Sashe 65
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kai yaro tsaya in faɗa maka, ni ba matar yara bace, mata manya ce irin masu shekaru 30 haka, kamar dai su Yah Jaish ɗin nan ko uncle Taheer nike so ba irinka karun yar..........". Ai bata karisar da maganar ba wani zazzafar mari ya wanke mata fuska wanda yasata dole ta haɗiyi sauran maganganun da ta yi niyar faɗa, lokaci guda ya shiga huci tamkar zai kama da wuta, ransa ta yi mugun ɓaci da ta ce mashi irinsu Uncle Taheer take so, sai ya ji tamkar ta watsa mashi wuta a zuciya, ai gani yake yi ma dama suna soyayya da uncle Taheer, take kishin nasu ta gado ta motsa tasa ya rasa control ɗinsa.
Amma da yake yana da raunin zuciya sai kuma tausayinta ya yi gaggawar kama shi, take ya yi danasanin abin da ya yi mata, muryarsa na sarkafewa ya ce. "Please Mahreen kada ki É—auki hakan matsayin cin mutunci, kiyi hakuri kin ji?".
Haba ta ji hannun maza ba wanda ta saba ji a kauyensu ba, har ɗauke wuta ta ɗan yi na wucin gadin kafin kuma ta dawo, tana dawowa ta fasa mashi ihu mai rikita dodan kunne, da gudu ta raɓa gefensa zata wuce ta fita, wai zata kai karansa wajen momma da Jaish.
Cikin zafa ya rikota tare da cewa. "Baki da hankali ne zaki fita a haka?". Ya faÉ—a yana É—aure fuska kamar bashi bane mai rarrashinta a yanzu. Cikin kuka hawaye bibbiyu ta ce. "Ka sakeni mugu kawai azzalumi, jikinka ne ko nawa idan na fita a hakan?".
In a cool voice sosai ya ce. "Jikinmu ne mu biyu, dan haka ba zan bari ki fita wani ya kalle mun ke ba". Ya kai karshen maganar tare da ɗagata cak sai saman bed ya direta. Tana ƙoƙarin tirjewa ta diro kasan bed ɗin ya yi gaggawar ce mata. "Wlh kina saukowa sai na faɗawa Obaid kece kika yi mashi aika-aika ranar".
Ai tana jin haka ta sake zunduma mashi ihu mai sauti tare da komawa ta zauna kafin ta ce. "Ban yafe maka ba, ALLAH zai saka mun".
Shi dai tin da ba zata sauko ta fita haka ba ai lafiya lou ne, koma me zata ce mashi tin da ba zata fita waje ba to ta daÉ—e bata ce ba, juyawa ya yi ya nufi waje, har sai da ya kai bakin door sannan ya ce. "Ki shirya ki tsara kwalliya ki zo garden ki nuna mun kwalliyar, idan ya yi kyau zan yaba, idan kuma bai yi kyau ba zan gyara maki". Cikin zolaya ya yi maganar, ya kai karshe yana kashe mata ido É—aya.
Haba ai sake zunduma ihu ta yi tana faÉ—in. "Mugu kawai, ba zanzo garden É—in ba, kuma wlh sai na faÉ—awa Yah Jaish, sannan sonka ne na ce bana yi, bana son yaro sai manya".
Har cikin ransa ya ji zafin furucinta, bare ma idan ta ce mashi yaro wannan abin yana kona mashi rai fiye da tinanin mutum, amma saboda yasan ya yi mata laifi, ya mareta, yanzu sulhu yake nema sai ya wuce ya fita bai sake cewa uppan ba, zuciyarsa tana yi mashi zogin ya sanyata kuka, sam bai so hakan ba, to amma ya zai yi? Basa iya controlling kishinsu ne su, abin a jininsu yake, da mata da mazansu dik haka suke, sai dai fatan ALLAH ya sassauta masu zafin kishi kawai.
Yana fitowa ya nufi room ɗinsa, wanka ya je ya yi ya shirya ya nufi garden dan hutawa ya yi waya da Auta, dan ya yi kewarta daga jiya da yamma zuwa yau, a ransa yana tinanin irin tsokanar Mahreen da zai rinƙa yi yana sanyata farinciki, ya ci alwashin daga yau sun kullah kenan, ba zai barta ta sarara ba, ya rinƙa takura mata har sai ta so dolenta.
------------------------------🔥
SPECIAL TIME IN CROWN OF INJUSTICE.
Karfe 4 na yamma daidai jiragen Black Tiger suka yi landing a international airport na Tunisia, already Smart ya ce da Jaish ya turo mashi motoci da misalin karfe huɗu airport zasu ɗauki bakinsa zuwa gida, so Jaish bai je ba sai ya tura motoci jibga-jibga guda shidda su tari baƙin. Kowacce mota tana ɗauke da tambarin Kingdom of power wato tambarin zaki kenan. Da wannan tambari Smart ya ganesu, dan dik motocin sabbi ne ba waɗan da ya sani bane, kun san Big Bro a zuwansa Kingdom of Power na farko ya yi ɓarnar da yasa aka sayi sabbin abubuwa, ciki har da motocin, bayan tafiyar Smart aka sayesu.
Strange things never end in this world, Sweetie, Pretty, Ronnie suna saukowa daga jirginsu suka yi arba da kyakkyawan fuskar Big Bro a tsaye a gabansu yana fuskantarsu. GabaÉ—aya sojijin yakinsa ne suka yi mashi zobe a wajen dan bashi cikakken tsaro, kasar Tunisia ta shaida da King of Black World ya zo cikinta a karo na farko, dan wancan zuwan tasa zuwan yaki ne da ya mamayesu, wannan kuma zuwan farinciki ne yasa suka san da zuwan.
Airport ɗin nan ta cika dam da sojojin yakinsa kawai, kuma dikka mutane ne ba robot ba, bai zo da robot ba, ainahin ƴaƴan da yake kwata daga iyayensu ya horarsu a fagen yaki su suka yi mashi rakiya this time, abin da ya yi mugun tada hankalin jama'ar kasar yasa labarin ta yi gaggawar isa kunnen King Zuhair cewa sun yi bakon da basu taɓa ganin mai karfin mulki irinsa ba, dan tin daga kan jiragen da suka take ma jirginsa baya har izuwa kan kyakkyawan tsadadden jibgegen jirgin da ya ɗaukosu an san karfin iko da karfin mulki ta zo, ganinsa da ido yasa sun sha jinin jikinsu, domin kuwa sun ga yadda iko da izza suka yi mubaya'a a jininsa. Sai dai yadda suka ja mahaukan sojojin yakin da suka take mashi baya ya sha sun yi balain tsorata, mamaki sosai suke yi kan yadda dik waɗan nan jiga-jigan warriors wai ran mutum ɗaya suke karewa, basu taɓa ganin tsaro irin nasa ba gaskiya.
---------------------🔥
Kallon juna Sweetie da Smart suka yi, lokacin guda suka sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, da sauri suka karisa in da yake tsaye ya zura hannaye a cikin aljihun wandan tsaddaden three-piece suit É—in jikinsa launin white color yana binsu da kallo da waÉ—an nan sharp eyes É—in nasa masu sanya mutum shiga shakku idan ya wurga maka su, suma dai sun shiga shakku, dan kuwa sun tsargu sosai suna tinanin ko dai hukuntasu zai yi ne da yake binsu da wannan kallo.
Sai da kuma suna karasowa in a cool way sosai ya ce. "Welcome to the home my blood brother". Ya faÉ—a yana canza kallon da yake bin Smart da shi izuwa kallon tsananin kauna. Amma kuma tamkar bai ga Sweetie ba, Smart kawai yake kallo.
Hot hug Smart ya bashi cikin tsantsan farinciki over. Zaro hannayensa daga aljihunsa ya yi ya rungumi Smart da kyau yana bin Ronnie dake nufosu da kallo, shi kuma Ronnie sai kallon birnin yake yi, ya ga sabon waje.
Shiru Sweetie ta yi tana tinanin me ta yi mashi da yake fushi da ita haka, bata san hankali yake son koya mata ba, ta ya za'ayi wani ya zo daga baya ya sameta a tare da shi har ya bata shawarar su bashi wahala kuma ta yarda? Ai wlh ban yi zatan haka daga gareta ba, tare fa Smart ya zo ya gasu, so yana son koya mata rikon amana ne, dik yadda yake son Ronnie kun san zai fi son Smart a kansa, amma dik da haka da yake Ronnie ya fara sani ai iya wuta bai rage ko mai kankantar son da yake yi mashi ba, sai ma karawa da ya yi, zai yi shawara da Ronnie bai yi da Smart ba, dik saboda me? Saboda kafin ya san Smart Ronnie ya fara sani, sam bai yi tinanin bata da hankali har haka ba, shiyasa ya shareta, dan hana ganin kenan za'a iya wasa da Æ™waÆ™walwarta a bata shawara ta cutar da shi da gaske kuma ta yi accepting, wannan kuskure ne babba ta aikata wanda yakamata ta san zaman da suka yi ya fi karfin ayi saurin juya mata tinani a kansa. AMMA FA A NASA TINANIN NE YAKE GANIN HAKAN, KU FA ME KUKE TINANI? ABIN DA YA FAÆŠA GASKIYA CE KUWA? FUSHINSA A KANTA NA GASKE NE KUWA? YA YI DAIDAI DA YA YI MATA HAKAN KUWA?. TO NI MA DAI KADA KU CE INA BIN BAYANSA, AMMA BATA KYAUTA BA DA ZATA YI SAURIN KARÆAR SHAWARAR SMART KAMAR DAMA TANA JIN HAUSHINSA KO DAMA JIRAN WATA DAMA DA ZATA WAHALAR DA SHI TAKE YI, GASKIYA BIG BRO ZAMANSU YA WUCI RA YI HAKAN..🥱
Raba jikinsa da Smart ya yi ya riki hannunsa suka wuce cikin motocinsu, shi kuma Ronnie ya riki hannun Sweetie da idanunta suka ciko tab da kwallah, da kuma Pretty, suka shiga cikin motar kusa da na su Smart.
KAI MY PEOPLE'S WLH BIG BRO YANA SON SWEETIE, DAN IN WATA CE WANNAN BAKAR ZUCIYAR TASA DA YA YI MATA ILLAH, AMMA ITA SAI DAI AYI FUSHI DA ITA A SHARETA, GASKIYA DAI YA BATA MATSAYI A ZUCIYARSA, AMMA FA A NAWA TINANIN NE!.
-------------------🔥
Zaune take a saman sofa a parlon Mommah tana shan cappuccino, har wani lumshe idanu take yi, cappuccino momma ba dai daɗi ba, tana sanye da English wears, ta yafa fen karami a kanta. Daga bayanta aka zuro hannu aka karɓe cup ɗin cappuccinon, kai tsaye ya kai ɗan bakinsa ya yi sipping tare da ɗan lumshe ido.
Ai miliyan ta juyo dan ganin wanene, tana ganin guyson ne ta wani uban É—aure fuska tare da dalla mashi harara kafin ta ce. "Ba zaka fita rayuwata ba ko?".
Gera guda ya É—aga mata alamar e yana kara sipping cappuccino. "Wlh sai na faÉ—awa momma da Yah Jaish".
"Iya karfinki kenan su ai dama na sani, wai ba da safe na ce idan kin yi kwalliya ni zaki fara zuwa ki nunawa ba? Meyasa baki zo ba?".