← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 130

Sashe 38

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zazzaro idanu Zarina ta yi tamkar kwayar zasu faɗo ƙasa. Bai bata damar yin magana ba ya sake cewa. "Ai aikinki ya rigada ya kare, dama ita rayuwa ka ci amana ce kai ma a ci naka, ka yi kirki kai ma ayi maka kirki, dik abin da ka yi shi za'ayi maka, dan haka kin ci amanar Omranish, kin kashesa da hannunki yana matsayin miji a gareki wanda bai rageki da komai ba, kika ci amanarda kika kashesa, to a yanzu kema zaki ɗanɗani ɗacin da ya ji a lokacin da ya waro idanunsa ya ga ke kika ci amanarsa, yanzu kema ki waro idanunki ki ga ni Ude Ranveer Abdul mutallab ni na ci amanarki, na karɓi mulki wanda dama shi ne burina, na ɗale kan kujerar da na taso da tsananin yunwansa, dan haka yanzu zaɓi biyu ne suka rage maki, ko ki durkusa a gabana ki yi biyayya in cigaba da yi maki alfarma, ko kuma ki ja da ni ki kare a ƙaskantacciyar baiwa wadda zata zama karya ga bayin dake cikin prison ɗin Kingdom ɗin nan, ke kanki kin san yadda suke mu'amala da mata a ciki, wlh in sa a jefaki ciki, ki kare rayuwarki a hannunsu suna yadda suka so dake suna rage zafi, dan haka zaɓi ya rage gareki". Ya kai karshen maganar yana sanya hannunsa ya ɗan shafi fuskarta ya gangaro zuwa bakinta, ɗan matse bakin nata ya yi kafin ya gangaro da hannunsa zuwa kirjinta, ya gangaro da shi zuwa saman ƴan kananan breast ɗinta, sannan ya ce.

"Komai ya kare daga albarkatun jikinki, na karar da komai, babu abin da zan yi dake, masu lafiyayyun kaya nikeso a yanzu, ke yanzu sai irin bayi ko tsoffin mayakan da suka yi laifi aka jefasu prison, su ne zasu kwasheki, ni babu abin da zan yi da yamutsastsun abubuwan nan". Ya kai karshen maganar yana matse mata kirji da karfi. WATO UDE ÆŠAN ISKAN MAI RAI NE NA GASKEN-GASKE.

Mamaki ya hana Zarina motsawa, dan jin abin take yi tamkar a mafarki, sai da Ude ya matse mata breast ne ta farga ba mafarki take yi ba, dan haka sai ta ce. "Ni kake faÉ—awa haka Ude?".

Kara matse mata kirji da karfin gaske ya yi har sai da ta datse idanunta, sannan ta ciza laɓɓanta alamar zafi. "Ki kirani da suna mai daraja wato King, kuma ki rinƙa tausasa harshe a kai'na kina kirana a daraje!!". Ya sake faɗa yana cigaba da murɗe mata breast guda ɗaya.

Hannunta tasa ta ture shi da karfi, sai dai ina, ko motsawa bai yi ba, sai ma kara murÉ—e mata Æ´an abubuwan nata da ya yi da karfin gaske wanda hakan yasa ta saki kara tare da durkushen kasa a wajen. Wani irin jan dogon numfashi ya yi game da saukewa a hankali. "Ki koyi ladabi ga manya in ba haka ba jikinki ya fi tsamiya tsami!".

Yana kai karshen maganar ya yi gaggawar wucewa ya nufi hanyar fita. Tamkar a mafarki ya isko muryarta tana faɗin. "Karya kake yi karamun ɗan iska, Thomas family sun wuci a ci amanarsu, ko ka manta nike rike da karfin ikon na tsafin da kake tunkaho da shi ne?". Ta faɗa tana miƙewa tsaye. YAU FA AKE YINTA!.

Ba tare da ya juyo ba, ya cigaba da tafiyarsa ya amsa mata da. "Kin manta da cewa ni na koya maki tsafi har na baki karaga da ikon juya komai É—in ne?". Yana kai karshen maganar ya yi gaggawar ficewa abinsa.

DUM!! DUM!! DUM ta ji gabanta ya bada bugu, da gudu ta mike ta haura wannan É—an siririn staircase É—in domin ta haura sama ta je ta duba gambun murza tsafin nata, ta tsorata da ya ce ai shi ya koya mata kuma ya yi niyyar bata damar juya komai, dan haka a yanzu hankalinta ya yi mummunar tashi.

MY PEOPLE'S ME KUKE TINANIN ZAI FARU? YA FAƊA ZATA KAYA A TSAKANINSU? MACIYA AMANA BIYU ABU YA KWAƁE MASU, AKWAI KALLO FA GABA!!.

----------------------------🔥

BLACK WORLD.🔥

Bayan ta yi sallah isha'i ne ta shirya cikin kayan barcinta tamkar yadda suka saba, Smart ne ya tasasu a gaba dikkansu uku ya ce sai sun ci abinci sun ƙoshi a kan idanunsa, dan yaga ramar tasu ta yi yawa sosai, yana zargin basa wani cin abinci, sai dai su ɗan taɓa kada yunwa ta yi masu illah. Kuma hasashensa gaskiya ne, dan kuwa basa cin abincin, idan sun ji yunwa zata yi masu illah sai su ɗan tuttura sama-sama, wani lokaci ma Sweetie bata yin breakfast, sai dare in yunwa ya nemi kaita ƙasa sai ya ɗan sha green tea, to shi ne fa yau Smart ya tasasu a gaba.

Ya zauna a saman chair yana kallonsu dikkansu uku ya ce su ci. Yadda kuka san suna cin dissa haka suke ta faman kwaɓe fuska tamkar an yi masu dole. Dai dai ya ga ba zasu ci ta arziki ba sai ya yi masu jan ido a kan in basu ci ba sai ya saɓa masu, wannan dalilin yasa suka ware suka fara turawa suna runtse idanu dan abincin basa jin ɗanɗanonta sam-sam.

Ba shi ya kyalesu ba sai da ya tabbatar sun yi nak, sannan ne ya miƙe ya nufi bedroom na Big Bro, shi kansa Smart ɗin baya cin abincin fa, domin ya shiga damuwa sosai, ga shi babu wanda ya san halin da Big Bro yake a ciki, hakan yasa yake mulkar birnin a matsayin Big Bro, dan ma Ronnie yana highlighting ɗinsa a kan wasu abubuwa dan gane da birnin wanda bai gane ba.

A cikin kwanaki ukun da ya yi a kan mulkin ɗan uwansa mutanen birnin nan sun samu canji da sassaucin rayuwa fiye da tinaninku, kuma a cikin kwanaki ukun nan mata almo 8 ne suka haihu a birnin, amma da yake Smart bai san da batun ɗaukan ƴaƴansu maza ba, sai bai karɓe masu ba, mata 6 dikka maza suka haifa, da ya ji labari babban kyauta ya shirya aka kai masu, ya basu maƙudan kuɗaɗɗen da kusan har su kammala rayuwarsu ba zasu cinyesa ba, har yasa mata dayawa suka ji sha'awar haihuwa.

Sai dai kuma sun shiga shakku da mamakin yadda aka yi Big Bro ya yi masu irin wannan kyauta bai kuma karɓi ƴaƴansu ba! Do sun san yana da kyau over to over, wannan ɗabiarsa ce, amma kuma batun karɓar ƴaƴa ya yi mugun ɗaga hankalinsu da bai karɓa ba. Amma sun yi shiru suka cigaba da zubawa sarautar ALLAH su ga ko ya canza tsarin ɗaukar ƴaƴan nasu ya mayar da su sojojin yakinsa ne!.

A kwanaki ukun nan ba ƙaramin tasiri sunan Big Bro ya kara a birnin ba, ya ja gabaɗaya a ko'ina sun manna hotunan bakar damisa suna nuna alfaharinsu na kasancewarsa sarkinsu, sun ji bala'in daɗin canzawar mulkinsa a kwanaki uku, harta sojojin yakinsa sun ji daɗi matuƙa, dan ya sassauta irin horon da yake basu, ya basu freedom sosai ba kamar yadda Big Bro yake azabtar da su da horo ba tare babu rana tamkar wasu jakuna ba.

Wani irin daÉ—in da Ronnie ya ji na ganin yadda mutanen birnin nan suke murna suke jin daÉ—i game da yabawa yayansa da alfahari da shi, ya yi fatan idan Big Bro ya farfaÉ—o ya yi continuation daga kan in da Smart ya tsaya, sai da kuma bamu san me zai faru ba, mu jira tashin nasa tukun nan.

--------------------------🔥

Bedroom ɗinsu suma suka koma, Pretty na ƙoƙarin kwanciya a saman gado Sweetie ta ce. "Ni kam ke kam Pretty yaushe zaki yi hankali ne?". Harara Pretty ta dalla mata kafin ta kwanta, sai da ta gama shan kamshinta sannan ta ce. "Wai Sweetie ni sa'arki ce zaki rinka mun magana haka?". IRIN ITA BABBAN NAN!.

Sanin hali yasa Sweetie sassauta murya, cikin sigar rarrashi ta ce. "ALLAH ya baki hakuri, ni ba faÉ—a nike nema ba, amma dan ALLAH Pretty ki gyara abin da kike yin nan, kina dai ganin kowa ya ci abinci a gidan nan amma ban da Yah Omerish, amma ke ko a jikinki, kuma kin faÉ—a mun mijinki ne shi da na ce ki dai'na zuwa wajensa, kin ce ya ce ke matarsa ce, amma meyasa baki son kyautata mashi?".

Harara ta sake galla mata tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa. "Ai da nace maki shi mijina ne ban ce maki ina son shi ba! Ni Kamran nike so, da shi kawai nike son rayuwa, dan haka babu ruwana da wani Omerish!....." Bata iya ƙarisa maganar ba sakamakon zaro idanu da Sweetie ta yi, muryarta na rawa sosai ta ce. "Kam....... Kam..... Kamran kike so?".

Kai ta jinjina mata alamar tabbatarwa. Dafe saitin kirjinta Sweetie ta yi, can kasan maƙoshinta ta ce. "Na shiga uku ina son abin da sisterta take so! Kamran take so? Ni ma shi nike so, ya zanyi da rai'na kenan?".

Ganin tana magana ƙasa-ƙasa yadda ba'a ji ne yasa Pretty ta ce. "Akwai wani abin ne naga kin shiga wani yanayi daga batun Kamran?". Yadda kuka san babbar mace haka take magana.

"Babu komai, amma please Pretty kina Sona?".
Tana kallon tsakiyar idanunta ta ce. "Wace iriyar banzar tambaya ce wannan? Ina da wacce nike so biyunki a duniyar nan ne?".

Kai Sweetie ta girgiza alamar a'a babu, sannan ta ɗaura da cewa. "To dan ALLAH idan har kina son farinciki na ki tashi ki je ki lallaɓa Yah Omerish ya fito ya ci abinci, dan ALLAH kada ki kara cewa komai kawai ki tashi".

"Amma dai kin san nice babba kike mun magana kamar kina bani umarni ko? Kin san kuma bana son haka, bana son a rinka nuna mun wani É—agun kai!". On a serious note ta yi magana. ÆŠan yake kafi kuka ciwo Sweetie ta É—an yi kafin ta ce. "Na ji Aunty Pretty, ALLAH ya huci zuciyarki jinin King Abdul Muxxalib, ai in baki yi haka na ba daga gidan sarauta kika fito ba, yanzu dai muna neman alfarman a je a rarrashin mana yaya ya zo ya ci abinci".
Chapter 38 · 0% Book details