← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 130

Sashe 126

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannun da ya ɗaga mata ne yasa ta dakata tana kallonsa. Idanunsa gabaɗaya sun canza launi zuwa jajir kamar wuta, dan ransa ya fara ɓaci............ "Saboda ina sonki ba shi zai baki damar ki tsaya a gabana kina faɗa mun abin da kika yi niyya ba, kada ki sake yin magana a kan addinina, bana son addinin naku kuma ba zan bishi ba, ko zaki tilasta mun ne?!". Ya faɗa yana miƙewa tsaye.

Dik da tsoronsa da take ji bai hanata sake cewa. "Tabbas zan tilasta maka komawa musulunci, dan shi ne addininka na gaskiya, kowa naka musulmine, ya za'ayi ka ce kai ba zaka musulunta ba? Baka son gaskiya Big Bro........".

Ai bata karisa maganar ba ta ji saukar wani irin gigitatcen marin da ya sanyata ganin taurari, take ta ji komai ya É—auke mata cak, wani irin jummmmm ta ji, take wani irin jiri mai karfi ya kwasheta ta tafi gabaÉ—aya zata faÉ—i. Da hannu É—aya ya rikota ta faÉ—o saman lion chest É—insa.

A razane momma da Smart suka miƙe tsaye, da sauri suka karisa kusa da su. Take shatin hannunsa biyar ruɗu-ruɗu suka bayyana a kan fuskarta.

Word ɗin momma har yana haɗe wajen cewa. "Haba Unays, meyasa zaka taɓa lafiyarta? Is she not your wife? Ko baka sonta ne?"........ Smart ne ya karɓi zancen da cewa. "Sorry my blood, amma idan ka cigaba da yi mata irin haka watarana zaka rasa ta ne".

ÆŠan rage tsawonsa ya yi ya É—auketa cak sai saman sofa ya kwantar ba tare da ya amsa su momma ba. A gefenta ya zauna yana sauke huci a hankali-hankali.

A tare momma da Smart suka dawo suka zazzauna....... "Momma bana son sake jin wanna addinin naku, ki faÉ—awa Maysh idan ta sake mun magana a kansa she will lose some pad of her body!". With harsh voice ya yi maganar.

Cikin alamar tausasawa momma ta ce. "Ba zata sake ba, amma please kada ka sake yi mata irin wanna mari ka ji?"........... Jinjina kai kawai yai ba tare da ya sake yin magana. A daidai lokacin ta yunkura a hankali ta miƙe zaune tana sunkuyar da kai kasa, ba karya ta maru fa gaskiya.

"I'm so sorry, ba zan sake yi maka haka ba, ni ma nasan na yi kuskuren yi maka magana a haka babu respect, ni É—in ce bani da control a kan addinina, amma zan kasance mai tausasa kalamai a kanka"...... Ba wai dan bata ji zafin marin da yai mata bane, no ita É—in yarinya ce mai hankali da hangen nesa, kuma tabbas tai kuskure a yadda tai mashi magana, tin da so kuke ya musulunta ai ba ja in ja da shi zaku yi ba har kuna ce mashi baya son gaskiya, wanna baku nemi ya musulunta ba, a hankali zaku bisa har ya fahimci abin da kuke son ya fahimta, kuma ta yi wani tinani ne, Big Bro ba mutum ne da wani zai iya tankwarasa ba, idan suna son ya bi abin da suke so dole ne su bisa a hankali, kuma ita da yake balain kauna zata iya juya zuciyarsa idan ta bisa a hankali, shiyasa ta bashi wanna hakuri, tana son shi over, tana son su rayu a tare, su haifi Æ´aÆ´a su gina zuri'a mai cike da farinciki, to dole zata jure, fushi ba nata bane, idan ta daure ta yi nasara lokaci zai zo da in tai fushi da shi ba zai iya barci ko cin abinci ba, dan haka hakuri da juriya shi ne nata a yanzu.

Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke na jin kalamanta, juyo da kallonsa a kanta ya yi, É—an rintse idanunsa ya yi ganin shatin yatsunsa a kan fuskarta sun yi jajir, har cikin ransa ya ji hakan batai mashi daÉ—i ba. In a cool way sosai ya ce. "Tashi mu tafi É—aki".

Satar kallon momma tai, dan É—azun ta faÉ—awa momma ba zata sake kwana da shi ba. Da sauri momma tai gyaran murya tare da cewa. "Unays ina son yau ka kyale mun ita mu kwana a nan".

Da sauri ya juyo da kallonsa a kanta. Nisawa mai É—an nauyi momma tai kafin ta ce. "Ta iya tausa sosai, so nike ta mun, kuma akwai abin da zamu yi da ita an juma, please ka barmun ita ka ji?".

Dik da yasan ba gaskiya momma take faɗe ba duba da yadda tongue ɗinta yake rawa, amma sai ya riko hannunta, cikin sanyin murya ya ce. "Dik abin da kike so shi nike so, ta zauna dake". Yana kai karshen maganar ya miƙe tsaye, a natse ya fara tattakawa ya nufi waje.

Da kallo suka bi bayansa har ya kai bakin kofa, zai fita kenan ya juyo da kallonsa a kansu. Da sauri suka zare idanunsu, ya gansu sarai, amma sai ya ce. "Kai zo mu tafi tin da yanzu dik É—aya muke". Yai maganar yana kallon Smart da gabaÉ—aya yau an yi mashi formating brain, abin da bai zata ba yau ya gani.

Miƙewa yai ya bi bayansa yana tinanin dole su haɗa kai da Sweetie dan ganin sun dawo da shi kan hanya, Smart bai taɓa zatan girman ilimi da hangen nesan Sweetie ya kai har nan ba, gaskiya ya jinjina mata sosai.

Suna fita momma ta dawo da kallonta a kan Sweetie, cikin tausasawa ta ce. "Ki yi hakuri kin ji ƴata? Kada ki karaya, zamu yi nasara In Sha ALLAH, na fahimci kece rauninsa, kuma ba zai iya yi maki komai ba, sai dai na lura baya son raini, kuma wanna a jininsu take, dik basa ɗaukar raini, ki rinƙa tauna magana idan zaki faɗa mashi, saboda zuciyarsu makauniya ce, idan ransu ta ɓaci suna mancewa da suna son abu".

Jinjina kai Sweetie tai, a sanyayye ta ce. "Babu komai momma, nasan halinsa sosai, nima É—azun É—in ban san ya aka yi nai mashi magana haka ba, amma ina fatan ALLAH yasa kada in sake yi mashi magana ba respect haka".

Alama momma tai mata da hannu a kan ta zo kusa da ita, da sauri ta miƙe ta je. Rungumeta momma tai tana zuba mata ruwan albarka kafin ta ce. "Kin ci abinci ne?". Kai ta jinjina alamar e ta ci................ Karya take yi bata ci ba fa, kawai bata jin kamar zata iya ci ne, dan yau King Of Heart ya mareta bayan fara soyayyarsu, abin ya taɓa mata zuciya.

"To jeki hau bed ɗina ki kwanta ko? Daga yau a ɗakina zaki rinƙa kwana, bari in duba daddynku in zo, gobe zaku je ku gaida shi, sai ki shirya, dan ya ce yana son ganin sabbin yaransa". Ta kai karshe cikin tausasawa tana ɗan murmushi.

Murmushi Sweetie ta saki kafin ta ce. "Ina sonki sosai momma"....... "Nima Ina sonki sosai Æ´ata, ina jinki tamkar Zunairata". Wani irin daÉ—i Sweetie ta ji har da kara kwanta mata a jiki. Shafa bayanta momma ta yi, almost 3 mins suna a haka kafin Sweetie ta raba jikinsu.

Miƙewa momna tai ta nufi waje tana faɗa mata ta je ta kwanta. Momma na fita ta sauke ajiyar zuciya, a ranta ta ce. "Ba zan iya kwanciya a gadanki ba momma, sai dai a saman sofa". Ta faɗa tare da miƙewa ta nufi cikin ɗakin, ita da an barta ma ɗakinsu Mahreen zata wuce, bata san cewa ta wuci nan ba, dole ne ita da Pretty a basu tsaro sama da kowa a gidan, tamkar yadda za'a baiwa su Smart tsaro, dan su ɗin bugun zuciyar zakunan gidan ne, in babu su babu su Smart, idan babu su Smart kuma ai a yanzu babu Kingdom of Power yadda makiya suka yi masu zobe ta ko'ina haka, Smart, Big Bro, Ramish su ne power ɗin Kingdom ɗin a halin yanzu!.

Saman sofar dake ɗakin momma ta kwanta tare da fito da wayarta, har ta kunna wutar screen ɗin kuma sai ta mike ta ɗauko bargo da pillow daga wajen closet ɗin momma. Ta dawo ta kwanta ta lulluɓa.

Tana kunna screen light ɗinta ta ci karo da sakonsa. "Na ji zafin ganin yatsun hannuna sun bayyyana a kan kyakkyawar fuskarki, ban ji daɗi ba, ya ragewa matata kyau". Shi ne abin da ya rubuta. A ranta ta ce watau dai hakuri ne ba zai taɓa badawa ba, kai Big Bro sai shirin ALLAH, ita ta gane kuskurenta ta bashi hakuri, amma shi dik da yasan bai kyauta ba ba zai bada hakuri ba.

Kwafa tai yi ta share message É—in taki reply, wai irin ta nuna mashi tana fushin nan sai ya bata hakuri. Fita tai ta fara yawonta a media. Jim kaÉ—an ya sake turo mata sako. "Maysh ba zan iya cin abinci ni kaÉ—ai ba, ki zo mu yi dinner a tare please".

Tana gama karanta sakon ta sake fita abinta taki reply, yana ganin ta gani kuma, hakan yasa ya ji babu daÉ—i, zuciyar maza ba zata iya fushi da abin da suke so ba, ya sake rubuta mata. "Fushi kike yi da ni my Maysh?".

Yes ta tura mashi. Yana gama gani ya rubuto mata. "Please ki daina kin ji? You're hotting my heart". Cikin sigar tausasawa yai maganar. Wani irin tausayi ya bata, bai taɓa yin soyayya ba sai a kanta, kuma irinsu idan suna son abu da zuciyarsu gabaɗaya suke so, shiyasa idan aka yaudaresu zaku ga suna kashe kansu, dan ba zasu iya jura ba, sun rigada sun bada zuciyar.

"Ba zan zake yin fushi da kai ba to". Ta rubuta ta tura mashi. Yana zaune a saman sofar da yake kwana, wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tura mata. "A hot kiss Maysh".

Kyakkyawar murmushi ta saki kafin ta kunna voice, a shagwaɓe sosai ta ce. "Uhmm uhmmm ni dai a'a, ka bari dai sai mun yi aure zan rinƙa yi maka mai sanyaka manta hanya".

Tin da ya kunna voice ɗinta ya sanya hannu ya ɗan dafe saitin zuciyarsa yana sauke ajiyar zuciya, Maysh tai mashi shagwaɓa, gaskiya ta narka zuciyar Big Bro, har ya ji dik wata damuwa tasa ta gudu, shi fa idan zata kwana tanai mashi shagwaɓa zai iya kwana yana saurara.
Chapter 126 · 0% Book details