← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 130

Sashe 16

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunta Ronnie ya riko suka nufi waje dan su je ya bata abinci. Ita kuma Sweetie ta cigaba da shiryawa tana tinanin yacce zata dakatar da su daga yin wannan party na dare da zasu yi dan nuna alhini da koke-koke a kan mutuwar mahaifin Black Tiger, dole ta dakatar da hakan ta koya masu cewa addu'a ake yi wa wanda ya mutu ba wai a shirya party sai an ci an sha sannan ayi koke-koke na ƴan awanni daga nan a sha giya a bugu a hau tikar rawa, mata da maza suna zinace-zinace a bainar nasi, maza da maza suna liyawa wato luwaɗi mata da mata suna les, dole ta dakatar da wannan babbar ɓarna, to amma ta yaya zata faro? Wannan shi ne tinanin da ya tsaya a ranta tin kwanaki uku da suka wuce. ME KUKE TINANIN ZAI FARU A WANNAN RANA?.

PARIS.🔥

Lokaci da Khadijah ta farka da safe bata sami Bobo a room ɗin ba, miƙewa ta yi ta shige cikin toilet, wanka ta fara yi kafin ta yi wa baby Ahmad, ta tsara mashi kwalliya cikin ɗaya daga cikin kayan da daddynsa ya saya mashi.

Ya yi matuƙar kyau sosai tamkar ka sace shi ka gudu da shi. Da kanta ta gyare ɗakinta tsab, ta zuba perfume na ɗaki kala daban-daban masu daɗin kamshi, ita ma cikin ɗaya daga cikin kayan da Bobo ya saya mata jiya ta shirya, wani kafurin crazy ne wanda ya yi matuƙar fito da surarta, cinyoyinta tamkar zasu fasa wandan, ga shi cinyoyin wandon dik a ɗan tsastsage kana ganin kyakkyawar lallausan fatar santala-santalan cinyoyinta, sai wani kara glowing yarinyar nan take yi abinta, tana tafiya tana juya mazaunai suna kara rikita hankalin Bobo!

Bayan sun shirya tsab sai tashin kamshi suke yi ne ta saɓo baby Ahmad a saman shoulder ɗinta ta nufo waje, fuskarta a ɗaure tamau alamar babu mutunci, yau ta ci alwashin tambayarsa wani irin zama suke yi, shin zaman aure ne ko na zina dan ma ta san a wani matsayi take!.

Kasa ta sauko, nan ta isko mom zaune saman sofa tana shan green tea. Ba tare da ta kalli in da take ba ta ce. "Good morning". Ta yi maganar tana nufar waje gabaÉ—aya.

Ai mamaki tamkar mom zata natse cikin ƙasa, sai ta rasa bakin magana, wai Khadijah ce yau ko kallon in da take bata yi ba? Kai abin da mamaki gaskiya, yarinyar da dik abin da za'ayi mata bata fasa ladabi da biyayya, har kasa fa da take tsugunawa gaida mom, ni ko na ce kece baki san ya fushin mai hakuri yake ba, ai tama yi maki da sauki dan akwai ɓirɓishin soyayyan ɗanki a ranta, ba dan haka ba zaki yabawa aya zakinta ne, ki godewa ALLAH ma ba da Zee aka zo ba, da kin gane Annabi Isa ba ɗan ALLAH bane Manzon ALLAH ne!.

"Ke zo nan". Mom ta faÉ—a a gadarance. Ba musu Khadijah ta juyo ta zo, dan uwa uwa ce ko a ya take, kuma dik lalacewar uwarka idan aka yi mata ba daÉ—i har cikin ranka ba zaka ji daÉ—i ba.

A saman sofa Khadija ta zauna don nuna mata girmamawa, bata tsaya a kanta ba. "Gani nan mom, oh ko da yake last time kin ce ke ba mom É—ita bace kada na sake kiranki da mom, to sorry for that, ya sunan da kike son in kiraki da shi?".

Bala'in can, ai mom kusan rasa abin faɗe ta yi, eyeeeee lallai Khadija ta zo da walaƙancin da ya sha gaban tinaninta, to dama mu Nigeria ai kada mutum ya so ganin fuskarmu ta walaƙanci, dan ba zata yi mashi kyau ba, a ganmu dai a mutumcin da muka fi shahara!.

"Miƙo mun ɗan nan ki tashi ki bani waje". Mom ta faɗa saboda rashin abin faɗe, dama ta kirata ne dan ta ci mutumcinta, to sai taga babu fuska, ba Khadijah ɗin da ta sani a baya bane.

Miƙewa Khadijah ta yi. "Wannan shi ne dalilinki na mun kiran ƴan tasha?". Ta faɗa tana ɗan sauko da baby Ahmad. Mom bata amsata ba, ta dai bita da kallo. "Baki buƙatar yi mun kiran ƴan tasha ko kiran nuna iko a kan Ahmad tin da kinga ke ba mom ɗita bace kamar yacce kika faɗa, dan haka ba zaki nuna mun iko ba, and ni ba zan hanaki Ahmad ba, saboda jininki ne kuma first jikanki kenan a duniya da bashi da madadin". BALA'I MAGANA FA KHADIJAH TA FAƊA MATA, WATO KO ZATA MUTU KO ZATA YI RAI AHMAD DAI FIRST JIKANTA NE DA DIK WANDA ZAI ZO DAGA BAYA MA SAI DAI YA BIYO BAYANSA, E LALLAI KHADIJA TA KARO WALAƘANCI!

Ta kai karshen maganar tare da miƙo mata baby Ahmad. "Ga shi nan ai, dama shi ma yana son jin ɗumin jikin kakansa a dai'dai wannan lokaci, kin ga safiya ne".

Ai mom ji ta yi tamkar kada ta karɓesa, saboda wani irin kululun bakinciki da ya taso mata, ƙoƙarin cusawa kanta tsanar Ahmad ta yi, sai dai ta manta bawa baya ɗaurawa kansa soyayya ko kiyayya, dan haka baby Ahmad jininta ne so dole!.

A kufule ta kai hannu ta fisgo Ahmad da karfi, a hanzarce Khadijah ta sake mata shi tana faɗin. "Ba fa sai kin saka karfi ba, kowa ya gansa ya san jikanki ne, saboda dake ma yake kama, kunga no need ki nuna power wajen karɓarsa, dan dole a baki kayanki". Tashin sense, magana cikin magana kenan, mom ta shaki takaicin wannan ma, dan ta rama sai ta ce.

"Sunan jikana ba Ahmad ba ne, sunansa Alex, ba zai taɓa zama musulmi mugun iri kuma ƴan'tadda ba". Cike da nuna isa ta yi maganar, wai dan ta shakawa Khadija takaici.

Sai dai ko kaÉ—an Khadija bata nuna ta damu ba, dik da tana tsoron hakan ya kasance, dan tasan mom zata iya rabata da Ahmad kuma ta mayar da shi krista, amma bata nuna kamar ta ji wani abin ba, muryarta a ware sosai ta ce. "To ai wannan ba wani abin bane, zaki iya saka mashi dik sunan da kika yi niyya, bakina kuma bakina ne baki isa ki umarcesa da sunan da kike so ya kira ba, ki kirasa a Alex ni kuma Ahmad, kin ga ai ba komai ko?".

Sosai mom ta ji bakincikin yacce Khadija bata ji haushi ba, dan haka sai ta ce. "Ba zai taɓa yin musulunci ba idan ina da rai"...... Siririn murmushi wanda ya fi kuka ciwo Khadija ta saki, sannan ta nufi hanyar barin parlon tana faɗin. "Ai ba wani abin bane, kada ki damu, ba dai kin yarda ɗan da ya kwanta cikin musulma kuma bakar fata jikanki bane? Kuma kin yarda ubansa yana tare da musulma! To ai dik abin da zai biyo baya nafila ne". WATO SAI MAI BASIRA ZAI GANE KALAMAN KHADIJA, BAKA KIRIN TA GASAWA MOM.

Ta kai karshen maganar tana ficewa waje abinta, burinta ta sanya mom ta fara ja baya da ɗaukan mata yaro, kuma da alama zata yi nasara, domin mom ta ji tsananin bakinciki na kalamanta na karshe cewa Ahmad ya kwanta cikin musulma kuma har ma ya sha nononta, dan haka sai ta dakawa Khadija tsawa a kan ya zo ta ɗaukesa ko kuma ranta ya ɓaci.

Wani irin Musulmin daɗi ne ya lulluɓe Khadijah, dama ta yi mashi wanka ne domin ta kaisa ga daddynsa su gaisa sai ta samu damar tambayarsa wani irin zama suke yi, dan haka ranta ya yi fari tas da mom ta ce ta zo ta karɓesa. Da sauri ta juyo ta dawo, tana zuwa tasa hannu ta karɓesa, da ɗan karfi mon ta dungura mata shi. Bata damu ba ta karɓesa ta wuce waje.

Kai tsaye garden na gidan ta nufa, dan tasan Bobo yana wajen, bawan ALLAH damuwa ce ta yi mashi yawa ya koma can ya zauna ko zai rage abin da yake ji. Ƙasa ƙasa ta yi sallama kafin ta shigo. Yana zaune saman ɗaya daga cikin lutsuma-luntsuman sofa's dake wajen karkashin wata kyakkyawar runfa ta shan iska.

Ai tin da ya hangota ya kafeta da ido tamkar ya tashi ya je ya rungumota yake ji, amma sai ya daure ya bita da kallo har ta iso shi. Sallama ta sake yi mashi, a maimakon ya amsa mata sai ya É—aure fuska sosai, cikin harsh voice ya ce. "Haka kika fito kika keta gabaÉ—aya masu aikin gidan nan kika zo nan?!". A tsawa ce ya yi maganar, kun san fa kishi a jininsu yake, jikin King Abdul Malik basa É—aga kafa fagen kishi.

Ganin yacce ya ɗaure fuska ne yasa ta sha jinin jikinta, dan tasan muguntarsa, idan ransa ya ɓaci baya duba in da yake nufa. Kasa ta yi da kai bata amsa ba. Wani irin tsawa ya daka mata wanda ya sanyata razana ta ɗan yi baya har tana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa. Miƙewa tsaye ya yi yana binta da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, ba dan yana tsananin sonta kuma yana neman sulhu ba da babu abin da zai hana bai tattakata a wajen ba.

Jikinta ne ya hau kerma, gabaÉ—aya ta ji harshenta ya yi mata mugun nauyi ta rasa bakin yin magana, takowa ya yi step biyu ya iso gabanta yana kara daka mata tsawa, take ya rikiÉ—e tamkar ba shi ba, yana wani huci.

Baya-baya ta fara ja tana ɗan girgiza mashi kai. Cigaba ya yi da takowa yana dalla mata wani irin kallo mai kama da harara yana jiran ta bashi amsa. A haka har suka kure wall ɗin wajen, tsayuwa ta yi tana tsuru-tsuru da eyes tamkar an tare ɓera a tarko.

Hannunsa É—aya yasa ya dafa wall dake bayanta, da yake ya É—an fita tsawo sai ya É—an rankwafo kanta. "Ba zaki amsa mun ba sai na yi ball dake?". Ya faÉ—a babu alamar wasa a tattare da shi!.
Chapter 16 · 0% Book details