Sashe 41
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta tsammaci ko ya manta da abincin ne, dan haka sai ta miƙe a natse ta karisa gabansa, a kusa da shi ta ɗan gefe ta tsaya ta jingina da jikin mirror drawer ɗin tana bin face ɗinsa da kallo. "Big Bro abincin fa?".
Bai tanka ba, hasali ma bai yi kamar yasan da tsayuwarta a wajen ba. Bata yi mamaki ba, idan da sabo ta saba. Gyara tsayuwarta ta yi tana cigaba da kura mashi idanun. Unexpected idanunta suka sauke a saman faffar kirjinsa, kada ku manta ya kwance igiyar bathrobe É—in, Lion chest É—insa a buÉ—e. Zubawa chain guda biyu da cross cikon na uku da suke wuyarsa ido ta yi, a mamakinta da ta yi wa cross É—in kallon kurillah sai ta ga alamar abu a cikinsa, sannan akwai alamar hoton fuska mutum a cikinsa, dan design na cross É—in nasa ya banbanta dana kowa, yadda wajensa yake kamar glass, cikin kuma baka iya gane me a ciki, sannan yana da kauri da É—an faÉ—i.
Kara zaro ido ta yi tana kure kallonta a kansa, shiru ta ɗan yi tana tinanin a ranar da wancan abin ya faru, lokacin da ya shaketa ya ɗagata sama ɗin nan tabbas ta yi ido biyu da wannan cross ɗin, tabbas a wannan lokaci wani irin koren wuta cross ɗin yake bayarwa yana wani juyi daga ta ciki. To meyasa a dik time da Big Bro yake lafiya cross ɗin take fara tas har da kyalli? Amma da zarar ya shiga wani yanayi cross ɗin zata koma koriya shar?! Abin ya yi matuƙar ɗaure mata kai, sannan bugu da kari yanzu ta tina cewa fuskar mai kama da wanda ta gani suke hira da Mommah ta cikin mirror ɗinsa (King Zuhair) shi ta gani a face ɗinsa ranar da abin can ya faru, to waye waɗan nan mutane a cikin rayuwarsa? Yana da matuƙar kyau ta san da hakan!.
Ta yi nisa cikin tinani sai ji ta yi ya hura mata iska mai É—an É—umi daga bakinsa izuwa saman fuskarta. ÆŠan firgita ta yi, a hanzarce ta dawo da kallonta a kan face É—insa, da ido ya yi mata nuni da mirror É—insa. A wani irin slow ta juyar da kallonta cike da fargabatar abin da zata iya cin karo da shi.
Lokaci guda ta É—an zaro idanunta tare da sake juyowa ta kallesa. "Su waye su?". Ta jefa mashi tambayar lips É—inta suna É—an kerma, saboda a jikinta ta ji cewa wannan guy da ta kallah shi ne Kamran, kerma da lips É—inta suke yi kuma shi ne kada ace wani abin Big Bro zai yi mashi! Da ta tabbata cikin takaici kuwa.
Sai da ya gama shan kamshinsa for almost 5 mins, sannan ya ce. "Shi ne Kamran É—in naku".
Ai a miliyan ta sake juyar da kallonta a kansa, yana zaune saman sofa, ya farfaÉ—o, Hoorain na zaune gefensa yana bashi tea a baki, ga sadauki Rishan a gefensa É—aya yana tura mashi abinci hannunsa rike da spoon, Alhamdulillah Kamran jiki ta yi kyau sosai, har Æ´ar kiba ya yi a maimakon rama, sai dai yau kwanansa biyu da farfaÉ—owa, ban da sunan Pretty babu wata suna da yake iya faÉ—a, yaki yarda ya yi magana da su Hoorain, akwai shi da bala'in zuciya kun sani, to fushi yake yi da Hoorain dik da bai san wanenen shi a gareshi ba a yanzu, kada ku manta Hoorain ne ya jibgesa kuma ya hanasa kama Pretty, shi ne har ya suma ya sha jinya haushin Hoorain na ransa. SAI DA KAI YARON MAMMARSA, KAWAI A BAKA PRETTY, SHI NE KAMATABLE, RASHIN BAKA ITA KUMA SHI NE RASHIN KAMATABLE, KO YA KUKA CE MAGOYA BAYAN DAMISAN MAMMARSA?!!.
"Kin san wanenen Kamran a gareku?". Big Bro ya jefa mata tambayar. Ta kafe Kamran da ido tamkar ta kirasa ya amsa take ji, ya tafi da imaninta sosai, sai dai ga mamakinta sai ta ga gabaÉ—aya daga shi, har su Hoorain, Ronnie da su sadauki Rishan dik yanayin fuskarsu guda ne, dikkansu Koreans ne, bata ma kara ruÉ—ewa ba sai da ta kalli Hoorain da kyau, shi ai hatta gashin kansa iri É—aya ne da nata babu wani banbanci, like abin ya yi mugun bata mamaki, ta shiga ruÉ—ani, sai dai bata gama fita ba ta ji cool sexy voice É—insa yana faÉ—in. "ÆŠan uwanki ne na jini, babanku É—aya da shi........". Bai kai karshen maganar ba ya dakata sakamakon sauke idanunsa da ya yi a kan Auta da ta shigo cikin É—akin a yanzu, hannunta rike da bottle na ruwa ta zo ta zauna kusa da Hoorain.
Lokaci guda Big Bro ya ji zuciyarsa ta amsa, a ransa ya ce wacece wannan mai kama da su haka? Domin samun amsa sai ya shiga bincike a kanta da Hoorain da ta zauna a kusa da shi tana miƙa mashi bottle na ruwan, sai tambayarsa Sweetie take yi ya aka yi Kamran ya zama ɗan uwansu. Amma bai bi ta kanta ba ya hau bincike kan Auta kawai, a nan ne ya ci karo da abubuwa da dama masu ban mamaki da al'ajabi, nan ne ya samu labarin Auta ai ƴar Autar King Zuhair ne, kuma ƴar Mommah, which means kenan Auta Autar idencial biyun nan ne, Autar the two Lions of Mommah kenan!. (Wato Autar su Smart Tiger and Black Tiger Tiger.)
ÆŠan shiru ya yi kamar mai tinanin wani abin, sai kuma ya koma ya fara bincike kan mutumin dake ikirarin shi ne mahaifinsa, wato King Zuhair. Ita dai ya barta da kumfa a baki ya ki zayyana mata ta yadda aka yi suka zama uba É—aya da Kamran, ya shiga wani aiki nasa.
Wannan bincike da ya yi ta jawo mashi abubuwa da dama a rayuwarsa, ya yi mamakin ganin yadda rayuwar King Zuhair take dabaibaye da ruɗani ga uban tarin makiya tamkar a kansa aka fara yin sarki mai adalci da gaskiya, ta ko'ina basu barshi ba, ya gano shirin su Zarina na neman mallake masarautar King Zuhair su shafesa a doran duniya, ya kuma gano akwai tarin makiya da munafukai dake kewaye da King Zuhair, wannan abin ya jijjigasa sosai, haka kawai ya tsinci kansa da jin tsananin zafin abin da ake shiryawa King Zuhair bawan ALLAH, domin dik rashin imanin Big Bro ya shaidawa kansa King Zuhair adalin sarki ne kuma bawan ALLAH wanda ya sadaukar da abubuwa da dama da yake kauna a rayuwarsa domin farincikin al'ummar da yake mulka, lallai sarki irin wannan bai cancanci a barshi ya faɗi ƙasa ba. SAI DAI KAI BIG BRO NAMU NA AMANA!!.
Yanzu amsa É—aya yake son sani shi ne meyasa sauran masarautun nan suke gaba da King Zuhair? Amsar da yake son sani kawai, wanda shi kansa Smart ita yake son sani! Dani da ku masu karatu ma dik ita muke son sani, dan ita ce tushen komai!.
Ya yi nisa cikin abin da yake yi sai gani ya yi Sweetie ta juya zata bar wajen cikin kunan rai, dan ya fi baki goma tana yi mashi magana bai amsa ba, shi ne ranta ya ɓaci zata wuce ta bashi waje. Hannunta ya riƙo ba tare da ya yi magana ko ya juyo ya kalleta ba, ya cigaba da abin sa yake yi na bincike-bincikensa, rafanan tsafin nasa suna bashi information kan yadda birnin nan ya canza gabaɗaya.
Zaro idanu ya yi yana kallan yadda jama'arsa ke yabonsa suna nuna kauna a garesa, nan ya shiga binciken menene dalili, yana rike da hannunta bai saki ba har ya binciko me yafaru a birnin da suke zuba mashi ruwan albarka haka. Shiru ya yi yana mamakin ganin abubuwan da Smart ya canza cikin kwanaki uku kawai. DAMA SAI WANI ABIN YA FARU WANI ABIN YAKE BAYYANA, A LOKACIN DA WANI ZAI KWANTA A LOKACIN KAI KUMA ZAKA TASHI, A LOKACIN DA WANI YA ÆATA A LOKACIN KAI KUMA ZAKA SHIGO HASKE!. WANI SANADI KE KAWO WANI, DOMIN KUWA BIG BRO A CIKIN RANSA YA FARA TINANIN YA CIGABA DA KYAUTATAWA MUTANENSA KAMAR YADDA SMART YA YI A CIKIN KWANAKI UKUN NAN, YANZU YA FAHIMCI ZAFI DA ZALUNCI A KAN AL'UMMA BAYA HAIFAR DA SOYAYYA SAI DAI SU YI MAKA BIYAYYA DAN DOLE BA DAN SUNA SO BA, KUMA HAKAN BA KARAMAR ABU BANE, DAN DIK RANAR DA SUKA SAMU WATA YAR DAMA ZASU YI MAKA BORE NE HAR SU FARMAKA MA, DAN HAKA SAMUN SOYAYYAR MUTANE YANA SAMUWA NE DAGA LOKACIN DA KA KULA DA SU KULA MAI TSAFTA, YA SAMU KARIN HASKE SOSAI, BA SHAKKA ZUWAN SMART BABBAN HASKE NE A GARESA.
(Yanzu kun gane dalilin da yasa Big Bro ya sume tsawon 3 days? Kuna tinanin a lokacin ɗaya in bai ga aiki a aikace ba zai yarda ya dai'na zaluntar mutanen birninsa ne? Kuna tinanin zai dai'na kwace masu ƴaƴa ta karfi da ya ji ne? Wannan dalilin yasa muka yi amfani da ƙwaƙwalwa wajen jinginesa ya suma na ɗan lokaci, sannan yanzu kunga zai ji daɗin kasancewar Smart a tare da shi har ma ya yi alfahari, wannan plan ta yi kuma ta mun sugar.🥱)
Yanzu ya gama fahimtar komai, kuma ya ji yana son taimakawa King Zuhair. Ajiyar zuciya a bayyane ya sauke kafin ya juyo da kallonsa a kanta. "Dogon labarin ne alaƙarku da Kamran, but sooner or later zan faɗa maki". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannu ya ɗan matsar da dogon gashin da ya zubo saman face ɗinta yana hana mashi ganin kyakkyawar face ɗin nata da kyau. Bafa ya gajiya da kallon yarinyar nan ko kaɗan, kome ta yi burgesa take yi, wata ƴar karama da ita a gabansa.
"To shikenan, yanzu mu je ka ci abinci". Yarinya mai hankali, bata jayayya da maganar manya, dik da a matuƙar ƙagare da son jin alaƙarta da Kamran da take yi, bata ja da maganarsa ba da ya ce ko ba jima ko ba daɗe zai faɗa mata, ta hakura ta taushi zuciyarta. (AMMA AKWAI SHEGEN NEMAN TSOKANA 😺)
"Kina son in ci abinci ne?". Da sauri ta gyaɗa mashi kai. "Ke kinci ne?". Nan ma kai ta gyaɗa mashi kafin ta shiga bashi labarin yadda Smart ya tsaresu sai da suka ci abinci suka ƙoshi sannan ya kyalesu.