← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 130

Sashe 127

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Maysh barci kike son hanani ko?". Typing yai ya tura mata. Take sai ga voice É—inta ya dawo mashi. "Uhm uhm ni in yi maka voice kai kuma sai ka mun typing ko? Bayan kuma kasan bana gajiya da son jin voice É—inka, rowa kake mun ni da kayana ko? To ni dai ka mun voice in ba so kake yi in yi kuka ba".

Ai Malam Big Bro tin da ya kunna voice ɗin ya lumshe ido yana jin wani irin azababben sonta yana kara huda zuciyarsa, neman natsuwarsa yai yana faman rasata. In a cool way a fili ya ce. "Maysh kina neman wuce lissafina ki kure hakurina"........ Voice ya danna ya hau bata reply cikin sanyin murya mai narka zuciya...... Lokacin da ya tura mata hannunta har yana kerma wajen ƙoƙarin buɗewa ta ji me ya ce.

A daidai wannan lokaci momma da King suna tsaye a tsakiyar room É—in king, sun yi cirko-cirko, da ka gansu kasan suna cikin tashin hankali. Sai kai komo King yake yi tamkar wanda ya zagi sarkin aljanu watau Big Bro ana nemansa ruwa a jallo a duniyar sama jannati , sai haÉ—a gumi yake yi, momma ma dai gumin nan take haÉ—awa.

To wai me yake faruwa ne kuma?.

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
Abin dake faruwa a nan shi ne, zuwansu Zarina England ashe ba iya zaman meeting kawai suka yi dan haɗa kai da kawo karshen Crown Of Power ba, sun sayo muggan makamai ta karkashin kasa, sannan sun yi gagarumin shiri, dan sun ce Kingdom of Power ba zata yaku gaba da gaba kawai ba, dole sai sun haɗa da su Missiles ta sama dan taimaka masu, shi ne suka sayi muggan makamai irinsu. Cruise Missiles, FOAB watau Father of All Bombs, shi ne mafi girma a cikin makami nau'in bombs da ba su da sinadarin nukiliya, sai Mother of All Bombs watau MOAB, da irinsu Conventional Bombs, JDAMs, GBU, da sauransu. Waɗan nan makamai ana amfani da su sosai cikin yaƙe-yaƙe, kuma suna ɓarna sosai. Ba su da sinadarin nukiliya amma suna iya ruguje manya-manyan gine-gine da filayen sojojin yaki.

To kiran da akai wa King daga Anti-Ballistic Missile Systems office ɗinsu shi ne tin daren jiya suke faman kakkaɓe makaman da su Udey suke harbo masu, da yake su suna da S-400 da S-500, waɗannan manyan makamai ne masu iya harbo missiles har da na nuclear daga nesa sosai, suna daga cikin jerin system mafiya ƙarfi a duniya masu iya tare makamai su hanasu sauka a cikin ƙasa.

Sannan suna da THAAD watau Terminal High Altitude Area Defense, ana amfan da shi wajen harbo makaman ballistic kafin su isa ƙasa.Yana kare ƙasashe da manya-manyan birane. Sai Patriot Missile System, ana amfani da shi wajen harbo makaman da ke tafe a matsakaicin nisa, yana da radar da ke gano harin kafin ya karaso kusa. Shiyasa tin jiya suke ta kakkaɓe makaman basu barsu sun sauƙa a cikin birnin ba.

Abin da ya fi ɗaga hankalin King shi ne su a halin yanzu ma basu da manyan makaman iya mayar da martanin hakan, sai karfin sojojin yake kawai suke da shi wanda za'a iya gwanzawaeda su gaba da gana, tin ainahi sun fi mayar da hankalinsu kan gina addininsu da yake-yake ta karfin sojojin yaki, ko kaɗan basu taɓa damuwa da su nemi makamai dan irin wannan rana ba, shiyasa suka shiga damuwa sosai.

(To komai na rubuta a littafina ko daga book one ne ku ajiye shi a kanku dan yana da amfani, waye ya taɓa zatan aikin Smart zai shigo cikin labarina sosai?🤔 Kun ɗauka kawai haɗa makamai yake yi shi da daddynsa dan jin daɗinsu kuma su samu kuɗi ko? To dan yaki ne wait and see.)

Amma dai yanzu mu faɗawa King cewa ɗansa yana da wannan ilimi ne ko dai mu barsa ya cigaba da shiga damuwa? Dan dai kun san Smart da daddynsa tun farko sun ɓoye wannan batu, a sirrance suke yin kayansu, haihuwa mai daɗi, shi fa King dik ta in da suka zo mashi yana da ɗan da zai tsaya mashi a wannan ɓangaren, shiyasa ni stars na labarina suke da siffa daban-daban, kowanne da kalar aikinsa, yanzu dai idan da tsafi da aljanu suke taƙama muna da Big Bro, idan makaman missiles ne muna da Smart, idan ta jirgin sama zasu yi yakin muna da Ramish air force ne, idan kuma da warriors ne shi ma muna da zaƙwakuran renon Commander Zafar, idan ma mata zasu aiko muna da su Aunty MieMie, idan karfi gwamnati zasu nuna mana muna da uncle Abbas, ɗan siyasa ne, idan taimakon wata ƙasa zasu nema to shi Big Bro ta ko'ina nemansa ake yi da ya haɗa kawance da su dan su zo su kwashe mashi tattalin arzikin kasa su bashi muggan makamai da tsaro, to a faɗa mana me ba mu tara ba? Shiyasa dik aikin da star na labarinan yake yi da amfaninta, ba kawai ina basu aiki dan suna bane, a'a kowa da amfaninsa, aikin da zan yi amfani da shi nike sakawa!!.

---------------------🔥

Sosai momma ta shiga damuwa dan tana tsoron kada makaman nan a samu akasi su faɗo cikin birninsu, zai yi ɓarna, za'a rasa rayuka da dukiya. Suna cikin wannan jimami da tashin hankali ga can uban nuclear yana tsaye a gaban mirror ɗin Big Bro yana kallon kansa, ya fito daga wanka, Big Bro ya ce ya zo su kwana a ɗaki ɗaya tin da momma ta ce ko kallon Pretty bata yarda ya je yi ba, shi ne Big Bro to su je ɗakinsa kawai su kwana tin da momma dik ta tattare masu mata ta rike.

"Rahilarh menene mafita a wannan al'amari dake tinkaromu ko in ce ya tinkaromu?". King ne ya yi maganar a cike da damuwa. Momma da gabaÉ—aya ta fara karaya ne ta amsa mashi da. "To yanzu dai sai dai in ce ka tara yaranka ka ji me shawarar da zasu yanke maka ko?".
Shiru King ya É—an yi kafin ya ce. "E zan zauna da su, amma Ramish baya nan ai". Jinjina kai ta yi. "E haka ne baya nan, amma dama ina son yin magana a kan Ramish, yakamata a yi gwajin jini dan yasan mahaifiyarsa, abin da ciwo sosai a ce bai san mahaifiyarsa ba, wlh na san kawaici kawai yake yi maka yake dannewa, amma yana son saninta".

Jinjina kai King ya yi. "Kin yi gaskiya, ai dole ma zai ji ciwo, dole zai so sanin wacce ta haifesa, bari ya dawo zan sa dik a yi gwaji mu gani"...... Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, har cikin ranta take son Ramish, saboda tin farko ya fi ɗaukarta tamkar uwa sama da Mama, baku ga baya ɓoye mata komai nasa ba, ita ya fara nunawa Leesharh, kuma ita ta yi mashi jinyar Aesh ɗin tasa a lokacin da ya yi mata aika-aika, ya fi shakuwa da momma sosai saboda kyan halinta, kun san kowa ya zo gidan ma ya fi shakuwa da ita sosai.

"Idan ALLAH ya kaimu da safe ki haÉ—o mun kan Æ´aÆ´ana manyan zamu yi zama da su kafin Ramish ya dawo, shi ma ya ce yana nan tafe In Sha ALLAH".

Da okey Momma ta amsa mashi kafin ta wuce ta haye saman bed É—insa ta kwanta, dan wani marayan jiri take ji, tana son faÉ—a mashi abin da yake gudana a kan Big Bro, amma gabanta har faÉ—uwa yake yi idan ta tina babban É—anta ba musulmi bane, abin ya tsaya mata a rai over, kuma ga wani irin magana da yake yi wai shi ba zai yarda da addininsu ba su ma kada su yarda da nashi idan sun yi ra'ayi, ta shiga damuwa sosai.

King ya lura da tana cikin damuwa, amma ya É—auka a kan yakin da ya tinkarosu ne, dan haka sai ya hau gadon dan rarrashinta ya kwantar mata da hankali.

A gefe guda kuwa Smart ya gama shirinsa cikin sleep kaftan ne ya zo ya samu Big Bro zaune a saman sofa yana chat da Queen of his heart. "Yakamata mu yi taking dinner blood". Smart ya faÉ—a yana kallonsa.

ÆŠan haÉ—e rai yai. "Ba zan iya ci ba sai Maysh ta zo, na saba ci da ita a tare".......... Cikin zolaya Smart ya ce. "To É—aukeni a matsayinta". Harara Big Bro ya dallah mashi kafin ya ce. "Bata da madadi ai".

"A'a nima ban ce ai mata madadi ba, kawai mu je zan baka a baki, dan nasan bai wuce haka take yi maka ba". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ja hannun Big Bro, dan dole yasa shi ya miƙe suka nufi wajen abincin.

Zama suka yi, Smart ya zuba masu a plate É—aya, ya sanya masu two spoon, Big Bro yana ta faman dannar waya Smart ya É—ebo abinci a spoon ya kai mashi saitin É—an bakinsa yana faÉ—in. "Bismillahir-rahmanir-rahim".

Aikuwa Big Bro ya buɗe baki zai karɓa jin abin da Smart ya ce yasa ya fasa karɓa, ya ce. "Ba zan ci abincin ba". Ya faɗa tare da yunkurawa zai miƙe. Da sauri Smart ya rikesa yana faɗin. "Sorry na manta ka ce baka son addininmu, to zauna ba zan sake ba".
Chapter 127 · 0% Book details