← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 130

Sashe 75

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kun tuna wani katafaren waje da na taɓa magana a kai wanda dik jumma'a ake tsere da dawakai a wajen? Kun tuna filin? To wannan fili Big Bro yasa a baje komai a fitar da tsarin palace irin nasa a wajen, ya buƙaci da a kawo masu gold, da su za'ayi kwalliyar ginin ma, yadda dai ya narka dukiya a nasa ginin haka zai yi wa mahaifinsa.

Abin da ya yi mugun É—aurewa Smart kai shi ne hadda Big Bro ya ce nan da kwana talatin ya bada su kammala wanna ginin, mamaki Smart yake yi a kan ta yaya za'a gama ginin nan a 30 days, bayan ba gini na wasa ya ce ayi ba, hawa goma daidai kamar sabon palace É—insa na Black World, yaushe aka fara bare a gama?. To amma nasa dai ido shi kam.

Bayan ya kammala wayar ne ya miƙawa Smart wayansa ya nufi waje. Da kallo Smart ya bisa har ya fice sannan ya dawo da kallonsa a kan Pretty da barci ya yi awon gaba da ita. Toilet Smart ya wuce dan ya ɗauro alwala lokacin yin sallah ta yi.

Zaune a zaman dadduma Big Bro ya isko Sweetie, tana sanye da dogon hijabi har kasa, ta idar da sallar mangariba. Sai kallon hijabin nata yake yi, bai taɓa kallo hijabi a zahiri ba, sai a media, kun san yadda birnin nasa take, do yasan hijabi, a zahiri ne bai taɓa gani ba.

Saman bed ya wuce ya kwanta yana cigaba da kallonta, while ita kuma bata tashi a wajen ba har sai da lokacin sallar ishai ya yi, ta yi sallah sanan ta miƙe bayan tayi addu'ointa. Cire hijabin ta yi, ta naɗesa da kyau, hijabin Auta ta je ta ɗauko dama, sai yau ta san ta yi sallah mai kyau da natsuwa ga cikken sutura.

Waje ta nufa ba tare da ta yi mashi magana ba, har zata buɗe door ta fita muryarsa ya katseta da cewa. "Ina zaki je?". A natse ta juyo. "Momma ce tace idan na yi sallah in zo in ɗauka maka abinci".......... Shiru bai sake yin magana ba, kai tasa ta fice waje. Ajiyar zuciya ya sauke yana tinano irin yadda Pretty ke kashe Smart da shagwaɓa, wannan abin ya tsaya mashi a rai, ita dai Sweetie a sanyayye take magana babu wani shagwaɓa.

Jim kaɗan ta dawo ɗauke da kayan abincin, yana jin yunwa sosai hakan yasa bai ɓata lokaci wajen saukowa kasa dan su ci ba. Ko da ta buɗe abincin, irin cimarsu ne, su texmari spagh da su kali-jeera, amma sam bai yi mashi ba, dan yana da zaɓen abinci sosai shi, a kowani rana yana da ra'ayin abin da yake ci, amma tin da yana jin yunwa, sai ya daure ya ce ta zuba mashi su ci. A natse ta zuba masu suka hau ci tana ta aikin satar kallonsa. Wlh ba ƙaramin tafiya da imaninta yake yi ba a lokacin da yake motsa kyawawan lips ɗinsa, sai ta ji tamkar ta mashi sumbata a wajen. Shi ma nasa ɓangaren satar kallonta kawai yake yi, ji yake yi tamkar ya jawota jikinsa.

A ɗayan ɓangare kuwa, shi ma dai Ronnie bai iya cin abincin kingdom ɗin ba, domin kuwa amai ya rinƙa zabgawa tamkar babu gobe, guyson ne ya taimaka mashi da kyar, kuma ya faɗawa momma shi ma Safras bai iya cin abincinsu ba, momma tasa aka kwashi kayan abincin aka fitar da shi waje, da mom Smart ta girkawa su Big Bro sai momma ta sanya aka sakawa Ronnie.

Kun fahimci dalilin da yasa shi Smart da Pretty basu yi korafi kan cimar Black World ba? Saboda shi yasaba cin irinsu a Paris, kunga Pretty ma ta saba ci a tare da shi a can, sannan abin da ya sa Smart ya iya cin abincin larabawa time da ya zo kingdom É—in shi ne daddynsa na Paris balarabe ne in baku manta ba, yayan momma ne, so ya taso ana girka ciman larabawa time to time, dan haka ya iya cin ciman dikka biyu shi kam.

----------------------------🔥

Bayan sun kammala Sweeeti ta ce bari ta kira kuyangu su tattare wajen, shi kuma ya miƙe ya koma saman bed ya kwanta.

A haka ta dawo tare da kuyangu suka zo suka gyare wajen tsab suka fita. Zama ta yi a saman sofa tana tinanin irin rayuwar da zasu yi a tare a wannan É—akin kenan sai suka ji knocking na door.

Kallon juna suka yi kafin su mayar da kallonsu a kan kofar. Zata yi magana ya ɗan yi mata gyaran murya alamar bai yarda ta yi magana ba, (wai irin kada wani ya ji mashi voice ɗinta, amma fa in jini😸) hakan yasa ta yi shiru. Miƙewa ya yi ya nufi door ɗin da kansa. Yana buɗewa sai ya ga Smart ne tsaye cikin sleeping dress masu balain kyau, mamaki ne ya kama shi na ganin Smart na knocking, wai meyasa zai yi knocking ba zai shigo kai tsaye ba?. Wato addinin musulunci duniya ne jama'a, ya za'ayi ka shiga ɗakin mutumin da kake ikirarin yana da mata kai tsaye ya shige masu ciki without their're permission? Wannan ai sai rayuwar dabbobi.

Kallon tsab Smart ya yi mashi kafin ya ce. "ALLAH yasa ban katse wani abin ba, dan naga yanayinka sai a slow"......... Shiru Big Bro bai amsa mashi ba, yana dai kallonsa.

"Yanagaka haka ne wai? Naga kamar kana cikin maye ne? Ko dai kana kan network ne?". Smart da neman tsokana ya sake tambaya.

Sai yanzu Big Bro ya gane nufinsa, dan haka sai ya kai mashi duka a shoulder, in a cool way sosai ya ce. "Ai ni ba irinka bane".
Ɗan leƙowa cikin ɗakin Smart ya yi wai dan ya tabbatar Sweetie bata jinsu kafin ya ce. "Shiyasa ranar na tarar kana mafarkin sisterta har da cewa ta cigaba da maka wasa da shi kada ta daina ko? To kai wani irin ne kenan?".

Shi ma Big Bro satar kallon cikin É—akin ta wutsiyar ido ya yi kafin ya ce. "Fita mana a É—aki". Ya faÉ—i hakan ne saboda ya ga Sweetie tana kallonsu, ita ma da gulma so take yi wai ta ga wanene ya yi knocking.

"Dama ai ni ba zama zan yi ba, ina zan zauna in ga abin da zai hanani barci bayan yar tsana ba iya mun komai zata yi ba, ni dai yanzu abin da ya kawoni shi ne ka zo mu je wajen daddy kafin mu yi barci".

Sosai Big Bro ya ji daÉ—in cewa zasu je wajen King, dan yana son sake ganin daddyn nasa. "One minute". Big Bro ya faÉ—a ba tare da ya jira amsarsa ba ya saki kofar ya koma ciki. Smart da tsona ya ce. "Zaka iya É—aukar five mins ma dan naga alamar sai ka huce".

ÆŠan jinjina kai Big Bro ya yi irin zan kamaka É—in nan, jan kofar Smart ya yi ya rufe masu ya tsaya a gefe yana jiransa. Kusa da Sweetie Big Bro ya tsaya, in a cool way sosai ya ce. "Kada ki fita ko nan da door, ko knocking aka yi kada ki buÉ—e". Cikin bada umarni ya yi maganar yadda kuka san shi ya ajiyeta.

Ita kuwa da yake soyayyarsa ya rufe mata ido farincikinsa kawai take so sai ta ce. "Okey In Sha ALLAH". Kamar zai rungumeta ya bata kiss yadda ta motsa lips É—in nan nata, amma sai ya daure tare da juyawa ya nufi waje.

Smart na tsaye yana jiransa, yana zuwa suka wuce part na king. Suna tafiya sai tsokanar Big Bro Smart yake yi, wai har yanzu bananarsa a tsaye take, dan haka dan ALLAH ya rinƙa sassautawa sister ɗinsu dan yarinya ce, kada ya je ya kasheta. Sarai Smart ya san Sweetie bata yi kama da wadda aka yi dis virgin ɗinta ba, amma saboda neman tsokana ne yasa yake yi mashi wannan tsiya.

Shi dai Big Bro bai yi magana ba, har suka isa bedroom na King. Kwance saman bed suka isko King Ramish yana zaune a gefensa suna É—an hira. Hayewa saman bed É—in suka yi suma, cikin girmamawa Ramish ya É—agawa Big Bro gaisuwa da turanci. Da kalma É—aya ya amsawa Ramish, wannan ma sai da ya É—auki one minute kafin ta amsa.

Haka ya sake É—agawa Smart ma gaisuwa, nan ma Smart ya amsa cike da kauna. Da kallo É—aya Big Bro ya yi wa Ramish ya ji ya kwanta mashi a rai, haka kawai ya tsinci kansa da kaunarsa, shi ma Ramish ya ji yana kaunar yayan nasa sosai.

"ALLAH ya yi maku albarka ƴaƴana". King ya faɗa cikin raunin murya. Smart da Ramish ne suka amsa da amin, shi kuma Big Bro sai ya ce. "Daddy meyasa ruhanan tsafi suka sanya ka kwanta jinya haka? Meyasa suka rike maka dikkan gaɓɓan jiki? Shin ka ci wani bashinsu ne baka biya ba?". DUM!! DUM. Haka kirjin King ya bada bugu, while Ramish da Smart kuma suka kalli juna.

Shi kuwa Big Bro ya kai hannu ya ɗan riko hannayen King cikin nasa, lokaci guda King ya ji tamkar an kwashe mashi dik wata ciwon dake a jikinsa, saboda waɗan nan yatsun Big Bro da ya bar dogayen nails ɗin sun taɓa mashi tafin hannu, dik wasu ruhanan sun gudu, a miliyan suka saki King suka watse. Da karfi King ya yunkura ya miƙe tamkar wanda aka karawa karfi.

Ai cike da mamaki Smart ya ce. "Big Bro me yake faruwa? Mekake son cewa?".......... Shiru bai amsawa Smart ba, kallonsa a kan dad da ya miƙe zaune ya ce. "Daddy menene yasa suka yi maka wannan mummunar riko haka? Akwai wani dill da ya haɗaku ne?".
Chapter 75 · 0% Book details