← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 130

Sashe 70

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A natse suka miƙe suka bi bayanta, parlon ya rage daga Jaish, Smart sai Big Bro. Cikin zolaya Smart ya ce. "Ko dai nima ina baku waje ne shalelen momma?". Harara Big Bro ya watsa mashi yana rarraba yatsun hannun momma da ya rike. Zoben da Jaish ya sanya mata kwanaki Big Bro ya zare daga yatsunta, dan ya ga zoben ya ɗan kamata har ya zana mata shati a yatsun nata. Da ya cire zoben ma sai ya hau shafa in da zoben ta zana zanenta kaman yana son cewa momma sorry, amma bai yi magana ba.

"Momma akwai tarin abubuwa sosai a wannan kingdom ɗin, daga zuwana na fahimci hakan, waɗan can yara guda biyu masu kama ɗaya kuma masu yanayi da mu ɗin nan ƴaƴan waye?". Cewar Big Bro da yake magana a kan su Omaid, wlh ba zaka taɓa zatah Big Bro ya kalli jama'ar da suka zo cikin parlon king ba, amma tsab ya kallesu ta idon da su basu sani ba, sannan dik ko yanzu ya gansu zai ganesu. Kun san fa idan magic da magic suka haɗu abin ya zama family issues ne ta bayan fage, kuma in har mai karfin tsafi kamar Big Bro ya bayyana a waje to dik kananan nan zai iya zaƙulosu. JAMA'A KU CE WA SU MAMMIE GA UBANSU YA ISO!.

Smart ya yi mamakin jin yadda ya yi tambaya a kan su Omaid.

Momma tana kallon dogayen yatsun Big Bro ta amsa mashi da. "Brothers É—inku ne, daga su sai autarku mace wacce ke aure a Crown of Justice". Ta kai karshen maganar tare da kai É—ayan hannunta ta riko yatsun Big Bro tana kallo, shi harta yatsun hannunsa ya fita daban da na sauran yaranta, dogaye da su, ga shi kuma a babban yatsansa na hannu da karamin ya bar farce nails mai tsawo sosai, sauran yatsun nasa kuma ya yanke nails É—in. Ta yi mamakin ganin yadda yatsun nasa suke, ga su da balain kyau, farare tas tamkar madara, suna wani kyalli suna glowing.

"Shikenan tin kannena ne, ni zan gyara komai da kaina". Ya faÉ—a yana É—ago da kallonsa a kan Jaish da yake ta faman binsu da kallo.
"Da wani abin ne? Ko sun aikata wani abin ne?". Smart ne ya tambaya.

"Dama ai su kullum cikin aikata laifuka suke, dan dik mutum irinsu baya son zaman lafiya". Big Bro ya bada amsa. Da sauri Jaish ya ce. "Ai idan ka ce aikata laifuka ma ka faÉ—i kaÉ—a, waÉ—an nan yara sai addu'a".

Momma dai sun saka ta a duhu, dan haka sai ta ce. "To ni dai ba zan shiga tsakaninku ba, yanzu dai kuje ku yi wanka kuzo ku ci abinci shi ne damuwata". Ko kaɗan bata damu ba, dan tana ji a jikinta Big Bro zai kula da kannen nasa matuƙa.

"Momma bana son in bar part ɗinki, a nan nike son room". Cewar Big Bro. "Meyasa ba zaka je tare da ɗan uwanka ba?". Momma ta tambaya. Sake yatsun hannunta ya yi tare da gyara zama kafin ya ce. "Kingdom ɗin nan ya mun kaɗan, a takure nike, amma idan ina part ɗinki kina tare dani zan rinƙa jin tamkar a sarari in da babu ginin komai nike".

Sosai momma ta ji mugu-mugun daÉ—in kalamansa, hakan yasa ta ce. "Akwai É—akuna guda uku dake babu kowa a nan, ka É—auki É—aya.......". Katseta ya É—an yi da cewa. "ÆŠaya mafi kusa dake ba".

Kyakkyawan murmushi ta saki kafin ta kai hannu ta shafi lallausan kumatunsa. "ALLAH ya yi maku albarka dikkanku".

Smart and Jaish ne suka amsa da Amin ban da Big Bro, momma bata lura da bai amsa ba, ta É—an kara shafan kumatunsa tana jin tamkar ta mai da shi cikinta dan tsantsar so da kauna.

Miƙewa Smart ya yi tare da cewa. "Bari in duba mana ɗakin da ya fi kyau guda biyu, Jaish ka shigo da kayanmu, suna cikin bayan motocin da suka ɗaukomu". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi wani siririn corredor wacce ɗakunan suke ta wajen. A nan ya zaɓawa Big Bro guda ɗaya shi ma ya zaɓi guda ɗaya, dama baya son zama a part ɗin Jaish.

Dawowa ya yi ya zo ya rike hannun Big Bro suka nufi room ɗin. Da kallon kauna momma ta bisu har suka kurewa ganinta, sannan ne ta miƙe ta nufi ɗakin Mahreen dan ta ga su Sweetie da kyau.

Zaune ta iskosu a saman bed, Sweetie ta buga uban tagumi tana tinanin Big Bro, ita kuwa Pretty ta tada kai da cinyar Mahnoor suna É—an hira, dama su kunga sun san juna, Sweetie ce bakuwa.

Mahreen kuwa ta matsa sai shafa kyakkyawan gashin Sweetie take yi tana tambayarta me ta shafawa kan nata ya zama kala haka mai balain kyau? Wai ita ma zata shafawa nata ne. Kun san tin da Mahreen ta ga Sweetie ta rikice, taga madarar kyau, kuma babban abin da yasa Mahreen ɗin ta kaunaci Sweetie shi ne gashin kantan nan dai mai balain ɗaukar hankalin nan da kowa yake santinsa har Big Bro, sai taɓa mata kai take yi tana karawa.

Da Sweetie ta ce mata babu abin da ta shafa gashin ne yake a haka, sai Mahreen ta ce to zasu zama kawaye? Kun san mutuniyar da son gayu, to ta ga Sweetie yar caras cas shi ne ta manne mata, tin É—azun take ta faman shafa mata gashi tana watsawa, dik wani É—auri da Sweetie ta yi wa gashinta sai da Mahreen ta warwaresa tsab ta hau watsa mata gashin. Ita kuwa ta buga tagumi tana jin zuciyarta na yi mata zafi saboda abin da Big Bro yake yi mata.

Jin sallamar momma yasa dik suka kai kallonsu a kanta, har suna haɗe baki wajen amsa mata sallamar. A kusa da Sweetie ta zauna tana kallon fuskarta. "Ƴata lafiya kuwa? Naga kamar tin da kuka zo baki a cikin mood mai daɗi".

Ƙaƙalo murmushi Sweetie ta yi. "Babu komai Momma, kawai kaina ne yake ɗan ciwo". Momma zata sake yin magana Pretty ta rigata da cewa. "Karya take yi maki momma, faɗa suka yi da mijin nata tin kafin muzo, Yah Omerish ne ya bata shawarar ta daina yi wa Big Bro magana, shi ne ta daina yi mashi magana, shi kuma abin ya ɓata mashi rai ya bar masu gidan gabaɗaya, daga baya suka yi ta nemansa har suka gaji, kwana uku baya tare da mu, da zamu zo nan ma ina ganinsa wani jirgi daban ya hau ba namu ba, kuma ya rigamu sauka a nan, to shi ne har yanzu basu shirya ba". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa zaune.

Sosai momma ta ji daɗin yadda yakasance Sweetie tana da sirri da natsuwa, wato tana kokarin rufawa mijinta asiri, abin ya burge. Kallon tsab momma ɗin ta yi wa Sweetie kafin ta ce. "Ni mahaifiyarki ce, kada ki koyi ɓoye mun komai kin ji? Kada ki kalli mijinki matsayin ɗana kice zaki ɗaukeni a surkuwa, uwa nike a wajenku dikka, dik abin da ya yi maki ki faɗa mun kada ki sake ɓoyewa, yanzu faɗa mun abin da ya faru dallah dallah".

Ƙasa ta yi da kanta, bata so faɗa ba amma sai ta ce. "Dama ranar ne ya shake mun wuya saboda na yi maganar wani namiji, to a ranar Yah Omerish ne ya rabamu faɗa, shi ne sai ya ce Big Bro bai san daidai da ba daidai ba a wani lokaci, kuma shi bai san ya yi kuskure ya bada hakuri ba, dan haka in nuna na yi fushi da shi in janye daga garesa har sai ya gane yana yin kuskure ya koyi bada hakuri, to shi ne shi kuma ya ji abin da muƙa faɗa sai ya yi fushi damu tin kan mu mu yi fushi da shi". Ta kai karshen maganar hawaye suna cika mata ido, ALLAH SARKI ITA BATA SAN ME SOYAYYA BA SAI A KANSA, ZUCIYARTA BA ZATA IYA JURAN HUKUNCINSA NA KIN YI MATA MAGANA BA!.

Momma ta gama fahimtar komai, murmushi irin nasu na manya ta yi kafin ta ce. "Kin yi ganganci kuma shi ma Omerish ya yi gangancin shiga tsakanin mata da miji, meyasa zaki bi shawarar wani a kan mijinki? Koma me ya yi maki ai mijinki ne, kin fi kowa sanin halinsa, kin san yadda zaki bi da shi ya koyi gane kuskurensa, kin san yadda zaki yi mashi ya koyi bada hakuri ba sai kin yi fushi da shi ba, ke ba mace bace? Mu fa mata dik girman namiji a tafin hannunmu yake, kina da hanyoyi da dama na horasa ba sai ta fushi ba, fushi da miji yana rusa soyayya sosai, kada ki sake yin fushi da shi, zan koya maki hanyar horasa cikin ruwan sanyi, batu na karshe kuma shi ne kishi a jininmu take tin daga kan iyaye da kakanni, ko da sunan wasa kada ki sake yin maganar wani namiji a gabansa, in ba haka ba bana jin akwai mai iya karɓarki ta daɗi a hannunsa". Ta ɗan dakata tana kallon fuskokinsu yadda suka tsareta da ido.

"Da na ce ku zo dining mu haɗu mu ci abinci, to tin da hakan ya faru kowacce ta kaiwa mijinta abincinsa ɗaki dan ku gyara alaƙarku, zuwa dare zan yi magana dake". Ta kai karshen maganar tana sanya hannu ta sharewa Sweetie hawaye. "Kada ki yi kuka, nan gidan farinciki kika zo, gida ne da suka san darajar ɗan Adam, gida ne na masu kima da sanin yakamata, ki saki jiki ni mahaifiyarku ce gabaɗaya". Tana kai karshen maganar ta jawota jikinta. A hankali ta hau rarrashinta tana shafa bayanta har sai da Sweetie ta sauke nannauyar ajiyar zuciya alamar ta huce kenan.

"To tashi ku yi wanka bari in baki kayan Zunaira ki saka, dan zai yi maku daidai".

Tamkar Sweetie zata ce mata sun zo da kayansu, amma sai ta yi shiru saboda tana son dik wani abin da zai fito daga hannun wannan golden heart É—in, momma ta wuci mai golden heart ma ai.
Chapter 70 · 0% Book details