← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 130

Sashe 4

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A natse ya hau saka kayan yana tinanin ai ranar Zunairarsa ta ji daÉ—i da ta gansa da irin wannan shiga, dan haka ko dan ta yi farinciki zai sanya. Haka ya hau sakawa yana tinanin yadda zai sameta........... Ya ilahi, ya yi fitina a cikin waÉ—an nan kaya, ya yi tsantsar kyau. Yana tsaye yana bin kansa da kallo sai ji ya yi uncle É—insa ya hau tattare mashi gashi ta baya, É—an rage tsawonsa kaÉ—an ya kara yi domin ya baiwa uncle É—in nasa damar gyara mashi gashin da kyau, dan kusan tsawonsu É—aya da Rishan É—in.

Kamar wani É—an yaro haka Rishan ya mayar da Hoorain a yau, da kansa ya gyara mashi gashi ya feshesa da tsadaddun hair perfumes masu kamshin daÉ—i, yana gyarasa yana faÉ—in. "You're our Prince, ba zan zuba maka idanu ba, saboda na ga kai baka É—aukar abubuwa serious".

Shi dai ya É—an yi kasa da kai, kamar mai tinanin wani abin. Sosai Rishan ya gyara mashi gashi ya É—aure a tsakiya kamar yadda al'adar Koreans take, sannan ya ja jelar gashin ya murÉ—eta ya kewaye É—aurin da ya yi mashi da ita, a karshe ya sanya pil ya kame gashin da ita!.

Ya sake binsa da perfumes masu kamshin kwantar da hankali. Shi kansa Rishan yasan Hoonaira ya yi fitina a yau, dole Zunaira ta ruÉ—e. Wani kyakkyawan Rose Rishan ya bashi haÉ—e da wani karamun box of chocolate kafin ya ce. "Good night my son". Ya faÉ—a tare da nufar toilet dan ya je ya yi wanka shi ma.

Har zai shiga toilet É—in sai ya ji Hoorain ya kira sunansa. Juyowa ya yi yana É—aga mashi gera guda alamar lafiya?. Da sauri Hoorain ya nufosa, yana zuwa ya tungumesa kafin ya ce. "I really love you my one and only uncle"..... Shafa bayansa Rishan ya yi haÉ—e da cewa. "Love you to my first son my first love". Ya kai karshen maganar tare da raba jikinsu, sannan ya ce da Hoorain ya je yunwa na damun Auta.

Da sauri ya juya yana mai jin tsananin kaunar uncle É—in nasa, ya nufi waje. Yana fita suka ci karo da Rishma, dama shi ta zo nema, dan Auta dai taki cin komai, ta ce sai ya dawo zasu ci abincin a tare, shi ne ta zo duba shi. Cikin girmamawa ya É—aga mata gaisuwa kafin ya tambayi ina Auta, a natse ta amsa mashi da tana É—aki tana jiransa.

A dai'dai wannan lokacin shi kuma Ude yana can yana kai komo a cikin bedroom ɗinsa, ya gama tsuma, surar jikin Auta ne kawai ya tsaya mashi a rai, ya kwaɗaitu da ita ainun, faɗi yake yi ko ta wani hali ne sai ya sami Auta, ko da rayuka zasu salwanta, sai ya ɗanɗani yarinyar nan!. Tinani yake yi ta yadda zai je mata ta aminta da shi ba wata gardama, can wata zuciya ta ce ya tsafeta, ya sanya zuciyarta a kwalba zata yarda da shi. Kai ya girgiza alamar wannan shawa bata yi mashi ba. Shiru ya ɗan yi, ya sake natsawa cikin tinaninsa. Can kuma wani ɓangare na zuciyarsa ya ce to me zai hana ya shiga siffar Hoorain ta tsafi, hakan zai sanya ta yi balai'n aminta da shi, zai samu sex mai daɗi da ita, dan zata zaci Hoorain ne sai ta sallama mashi kanta.

Na'am ya yi da wannan shawara, dan haka sai ya fara tsara da wani lokaci zai je mata?!.

Shi kuwa Hoorain sallama suka yi shi da Rishma, ta wuce ciki wajen Rishan shi kuma ya nufi bedroom É—insa. A natse yake takawa, gabaÉ—aya a matse yake da son ganinta, amma dik da haka sai da ya fara zuwa in da Kamran ke kwance yana jinya ya duba shi kafin ya nufeta.

Tana tsaye a jikin window, ta yaye curtain tana kallan harabar kingdom É—in, sanye take da wani figaggen riga wanda ya tsaya mata a iya gwiwowinta, rigar ya yi bala'in yi mata kyau, ga shi very silky haka, yau sarauniya Rishma da kanta ta je ta yi mata sayayyar kaya sosai, daga ciki ne ta sanya wannan sleeping dress É—in, ta yi fitina a cikin kayan.

ÆŠan dakatawa ya yi a tsakiyar bedroom É—in yana kallonta cike da zallar kauna, ko kaÉ—an bata ji shigowarsa ba, hankalinta ya yi nisa wajen tinanin ina ya tafi to? Ga shi daga ita har shi babu waya a hannunsu, and bata san number Rishan ba bare ta kirasa ta tambayesa ina yake ko da wayar waye ne. Sai dai ta ji bugawar zuciyarta alamar yana kusa kenan!.

Wani musulmin ajiyar zuciya ya sauke, hankali ya kwanta ya ɗaura idanunsa a kanta. Takowa ya yi step biyu, sai kuma ya ɗan dakata ganin tana ɗan ɗaga kai kamar zata juyo, ƙamshin perfume ɗinsa ne ya daki kofofin hancinta shiyasa ta ɗan ɗaga kai tana shaka. Ganin bata juyo bane yasa ya kara lallaɓawa a hankali.

Unexpected ta ji saukar hannunsa a saman shafaffen cikinta game da kwanto da kansa a saman shoulder É—inta, kamshin dake jikin dogon arabs hairnta ya fara shaka yana É—an lumshe idanu.

"Sai yanzu zaka dawo?". Ta faÉ—a tana turo baki. Juyo da ita ya yi suna fuskantar juna tare da gyara tsayuwarsa, ya tsaya da kyau kafin ya ce. "Sorry my Hoonairata". Ya yi maganar yana É—aura hannunsa É—aya a saman mazaunanta ta baya.

Ture shi ta yi game da cewa. "Ban hakura ba, kuma fushi nike yi da kai". Ta kai karshen maganar tare da wuce, ta raɓa gefensa izuwa saman bed. Binta da kallo ya yi yana jin wani irin musulmin yanayi na shigarsa, yadda take tafiya tamkar bata son taka ƙasa, kai ka ce da gangan take yi mashi irin wannan tafiya, dik tasa ya rasa natsuwarsa.

Hayewa saman bed ta yi tare da jawo pillow ta ɗaura a saman lap ɗinta, ba tare da ta kalli in da yake ba ta kifa kanta a jikin pillown. A ransa ya ce kome ta yi kyau yake yi mata, dama idan mace bata da rigima ai namiji ka auro ba mace ba, har cikin ransa ya ji wani musulmin daɗi ta lulluɓesa na rigimar da ta yi mashi, mace da rigima aka santa. A natse ya taka izuwa in da take domin yin rarrashi. Yana zuwa ya zaune a gefen bed ɗin.

Yatsun hannunsa ya kyasta mata wanda hakan yasa ta ɗago da kanta, slowly ya kwantar da nasa kan a in da ta ɗaga nata, a saman laps ɗinta kenan, yana kallon face ɗinta yacce take faman turo baki. Ƙasa sosai ya yi da murya, cikin wata iriyar murya da bai taɓa yin magana da ita ga kowa ba a rayuwarsa ya ce. "Ba zan ce Hoonaira ta yi hakuri ba, amma zan ce ta yi mun purnishment ɗin da ya dace dani, saboda nasan ban kyauta ba, yakamata ace na dawo da wuri domin in bata dinner, amma na barta da yunwa". Yana magana yana kallan face ɗinta.

Cikin dabara take satar kallon kayan jikinsa, bata san yana kallonta ba, kayan sun yi matuƙar yi mashi kyau over, sai ta ji dik wani fushinta ya gudu, dama rigima ce kawai irin tata.
Hannunta ta É—aura a saman massive chest É—insa dake buÉ—e. "Zan kuwa baka purnishment sosai, dan ni ba zan hakura ba".

ÆŠan limshe idanunsa ya yi jin saukar hannunta a wajen, slowly ya sake warosu a kan face É—inta. "Kowani purnishment in dai daga Hoonairata ce, zan yi farincikin yinsa". Ya faÉ—a yana juyo da jikinsa gabaÉ—aya gareta.

Slowly ta ɗan yi mashi kamar tafiyar maciji da hannunta daga kirji zuwa wuya zuwa face ɗinsa, lallausan kumatunsa ta ɗan shafa kafin ta ce. "Ka yi kyau sosai my hero, kayan sun yi maka kyau and........... ". Sai kuma ta yi shiru. While shi ma shiru ya yi yana sauraronta, sai a lokacin kuma ya tina ya bar rose and chocolate da Rishan ya bashi a ɗakin da Kamran yake. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Saboda ke na sanyasu, and ke kaɗai na yiwa kwalliyar, and menene kuma? Karisa faɗi in ji". Ya faɗa muryarsa na ɗan sarkewa, saboda yadda take taɓa shi har cikin ransa yake ji!.

Siririn murmushi ta yi kafin ta ce. "A'a babu komai, ka dai yi kyau".......... "Please my Hoonaira, and menene?". Cike da matsuwar san jin amsar da zata bashi, tabbas ya karanci kasan harshenta, so take yi ta ce and lips É—insa sun yi bala'in yi mata kyau yanzu, amma sai ta fasa faÉ—i, sam bai ji daÉ—i ba, ya so ta faÉ—a, dan shi ma dai ba laifi yana son bawa flowers ruwa in dai da ita ne!.

"Kai my hero, in kana son in faÉ—a ka dai'na kallona to"....... Slowly ya rufe idanunsa yana faÉ—in. "Na dai'na kallanki. FaÉ—a mun to".

Uhm kalaman Risham ne suka dawo cikin kunnenta, na cewa kada ta taɓa jin kunyarsa tin da mijinta ne, tana tsananin sonsa, kuma shi ma yana sonta, kada ta yarda da wani kauyanci wai jin kunyarsa, ta kula da abinta ta yadda zata kara gina soyayyarta a ransa ba wai ta tsaya kunya da shirme ta rushe ginin soyayyar da ya yi tun farko ba, dayawan mata daga wannan waje suke ruguje ginin soyayyar da mazajensu suka yi masu tun farko, a maimakon su karawa ginin ƙargo sai shirmensu yasa su rushesa su kuma dawo suna danasani!. RISHMA BATA SAN DAMA ITA AUTA ƳAR LOVE BACE, TANA SON HOORAIN, KUMA BATA TAƁA ƁOYEWA A KO'INA TANA SON SHI, TO TIN DA TA TSUGUNNA A GABAN GABAƊAYA FAMILY TANA RIƘON KING TANA FAƊA MASHI TANA SON HOORAIN AI DAGA NAN YAKAMATA KUSAN BA KARAMUN SO TAKE YI MASHI BA WANDA BATA IYA ƁOYEWA! KO A GABAN WAYE ZATA IYA FAƊA!.
Chapter 4 · 0% Book details