Sashe 37
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ude yana tsaye jikin bed É—in tsirara yana kallonsu, amma su basa iya kallansa, ya sha madarar mamakin ganin yadda Hoorain ya shigo cikin É—akin, bai san cewa dik karfin tsafi banza ce a idanun addu'a, yaron mamma fa daga masallaci ya fito, ga shi azumi suka wuni da shi, ya yi sallah ya yi karatun Alqur'ani mai girma, sannan ya yi askar, ai dole nema ya iya buÉ—e kofar nan ya shigo.
Cikin kuka Auta ta fara bubbuga kirjinsa tana faÉ—a mashi dik abin da ya faru da ita daga farko har zuwa yanzu da take rungume da shi.
Ude ya so toshe bakinta a kan kada ta faÉ—a, sai dai ya gagara yin hakan saboda tana jikin Hoorain yaro jiki dik addu'a, dole yana ji yana gani ta faÉ—i komai.
Tin da ta fara magana gabaÉ—aya yanayin Hoorain ya canza, to me zai faru? Wai kun manta Hoorain da zafin kishi ne? Jaish da yake matsayin yayanta ma ranan da ya mareta ba shakesa ya yi a cikin fada gaban kowa ba? Kun manta yadda ya tsawatarwa uncle Taheer rike hannun Auta? Kun manta yadda ya kare da wancan guy da ya biyo Auta a lokacin walimar da mummyn Chuchu ta haÉ—a? Mutumin da tin bashi da tabbacin kai baima sa a ransa zai mallaketa ba yake tsananin kishinta haka bare kuma ace ta zama matarsa, tana cikin É—akinsa sannan wani ya zo ya ce zai keta mutumcinta ku yi tinanin Hoorain zai barsa? Tab ai ina ga ko ubansa na gaskiya ne ba zai raga mashi ba bare na boge.
Tsabar ɓacin rai wani irin kerma jikinsa ta fara yi, gabaɗaya tsuma yake yi tamkar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka yake ji, idanunsa a take suka canza launi suka yi jajir kamar wuta, tsantsar ɓacin rai ne ya bayyana a kan fuskarsa, shi da aurenta da Abdussalam ma ya kasa shanyewa sai da ya tambayeta Abdussalam ya taɓata ko? Bare yanzu! Ai rabata da jikinsa ya yi, ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, cikin wata iriyar murya wadda da ka jita zaka san da kyar aka ƙaƙalota za'ayi maganar da ita.
"Ya taɓaki ne?". Ya faɗa yana mai da kallonsa ƙasa, dan ya fahimci ta razana sosai da ganin yanayinsa, so kada ya ƙara ɗaga mata hankali cikin wanda take a ciki. Girgiza kai ta shiga yi. "A'a bai taɓani ba". Ta faɗa tana wani irin shessheka. "Wanene shi?". TASHIN SENSE.
Ita kam waye zata ce tin da bata san kamanninsa na ainahi ba! A suffar Hoorain ya zo mata, bata san wanene bane, kai ta shiga girgizawa kafin ta ce. "Ban san shi ba, amma koma wanenen matsafi ne sosai, saboda yadda ya fito a siffarka ya zo nan".
Shiru Hoorain ya yi, lokaci guda ya tina da abin da ya faru dashi a ranar da kuma in da ya ɗauko Fanan, dan haka koma wanene yana da alaƙa da wannan waje da ya ɗauko Fanan kenan. Sake Auta ya yi tare da yunƙurawa zai sauko ƙasa ya nufi waje, dan ya yi alkawari koma uban waye, ko wuta yake tauna ya haɗiye dan bala'i yau babu mai kwatarsa daga azaban da zai yi mashi, ba zai ɗagawa kowa kafa ba.
Ihu Auta ta zunduma mashi da karfi tare da cewa. "My Hero ina jin tsoro, kada ka tafi ka barni, wlh zai sake dawowa, na shiga ukuna ni kam".
Tamkar ba zai tsaya ya saurareta ba, dan idan ransa ya kai miliyan to ya ɓaci, amma tinawa da ya yi cewa ga yadda ta rabu da iyayenta da ƴan uwanta dik saboda shi, sai ya ga bai kamata ya barta tana kuka ba, kuma ya yi mata alkawarin ba zai bari ta yi kuka ba, wannan dalilin yasa ya dakata tare da zuba mata ido yana sauke wani irin huci tamkar zai kama da wuta.
A karfi ta faɗa jikinsa tana kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Dik zafin da ya ɗauka sai ya ji kukanta na neman wanka mashi, dole ya danne zuciyarsa ya hau rarrashinta, tin tana kuka da karfi har ta koma yi a hankali-hankali, daga karshe ma sai ta yi shiru tana daka hamma alamar barci. Cikin magagin barci can ƙasa ƙasa ta ce. "My Hero barci nike ji sosai, dan ALLAH ko na yi barci kada ka fita ka barni ni kaɗai, ka zauna a tare da ni".
Kyakkyawan arab hairnta ya shafa yana gangarowa har tsakiyar bayanta kafin ya ce. "Babu in da zan je in sake barinki har sai ranar da takobina ta sauke kan wanda ya niyyar zaluntarmu, sai na raba kansa da gangar jikinsa kafin nan ne nima zan iya barci".
Lokacin da ya yi wannan magana har barci ya yi awon gaba da ita, dan haka bata ji bare ta amsa, shiru ya yi yana cigaba da shafa bayanta a hankali yana ɗan yi ƙasa har zuwa kan mazaunanta, tinani ya luluƙa a kan wani mai karan kwanan ne yake neman shiga gonarsa? Lallai dole ya binciko, kuma koma wanenen dole ya kashe shi in ba haka ba zuciyarsa ba zata yafe mashi ba.
Ya jima a haka yana tinani kafin ya dawo da kallonsa a kan hannunsa, bai ma san yana ta shafe mata mazaunai ba, hankalinsa ya yi nisa. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke cikin barci, hakan yasa ya kai ɗan bakinsa ya sumbaci forehead ɗinta, a fili ya ce. "Kin wuci na bar idanunki su rinƙa zubar da kwallah matukar bana farinciki ba, ba zan taɓa barin dik mai shirin cutar dake ya zauna lafiya ba!"
Ya kai karshen maganar tare da kwantar da ita a hankali saman bed ɗin, ya kwaso pillows ya sassaka mata a gefe-gefenta, ya ja duv ya lulluɓa mata, a ransa ya hau tinanin bata ci abinci ba fa. NI KAM NA CE WANNAN UWAR WAHALA DA TA SHA TA TSIRA DA KYAR INA WANI BATU NA CIN ABINCI? AI SAI DA SAFE KUMA.
Sam bai ji daɗin hakan ba, matso da ɗan bakinsa dab da nata ya yi, sumbata ya manna mata tare da ƙoƙarin ɗagowa kenan ya ji tasa hannu ta rungumoshi mai gabaɗaya, cikin magagin barci ta ce. "Ka kwanta a jikina my Hero, bana son ka matsa".
Gefe guda na zuciyarsa ne ta lulluɓa da farinciki, ya ji daɗi sosai har da sauke ajiyar zuciya, gyarawa ya yi ya kwanto a jikinta, a hankali ya juyo da ita ta dawo jikinsa shi kuma ya koma saman mattress, ya ja masu duv ya lulluɓa masu.
Dik Ude yana tsaye yana kallonsu, takaici tamkar ya kashesu dikkansu, saboda yadda yake tsananin katse yana buƙatarta, ya so ace shi ta runguma haka yadda ta yi wa Hoorain, a ransa ya ce da ta samu gata fiye da yadda tsammani zai iya tsammata.
Da kyar Hoorain ya laluɓo remote na light ɗin ɗakin ya kashe wutar ya kunna dim light, sannan ya hau tofa masu addu'oin barci yana ɗan shafe jikinta dan ya rage zafi. Ganin sun kashe wutar ɗakin ne yasa Ude ya fice ya basu waje, dan ya ji ma suna karanto addu'oi yasan ba nasara zai yi ba, sai ya kwashi tsummokaran kayansa ya yi gaba yana ciza laɓɓansa bai samu abin da yake so ba.
Tin yana iya shafeta kaÉ—an-kaÉ—an har barci ta yi awon gaba da shi mai gabaÉ—aya, suna manne da juna, wannan shi ne hanta da jini.
---------------------🔥
Komawa É—akin tsafinsu Ude ya yi, nan ya isko Zarina a tsaye tana jiransa, saman waÉ—an nan jajayen sofa ya zauna yana binta da wani irin kallo, dama cike yake da takaicin bai samu abin da yake so ba, ga Zarina ta zo zata kawo mashi wani ciwon kai.
Tana a tsaye kan kafafunta tana wani irin huci, da alama a fusace take. Yana zama ta dalla mashi wani irin kallo, in a cool way sosai, dan ita wlh baka taɓa jin ta ɗaga murya a magana, ba karya tana da sanyin murya sosai, can ƙasa ta ce. "Amma dai kasan tin ɗazun kai nike jira ko?".
Yana ta hucin takaici ya ce. "Ni kike jira kamar ya? Me zan yi maki?". Sosai ya yi shocked da jin maganarsa, dan ko da wasa bai taɓa yi mata magana irin haka ba, amma sai ta daure da cewa. "Yanzu me abin yi? Ta wace hanya zamu ɓullowa yaron nan domin in koma kan kujerar mulkina......".
Bata karisar da maganar ba ta dakata saboda idanu da ya zaro mata, muryarsa a ɗan dishashe ya ce. "Tab kina tinanin sake komawa kan mulki kenan? Ban kara tabbatarwa ƙwaƙwalwar kifi ne dake ba sai yau!".
Zaro idanu ita ma ta yi da jin kalamansa, kai ta ɗan girgiza kafin ta ce." Ban gane me kake son cewa ba!". Miƙewa tsaye ya yi, cike da gadara ya tako zuwa in da take, sai da ya zagayeta sau biyu kafin ya tsaya a gabanta suna fuskantar juna. "Ba zaki gane me nike son cewa ba ai saboda na faɗa maki ƙwaƙwalwar kifi ne dake, idan ban da dakikanci da jakanci har zaki yi tinanin komawa kan mulki bayan ina raye? Kina tinanin yanda na zauna a saman kujerar da na fi sonsa fiye da komai na fara jin daɗinsa ina moransa sai kawai in sake tashi in bar maki waje ko?".