Sashe 62
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ya girgiza kai alamar babu, yanzu yagama tabbatarwa ba mafarki bane, dan idan a mafarki ne wlh Omaid ba zai ji a jikinsa ba, dole zahiriya ce, dik abin da Omaid ya faɗa halin da ya tsinci kansa a daren jiya kenan, ya ji tsoro kuma zuciyarsa ta yi ta bugawa da sauri-sauri, lallai wani ne ya yi mashi wannan abin, to waye? Ya jefi kansa da tambayar da babu mai amsa mashi. NI KAM NA CE GASKIYA YARAN MOMMAH GIFTED ƊIN NE DA GASKE, KUNGA WATA BASIRA! HAR YA GANO BA MAFARKI BANE! MAHREEN ALLAH YA CECEKI, DAN WLH IDAN OBAID YA KAFA RANSA A KAN BINCIKE CIKIN ƘANƘANIN LOKACI ZAI GANOKI, UHM NA DAI YI SHIRU!.
Ganin ya yi shiru ne yasa Omaid ya fara binsa da kallon tsab. "Ya kamar baka yi sallar asuba ba? Kamar yanzu ka tashi ko?". Cewar Omaid, saboda ya ga É—an uwan nasa gabaÉ—aya a hargitse.
Kwarai yanzu ya farfaÉ—o daga suman, fitsarin da ta yi a jikinsa ma har ta bushe kamar bai yi ba, shiyasa ma bai san ya yi ba.
"Yanzu na tashi, barcin yau ta yi nauyi dayawa, amma kai ma ya kamar ba a nan ka kwana ba?".
Jinjina kai Omaid ya yi. "Ba'a nan na kwana ba, almost 4 na asuba ina garden, da na fito na wuce masjid, daga nan na wuce room na mommah na kwanta sai yanzu na tashi ne nike samun labarin Aunty Sareena bata da lafiya, shi ne na zo in yi wanka mu je dubata".
Ɗan yarse ne fuska ya yi kafin ya ce. "Meyasamu Aunty Sareena ɗin?". Omaid yana miƙewa tsaye ya ce. "Gaskiya ban sani ba, amma bari in yi wanka sai mu je mu gani".
Da sauri Obaid ma ya miƙe yana faɗin. "Sai dai mu yi wankar tare, dan ba zan iya jiranka ba". Uhm kuruciya za'a kirasa ne ko tsananin kaunar juna? A tare dai suka shiga toilet ɗin suka yi wanka, suka kuma fito a tare, suka shirya cikin shiga iri ɗaya, sannan Obaid ya tada sallah dan biyan asuba ɗinsa. Shi kuma Omaid ya haye saman bed dan ya jirasa.
Bayan ya kammala suka tafi a tare zuwa side ɗin uncle Abbas. A can ɓangaren kuma Mahreen tsantsara shigarta ta yi cikin wandon jeans baki da riga long sleeve fara, ta ɗaura jacket mai girma zuwa gwiwarta kasancewar ana sanyi, ta sanya hular jacket ɗin a kanta, ta yi masifar kyau kam over to over.
Ta fito ta nufi room ɗin Mahnoor, dama ita take jira, tana zuwa ta ce su tafi. Fitowa suka yi, suka sauko parlon kasa zasu fita kenan suna ci karo da guyson da ya fito daga ɓangaren king. Cikin sanyin murya sosai fiye da ko yaushe ya ce. "Ina kwana Aunty Mahnoor".
Fuska a É—auke da murmushi ta amsa mashi da. "Lafiya lou Yah Omar ka kwana lafiya". Alhamdulillah ya amsa mata da shi kafin ya mai da kallonsa a kan Mahreen da ta tsaresa da kallo, a ranta ta ce shi dai yana son farar jallabiya, kuma tana yi mashi mugun kyau.
Nufar waje Mahnoor ta yi tana faÉ—in. "Mahreen baki iya gaisuwa bane ko?". Tana turo baki ta rufa mata baya kafin ta ce. "Kanin nawa zai gaisar? Shi yakamata ya gaidani tin da ni auntynsa ce, yaro ne fa karami....."
Bata idasa rufe baki ba ya kai hannu ya damko hannunta, take yanayinsa ya canza, ya ɗaure fuska tamkar bai taɓa yin dariya ba. Daidai lokacin Mahnoor ta juyo zata yi mata faɗa, ai tana ganin ya damketa tasa kai ta yi waje abinta, addu'a ma take ALLAH yasa ko marika biyu lafiyayyu ya sakar mata kila ta dawo daidai, ina ba iskanci ba mutum ya baki almost 7 years ki ce wai yaro ne ƙaramin kaninki, hmmmm.
Dakatawa ya yi sai da Mahnoor ta fita sannan ya ce. "Mekika ce?". Yadda ya yi magana a Omar É—insa ya yi ta ba guyson ba. Dik da taga babu wasa a tattare da shi hakan bai hana mata ta ce. "Kai yaro ne na ce, ba zan gaisheka ba sai dai ka gaisheni".
Haba wani irin kululun bakinciki ne ya tsaya mashi a maƙoshinsa, tin da take ce mashi kaninta bai taɓa damuwa ba, amma yau da ta kirasa da yaro abin ya yi balain bakanta mashi rai, wai yaro, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, gaskiya ta kure hakurinsa yau, tinani ya shiga yi a kan me zai yi wa yarinyar nan ta san cewa akwai banbanci, wlh har wani ja idanunsa suka yi alamar ransa ta ɓaci sosai.
Daidai lokacin Jaish ya shigo parlon bakinsa a É—auke da sallama, hakan yasa guyson ya saketa tare da juyo da kallonsa a kan yayan nasa. Da gudu ta yi waje tana faÉ—in. "Saboda na ce maka yaro shi ne kake haÉ—e rai? To na faÉ—a yaro ne kai karami ma kuwa wanda baka wuce in goyaka ba".
Haba ai wani irin yawu ya haÉ—iye wanda har sai da Jaish ya ji sautin haÉ—iyar, ido cikin ido suka kalli juna da Jaish na Æ´an sakanni kafin Jaish ya ce mashi. "Ka yi hakuri".
Shiru bai amsa ba, yana dai kallonsa bai kawar da ido ba. Matsawa dab da shi Jaish ya yi tare da riko hannunsa da nufin ya yi mashi magana kawai sai gani ya yi guyson ya sake mashi jiki gabaÉ—aya ya yi.......
Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...âœï¸ðŸ”¥ðŸ•Šï¸
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
-------------------------------------------🔥♥ï¸
ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥
Shiru bai amsa ba, yana dai kallonsa bai kawar da ido ba. Matsawa dab da shi Jaish ya yi tare da riko hannunsa da nufin ya yi mashi magana kawai sai gani ya yi guyson ya sake mashi jiki gabaɗaya ya yi ƙasa zai kwanta Jaish ya yi zafan rikosa da kyau yana kallon fuskarsa da yadda ya fito da tongue ɗinsa waje ya datseta da hakwaransa tamkar zai cire harshen nasa.
Nisawa Jaish ya yi kafin a fili ya ce. "Babbar magana, aiki ya dawo baya". Ya faɗa tare da gyarawa da kyau, ya ɗan duka ya saɓi guyson a saman shoulder ɗinsa ya juya da shi izuwa part na mommah.
Tana zaune a saman wannan shinfiÉ—a tata ta manyan Æ´aÆ´an sarakuna kuma gimbiyoyi da ake ji da su kuyangarta dake yi mata hidima bayan tafiyar Mama Haulat ta shigo bakinta a É—auke da sallama. A natse momma ta amsa mata, ta haÉ—e cikin wani dandatsetsen alkyabbarta mai balain kyau da É—aukar ido.
A gabanta kuyanga Salma ta tsugunna tare da neman izinin yin magana. Go ahead momma ta bata tana mai binta da kallo, muryarta na É—an rawa ta ce. "Prince Jaish ne yake neman iso cikin gaggawa".
Kallan hakan ta fuskar basira Momma ta yi kafin ta ce. "Yi mashi iso". Ta faÉ—a a cakin ranta tana fatan ALLAH UBANGIJI yasa lafiya, dan yadda ta ga Salma take zazzare ido da wuya idan ba wani tashin hankalin ta gani ba.
Da sauri Salma ta tashi ta nufi waje har kamar zata kifa. Tsaye ta isko Jaish kamar yadda ta barshi bai motsa ba, a gabansa ta zube gwiwowinta kafin ta ce. "Tanai maku iso". Ai yana jin haka bai tsaya bi ta kanta ba ya yi gaggawar raɓata ya wuce ciki. Bakinsa a ɗauke da sallama ya shigo ciki, momma na ganinsa ɗauke da guyson bata san lokacin da ta miƙe tsaye tana faɗin. "Jaish lafiya kuwa?".
Bai yi magana ba har sai da ya kwantar da shi flat a saman lallausan shifiɗar tata, sannan ne ya ɗago da kansa ya kalleta, a natse ya ce. "Ba lafiya ba, i think Omar ya koma Omar ɗinsa na ainahi ne, ɓata mashi rai aka yi ya yanke jiki ya faɗi, ga shi ya datse harshen nan nasa da yake yi a baya".
Zazzaro ido momma ta yi a kan fuskar guyson, yana datse da harshensa a waje ya sume, take harshen tasa ta yi jajir tamkar jini ya taru a cikinsa. Kun san akwai mutane masu irin wannan ɗabi'a ta zafin zuciyar, idan zuciya tai masu yawa ko duka zasu yi sai sun fito da harshe waje su datse da hakwara da karfi, so dazarar anga sun fito da harshe waje sun datse da hakwara ma za'a gujesu saboda an san bakar zuciyar ta motsa zasu yi mugunta ne. Guyson yana da balain zuciya fiye da yadda kuke tunani, ga shi da saurin hawa, baya sauƙa ta daɗi, sannan in ransa ta ɓaci fita yake out of control, a wannan point ɗin zai iya aikata komai ba tare da ya sani ba, sai zuciyar ta sauka yake iya fahimtar ya yi kuskure.
Zuciyar Omar sak na Big Bro, basu da wata banbanci, dan dai shi yaro ne kawai, sannan shi É—aya ne ba su Æ´an biyu ba, kun san Æ´an biyu nasu ya fi tsanani. Tun guyson yana da shekaru biyar a duniya kakansa mahaifin momma, wato Husaini Akka King Badeen kenan, ya fahimci guyson mutum ne mai bakar zuciya sosai, baya da tsokana, amma ida ka shiga gonarsa zaka yi danasanin zuwanka duniya, ya fita daban da sauran yara, silent yake, da King Badeen ya fahimci hakan sai ya sanar da Momma cewa dik cikin Æ´aÆ´anta babu mai irin zuciyar wannan yaron, kun san dik shi ya renesu ban da Smart da Big Bro, so yasan halinsu Omaid dikka.