← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 130

Sashe 10

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya dai ko?". Ronnie ya tambaya yana nufota....... "I think su Big Bro ne suka dawo, kasan ya ce mun yau zai dawo ba zai kwana ba". Tana magana tana murmushi. A kusa da ita ya zo ya tsaya idanunsa a kan jiga-jigan jiragen dake shawagi a sararin samaniyar empir É—in. GabaÉ—aya jiragen da tambarin sunan Black Tiger a jikinsu, sannan da hoton bakin damusa.

A sanyayye ya ce. "Waɗan nan ai ba droms na yaki bane, jirage ne da suka ɗauko solar + hydrogen wato cibiyoyin wutar lantarki mai tsaftar da kuma karfin da wuta ba zata iya yankewa a new palace ɗin Big Bro ba, sai kuma self-healing materials, wato karafa da ke iya daidaita yanayi, irin ko iska, ruwa, zafi or sanyi ake yi a birnin cikin empeir na Big Bro zata kasance da daidaitaccen yanayi, so kayan kara ƙawata new empeir ɗinsa ne".

Face É—inta ne ya É—an canza, ta so ace sune suka dawo, amma ba komai zata yi dakon jiransu. Cike da farinciki a ranta ta ce. "Bro kasan me?".
Juyo da kallonsa a kanta ya yi kafin ya amsa mata da bai sani ba.

"Wannan new empeir ɗin na Big Bro bana jin akwai irinsa a duniya, ka duba girman ginin fa, gold ya yi kuka a wannan gini, kalli yacce yake wani irin kyalli yana ɗauke idanu, dik glasses da aka yi amfani da su wajen wannan gini ban taɓa ganinsu ba sai a kan wannan palace ɗin, gaskiya ya yi karshen haɗuwa sosai".

Idanunsa a kan kyakkyawan face É—inta ya ce. "I wish wannan palace É—in ya ci sunan Omaish red diamond palace tin da kinga da red diamond É—in nan aka yi kusan rabin ginin".

Zaro mashi idanunta ta yi har sai da ya É—an rage nasa, kara faÉ—aÉ—a murmushinta ta yi game da cewa. "Ba dai Omaish ni ba, wane ni, na ma san sunan da za'a saka mashi bai wuce Black Tiger new palace ba".

Nisawa ya É—an yi kafin ya ce. "Uhm wannan empeir da muke ciki ita ce Black Tiger new palace ai, old one da muka baro kuma gold palace sunanta, dan haka ina fatan canjin sunan da za'a samu a sabon nan ya zamana sunanki ne, kai sunanki ne ma In Sha ALLAH".

Saboda bata son su ja maganar ya yi tsawo yasa ta ce mashi tana zuwa. Ta kai karshen maganar tare da wucewa tana sakin curtains na views É—in. Ya gane waskewa maganar take son yi, dan haka sai ya rabu da ita ya bita da idanu kawai.

Waje ta nufo, kai tsaye ta wuce bedroom na Black Tiger. Tana zuwa ta shigar da password ɗinsa ta buɗe kofar, tana sanya kai sai da ta sauke wani sanyayyar ajiyar zuciya, take wani Musulmin daɗi ya lulluɓeta, dama tin ɗazun kewarsa kamar ta yi ihu, yanzu da ta shigo side ɗinsa sai ji ta yi tamkar shi ta gani.

Wucewa saman swang sofas dake a É—akin ta yi, luntsama saman É—aya ta yi ta zauna tana tinanin rayuwar duniya. GabaÉ—aya sai ta ji ta damu da baya nan, a Æ´an kwanakin nan bata cika yin tinanin Kamran ba, saboda a yanzu soyayyar Black Tiger ya ci karfin zuciyarta, idan ba shi ba bata tinanin kowa!.

Ta jima zaune a wajen kafin barci ya fara ɗauketa, da kyar ta iya miƙewa tana zabga hamma ta koma saman dogowar sofa ta kwanta, tana kwanciya babu jimawa barci mai nauyin gaske ya ɗauketa. Shi ma Ronnie kasancewar sun kammala shirya komai da zasu tarbi Pretty, hayewa bed ɗinsa ya yi ya kwanta yana tinanin a wani halin yayansa yake ciki a yanzu!.

.......... AFTER SOME MINUTES.

Can cikin barci ta ji tamkar an É—agata sama, sai kuma ta jita a jikin mutum wanda hakan yasa a razane ta waro idanunta. Ai tana warowa kai tsaye sai saman kyakkyawan face É—insa da ta karayin very fresh, sai dai kuma alamar yana a cikin damuwa, domin fuskar ta fi ta kullum tamau.

Ai a miliyan ta yi blinking eyes É—inta domin ta tabbatar ba mafarki take yi ba. Aikuwa shi É—in ne, yana sanye da black pj's a jikinsa, kayan sun yi masifar yi mashi kyau kasancewarsa fari tas cikin bakin abu.

Zabura ta yi zata kwace kanta sai ji ta yi ya shinfiɗeta a saman katafaren king bed ɗinsa ya juya tamkar ba shi ba, ya nufi in da Pretty take kwance a balconynsa, yau a tsananin natse yake tafiyarsa fiye da kullum, tamkar jikinsa dik a mace. Lallai barci mai nauyin gaske ne ya ɗauketa, domin kuwa yacce jirage suka rinƙa shawagi a sama kusa-kusa suna kukan nan dik bata ji ba, yacce empeir ɗin ta ɗauki tashi ta ko'ina dik bata ji ba, ko'ina sai da ya amsa Big Bro ya dawo, amma dik bata ji ba, saboda daren jiya bata samu ishasshen barci ba, dik saboda zumuɗin dawowar Pretty, shiyasa barci yakamata mai nauyi.

A miliyan ta diro kasan bed ɗin, da gudu ta bi bayansa tana faɗin ina yar uwarta? Ko sannu da dawowa bata yi mashi ba, ita dai yar uwarta kawai. Shi kuwa yana dawowa ya kwantar da Pretty a balcony ya wuce toilet, sai da ya yi wanka ya canza kaya, ya buƙaci abincin da zai ci, sannan ya dawo zai wuce wajen dining area ɗinsa ne ya hangota zata faɗi ƙasa, barci ya yi daɗi har ta kusa faɗuwa bata sani ba, shi ne ya yi gaggawar zuwa ya ɗauketa zuwa saman bed ɗinsa!.

Zama ya yi gefen Pretty bayan ya ɗauko bottle water kenan. Da gudu ta ƙariso wajen, idanunta a kan Pretty dake kwance, jikinta har kerma yake yi, tamkar mai tsoron yin magana ta ce. "Pretty ɗita ce wannan?". Ta tambaya tana dawo da kallonta a kansa. Kada ku manta tun Pretty tana da shekaru bakwai Sweetie tazama makauniya, dan haka bata san ainahin kamannin Pretty ba, shekara bakwai ai kunga ita ma ba wani wayau ke gareta ba, so banda kamannin da suke yi matsayinsu idencial da ba zata iya gane Pretty ba!.

Yana ƙoƙarin ɓalle robar ruwan ya ɗago da kallonsa a kanta, sai a lokacin ya fara kare mata kallo, ta yi fitina a cikin kayan jikinta, har cikin ransa sai da ya ji wani irin sanyi ganin haɗuwar da ta yi, kamar zai ce wani abin sai kuma ya fasa game da kawar da kallonsa daga kanta, ruwa ya tarbo a hannunsa ya shafa a face ɗin Pretty yana jin wani irin musulmin daɗi da kuma sabon yanayi yana kara shigarsa........ Dik wannan bidiri Ronnie yana can shi ma yana ramakon barci!.

Kun san tin da duniyar shaiÉ—anu suka bar jikin Black Tiger ya koma so sillent over fiye da da can baya, da idan ka mashi magana sau biyu zuwa uku zai amsa, amma yanzu ka yi ta magana ba ya amsawa, magana mugun wahala take yi mashi, wato yanzu ne ainahin siffarsa ta bayyana, ga jinin sarauta dake guda a jikinsa, sai abin ya taru ya yi mashi yawa! Ya zama miskili ajin farko, kallo da ido kawai ya wadatar!.

Nannauyar ajiyar zuciya Pretty ta sauke kafin ta waro idanunta a natse. Kai tsaye sai kan face É—insa, a karo na biyu ta sake sauke ajiyar zuciya, dan a tinaninta Smart É—inta ne. Lumshe idanunta ta yi zata fara yi wa Smart iskancin da ta saba. A hankali ta É—ago da kanta ta koma jikinsa, a saman Lion chest na Black Tiger ta kwantar da kanta, ita ta manta a ina take ta suma, kawai zata fara rashin M da ta saba.

Hannu tasa ta fara dukan kirjin nasa a hankali, cikin shagwaɓa sosai ta fara faɗin. "Ni ka tashi muje ka rakani in ci abinci, yunwa nike ji".

Ai daga Black Tiger har Sweetie babu wanda ya iya kwakkwarar motsi, Sweetie ta yi suman tsaye ganin yacce ƴar ɓul-ɓul ɗinta ta kara kiba da cika, gurun wuyarta so Masha ALLAH. Shi kuwa Black Tiger ji yake tamkar Sweetie ce a jikinsa take yi mashi wannan shagwaɓa, haka kawai zuciyarsa ta ayya mashi ina ma ace Sweetie ce ta iya shagwaɓa yacce Pretty take yi, ai da sai shiru.

Jin bai amsa mata bane yasa ta sake cewa. "Ya na ji kirjinka ya kara tauri da girma?". Tana magana tana mashi iskancin da take yi wa Smart, wato tana bin sassan jikinsa da shafa, har zuwa kyakkyawan wuyansa, wanda shi kuma gabaÉ—aya ya mayar da abin kamar Sweetie ce take yi mashi hakan, kun san ita ma ta iya mashi tsiya har da sumbata wani lokaci!.

Lokaci guda abin tamu ta mata ya motsawa Sweetie, wato kishin da bata san shi ba, kun san shi kishi ko ka san shi ko baka san shi ba idan ta motsa maka sai ka yi, abin a jininmu yake, dan haka wlh ita Sweetie bata ma san tana son Black Tiger ba, bata san menene kishi ba, kawai dai ta ji zafin irin yacce Pretty take shafe mashi jiki ne, hakan yasa ta ce. "Omnish lafiyarki kuwa? Kin san shi ne?".

A wani irin miliyan Pretty ta waro idanunta waje, domin ko mutuwa zata yi ta dawo muryan Sweetie ba zai taɓa ɓace mata ba. A zabure ta juyo da kallonta izuwa ta in da ta ji maganar.

Tamkar a mafarki haka ta ga Sweetie, ai bata san lokacin da ta bar jikin Black Tiger ba, sai ganinta a gaban Sweetie kawai ta yi, ashe muryarta garau yake iskanci ne yasa take magana a shagwaɓe, da karfi ta ce. "Sweetie na?!!".
Chapter 10 · 0% Book details