← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 130

Sashe 12

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai kawai ta jinjina mashi ba tare da ta sake yin magana ba, da haka suka sauko ƙasa, nan ta ga wata sabuwar duniyar da ta gagara hakura har sai da ta tambayesu ina ne nan? Wai dan ma ba ta glass way kuma bata escalator ya biyo da ita ba, elvator suka biyo wanda shi ta saba shigarsa a kingdom of power, ina ga da ta glass way ya biyo da ita wannan mayyar tsoro ba zata taɓa hawa ba, dan zata ce zata faɗo kasa ko kuma ta ce glass ɗin zai fashe ta faɗa kasa, tana ganin kasa da nisa ai yaseen ba zata hau ba.

A dining room suka isko Sweetie ta gama zubawa kowa abinci tana jiransu. Pretty sarkin ci take ta hau ci abinta, bata bar kanta a duhu ba, sai da ta ƙoshi cak sannan ta sake tamnayarsu wai ina ne nan?. Dikkansu sai suka rasa ta yacce zasu yi mata bayani, dan haka sai suka ce mata Big Bro royal palace kawai. Kasancewar tasan su Aneesa suna kiran Smart da babban yaya, sai ta zaci shi ne Big Bro ɗin ai, dan haka sai ta bar zancen a haka kawai ta hau yaba kyau da tsaruwar wajen.

Ita dai Sweetie yanzu hankalinta gabaɗaya ya yi kan Big Bro, sannan tana son su keɓe da Pretty ta tambayeta ina Spender ina kuma Kamran, tana san samun waɗan nan amsoshi guda biyun! Sai dai kafin samunsu sai dare ta tsala idan Ronnie ya yi barci, sai su haura sama su tattauna, dan haka sai ta danne tambayoyin a ranta suka cigaba da hira har zuwa lokacin sallar magrib, yau saura kwanaki biyar sallah!.

A ɓangaren shi kuma Big Bro, shirye cikin wasu irin mahaukatan kayan barci masu bala'in kyau ya fito, wando ce dogowa har ƙasa, sai kuma rigar zuwa gwiwarsa, rigar a buɗe take sai maɗauri a tsakiya, rigar dai zubin bathrobe take da, sai dai kuma kayan silky ne, ya yi fitina a cikin kayan, and ya ɗaure dogon gashin kansa har tsakiyan bayansa, yacce dai gashin gabaɗaya mutanen birnin suke, su fa hakikanin kiristoci ne masu ɗaukar abubuwa da muhimmanci ba kiristoci masu sunan kiristoci kawai ba.

Dan haka shi ma yana da dogon gashi sosai har tsakiyar baya dan koyi da Yesu, yau sam bai ɗaure gashin ba, kun san Annabi Isa baya ɗauke gashin kansa, haka yake zubosa side by side, shiyasa suma mutanen birnin basa taɓa ɗaure gashin kansu, sai su rabata gida biyu su sakota side by side, so shi Black Tiger yana ɗaurewa gaskiya, ba zaka taɓa sanin yana da dogon gashi sosai bama sai ya warwareta, gashin nasa bata da cika ne sai tsawo, kun san gashin larabawa ai, ga shi bakinkirin yana sheƙi.

Yau ya fito a ainahin kiristoci masu ƙoƙarin koyi da Yesu ɗin da ya saki gashin, ban taɓa sanin yana da wani dandatsetsen cros a wuyarsa ta zallar zinari ba sai yau, da alama ba kullum yake saka cross ɗin ba, idanunsa nan sun kara tura kala alamar akwai abin da yake damunsa, sai tashin fitinannen kamshi yake zubawa.

A gaban mirror ya tsaya domin cigaba da gwadawa ko zai iya kallan Mommah. Ɗan limshe idanunsa kaɗan ya yi tare da sake warosu jin alamar an taɓa kofarsa, ajiyar zuciya ya sauke, domin ko bai juyo ba yasan Sweetie ce.

Ita kuwa sai lallaɓawa take yi a hankali wai irin kada ya jiyota ɗin nan. Tana sanye da sleeping dress irin na jikin Ronnie, ta baiwa Pretty ma kala ɗaya ta sanya, ta baro Pretty da Ronnie suna hira ta ce masu bari ta je parlourn kasa tana zuwa, ta yi dabara ta ɗauki rose ɗinta ta fito. Shi Ronnie sarai yasan ba wani parlon ƙasa da zata je, Pretty ce bata san karatun ba.

Cigaba da binciko Mommah ya yi yana jin takun da take yi na nufosa har cikin ransa. Unexpected ya ji ta kwanto da kanta a saman bayansa, yacce Ronnie ya ce ta yi haka ta yi mashi, ta kawo mashi rose ɗin gabansa, cikin sanyin murya ta ce "Thank you so much my Big Bro, na yi farinciki sosai da ka haɗani da ƴar uwata, and na jinjina maka, ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata da ka zama sanadiyar na samu ganawa da sister ɗita ɗaya tilo a duniya, this rose is yours, saboda farincikin da ka sanyani a ciki ban san da me zan biyaka ba, amma ga wannan karamar kyauta daga gareni, please kada ka ce ba zaka karɓa ba ka ji?". Ta kai karshen maganar tare da dawowa ta gabansa tana cigaba da miƙo mashi rose ɗin.

To shi tin da yanzu ba dutse bane kuma babu duniyar shaiɗanu, sannan shi ɗin lafiyayyen namiji ne tuni ya ji wata shaukin mai musulmin daɗi ta lulluɓe zuciyarsa, ai bai san sadda ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ba, tin da ya baro kingdom of power yake jin ɗacin rai, bai samu natsuwa gamsasshe ba sai a yanzu, wani irin yanayi ya ji tana ratsa shi.

Ya shagala da jin yanayi mai daɗi unexpected ya ji saukar sumbata a saman lallausan kumatunsa, kwata-kwata bai ji time da ta sanya hannunta ta saƙalo wuyansa ba, sai dai ya ji haɗaɗɗen sumbatar da ta yi nasarar karasa jefa zuciyarsa cikin wata iriyar shaukin da tin da ya zo duniya bai taɓa jin irinsa ba, lokaci guda ya jisa tamkar a sararin samaniya, ya ma gagara iya fasalta yacce yake jin kansa.

Ganin bai yi mata kuma ko kallon face ɗinta bai yi bane yasa jikinta ya yi mugun sanyi, kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta juya gane da ɗaura mashi rose ɗin a saman mirror, a fili ta ce. "Dama na san ba zaka kulani ba bare ka karɓi kyautata, amma please ko ba zaka karɓa kyautar nan ba ka ajiyesa a tare da kai kuma a waje mai muhimmanci, na gode da taimakonka a gareni". Cikin sanyin murya da karyewar zuciya ta yi maganar. Ta kai karshen maganar tare da ɗan matsawa kaɗan zata raɓa gefensa ta wuce.

Da ido ya bi kyakkyawan face É—inta zuwa kan haÉ—aÉ—É—en gurun wuyarta, har ta É—an wucesa kaÉ—an tana nufan waje, unexpected ta ji saukar hannunsa a saman waist É—inta, ya jawota ta dawo gabansa, ba tare da ya cire hannunsa daga waist É—in nata ba ya É—an rankwafo kanta, kallansa gabaÉ—aya a kan É—an bakinta, kamar zai yi magana sai kuma ya É—an yi shiru.

Kallan tsantsar kyansa a kurkusa ta tsaresa da yi, ji take yi tamkar ta sumbaci ɗan bakin bawan ALLAH'n nan, yau ya yi wani fitina, yacce ya saki gashin kan nan nasa sai ya ruɗa mai kallansa, ga gashin na larabawa mai tsananin laushi da sheki, bata taɓa zatan shi ma yana barin gashi irin na mutanen birnin ba sai yau, kuma ya yi bala'in kara fito da tsantsar kyansa. While shi ma abin da yake ji a ransa kenan. In a cool way sosai bai san time da ya furta. "You're so kind, sexy and adorable". Ya yi maganar ne ba tare da bakinsa ta hana abin da zuciyarsa take ayyanawa fita fili ba, ya tsareta da idanu zuciyarsa na ta yaba kyanta shi kuma yana ƙoƙarin dojewa, shi ne dai maganar ta fito fili.

Mamaki tamkar ya kasheta, wai yau ita ce Big Bro yake cewa tana da kyau? Abin da mamaki, gabaÉ—aya hankalinsa a kan kyakkyawan É—an bakinta da take É—an motsa shi a hankali-hankali, kamar yana kerma saboda mamaki da kuma ta É—an fara tsorata na irin kallon da yake yi mata, kuma tin da ba dutse bane lafiyayyen namiji ne tini idanunsa suka fara canza launi, alamar abar gadan ta motsa, jikinsa har tsuma yake yi.

Uhm a kan Sweetie ya fara sanin feeling bayan rabuwarsa da duniyar shaiÉ—anu, kunga kuwa dole idan ya ganta sai komai ya motsa mashi.

Sai a wannan lokacin kallanta ya sauka a kan kyakkyawan cross dake É—aure a wuyansa, take ta ji babu daÉ—i, bata so hakan ba, amma a zuciyarta ta kuduri niyar rabashi da ita, dama addinin nasa gabaÉ—aya.

Hannunta na rawa ta sanya ta ɗan taɓa kyakkyawan arab hairnsa da ya ɗan zubo ta saman shoulder ɗinsa zuwa kirjinsa, ɗan janye gashin ta yi domin ta samu damar ganin cross ɗin da kyau, dama gashin ya ɗan lulluɓesa ne, dan tabbatarwa yasa ta janye gashi.

Wani irin kamshi ne ya kara dukan hancinta na mayukan gashinsa, babban yatsanta na rawa ta ɗaura a saman cross ɗin ta ɗan shafo a hankali. Slowly ya lumshe idanunsa tare da sake warosu a kanta, zuciyarsa ta so ace Sweetie ta iya shagwaɓa kamar Pretty, saboda babu karya ɗazun Pretty ta tafi da shi yacce take ta zuba mashi shagwaɓa.

Muryarta na É—an rawa ta ce. "Big Bro wannan cross É—in fa? Please zaka iya bani tarihin wanda yake a jikin cross É—in a tsaye?".

Kun san hoton Annabi Isa suke sawa in da suke ikirarin an kashesa an buga kutsa a hannaye, to so take yi ko ta wace hanya su yi muhawarar addini tsakaninta da shi, dan tasan hujojin da zata bashi wlh sai ya musulunta babu shiri, amma shi kuma sam yaki, shiyasa ta ɓullo mashi ta wannan hanya, ta nuna kamar bata san ma'anar cross ba.

Sai dai kuma ita ta yi tambayarta kuma ta ji kayanta ita kaɗai, dan shi gabaɗaya hankalinsa ya yi nisa wajen wani tinani, yacce ta motsa lips ɗinta ta yi maganar cross ɗin nan ba karamun kara birkita mashi lissafin ƙwaƙwalwa ya yi ba. Slowly ya ɗan matso da face ɗinsa dab da ita tamkar zai haɗesu, sai kuma ya dakata yana ɗan shakar kamshin perfume ɗinta. Sosai ta tsorata, bare ma da ta tina abin da ya faru rannan a toilet, gabaɗaya sai ta ji jikinta ya hau kerma, a tinaninta wani abin zai yi mata.
Chapter 12 · 0% Book details