da bai san robot bane a lokacin, baya ji baya gani, hannu yasa da karfin gaske ya cakumo robot É—aya, da karfi ya É—agasa sama, jefa da shi gefe ya yi, to kun dai san su robot karfe ne, to me zasu ji? Ai kome Big Bro zai yi masu a banza wai an yakushi kakkausa.

Kokawa suka fara yi gadan-gadan cikin zafa, tamkar wasu mayunwatan zakunan da suka É—auki tsawon shekara babu ci babu sha yanzu suka ga abinci, gwabzawa suke tamkar na za'a mutu ba.
Sai jifa da su Big Bro yake yi suna kara miƙewa su nufosa. WANNAN SHI NE FAƊAR ALJANI DA ROBOT.

Wani irin shaƙa da robot ɗaya ya yi wa Big Bro sai da ya ji kamshin lahira, da karfi ya yi jifa da shi saman glasses dake wajen wanda Smart ya fasa cup da kuma na laptop and table da Black Tiger ɗin ya fasa. Saman glasses ɗin ya faɗa, take suka sossoke mashi damatsan hannu jininsa ya fara koranya.

Dai'dai lokacin Smart ya hauro wajen, ya kai Sweetie wajen Ronnie a É—akin su, ya kuma gargaÉ—esu a kan kada su fito, shi ne ya dawo domin ya kwantar da wannan tarzoma, dan ya san waÉ—an nan robot idan bai dakatar da su ba zasu iya hallaka Big Bro.

Cikin wata iriyar zafa Big Bro ya miƙe yana wani irin huci tamkar zai kama da wuta. Robot ɗin ne suka nufesa a tare da nufin su takeshi su jefasa kasan benen, dan a tinaninsu mugu ne zai yi zalunci kashe shi zasu yi.

Gab zasu taɓa shi Smart ya ce masu a'a bai yarda ba, cike da bada umarni ya ce su ɗaure mashi shi dai, kada su kuskura su sake taɓa lafiyar jikinsa. Cikin girmamawa suka karɓi umarnin, sannan suka amsa da okey. Da sauri Smart ya ɗauko masu sarka suka ɗaure shi, amma fa da kyar suka iya ɗaure shi ɗin, sai da suka sha fama.

Umarnin Smart ya yi masu da su kai mashi shi bedroom ɗinsa, haka kuwa suka yi, suka kwashesa sai cikin bedroom ɗin bayan sun ɗauresa, a saman bed suka kwantar da shi. Gefensa Smart ya zauna yana kallan cikin idanun ɗan uwan nasa, lokaci guda wani irin mugun tausayi ya kama shi, bai taɓa jin tausayin wani abu kamar yadda ya ji tausayin Big Bro a yanzu ba.

Shiru Big Bro ya yi tamkar abubuwan sun lafa mashi, sai dai kuma ga wanda ya san idanunsa zai fahimci sam basu lafa mashi ba, domin kuwa idanunsa ba su koma dai'dai ba.

Lokaci guda Smart ya tsinci kansa da tinanin bari ya tofa mashi addu'oi ko za'a sami sassauci. Hakan kuwa aka yi, a hankali ya fara karanto ayoyi goma na farkon suratul baƙara, kun san dik shaiɗancin shaiɗani yana mugun shakka da tsoron suratul baƙara da yaseen.

A cikin zuciya Smart ya fara karantowa har ya kai karshe. Slowly ya ɗan matsa dab da Big Bro ya fara tofa mashi. Ai yana tofa na farko wani irin jijjiga da Big Bro ya fara yi, take wasu irin hasumiya na wasu muryoyi kala daban-daban suka fara tashi a cikin ɗakin, tamkar bed nasa zai ɓaɓɓalle haka ya fara yi, yana wani irin daddamke jikinsa yadda kuka san ana cizgar namar jikin nasa ne, gabaɗaya jijiyoyinsa sun mimmiƙe sun fito raɗo-raɗo, idanunsa ya koma bakinkirin babu ɗigon fari a ciki, ga wasu jijiyoyi da suka shararo mashi a gaban goshinsa, yadda kuka san ana zare ran bakin shaiɗani.
Chapter 34 · 0% Book details