← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 130

Sashe 28

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin sai wani irin huci mai bala'in zafin gaske Black Tiger yake fitarwa tamkar zai kama da wuta ne yasa ta kara matsawa kusa da shi. Hannu ta ɗaura saitin Lion chest ɗinsa, kamar zata taɓa saitin zuciyarsa sai kuma ta ɗan fara shafa wajen, in a cool way sosai ta fara faɗin. "Cool down our Big Bro, cool down please, zafin ya yi yawa, yi sanyi haka kada zuciyar nan ta fashe, bamu son wannan black heart ɗin Big Bro, yana wahalar mana da kai, please ka kwatanta yakicesa ka gefar ka ji?". Cikin sigar rarrashi ta yi maganar, tana cigaba da shafa saitin zuciyarsa.

Lokaci guda suka ji a bayyane ya sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya almar black heart É—in ta fara sauka kenan, da gaske ya fara cooling down É—in fa, ALLAH mai iko mai yin yadda ya so, yanzu da a baya ne kuna tinanin Sweetien ta isa tasa black heart ya yi cool? Ai da tana nufo shi da ita dik zai haÉ—e ya turmushe.

Smart dai yanzu kamar kansa ta kulle kamar kuma bata kulle ba, ya ma rasa gane a wani hali yake a ciki kuma me yakamata ya yi?.

Cigaba Sweetie ta yi da shafa kirjinsa tana faÉ—a mashi cool words masu kwantar da hankali, ita sam bata gasgata Smart gaske bane, ta barsa matsayin almara ko shashatau shiyasa bata bi ta kansa ba.

Almost 5 mins sukena haka kafin Black Tiger ya sake sauke wata nannauyar ajiyar zuciya mai sauti sosai alamar ya sauka gabaɗaya, hannunsa ya kai ya riƙo nata dake a saman kirjin nasa, bai iya ce mata ko uppan ba, ya ƙanƙame hannunta kamar zai mayar cikin nasa.... ALLAH YA FI GABAN WASA, ALMOST 2 YEARS SWEETIE TANA ADDU'A ALLAH YA SASSAUTA BLACK TIGER AI DOLE MA YA YI SAUKI, ADDU'A BATA FAƊUWA KASA BANZA SAI DAI JINKIRIN AMSAWA!!.

Da dai Smart ya ga waÉ—an nan ba kula shi zasu yi ba sai ya ce bari shi ya kulasu, sun tsaya sun tsare juna da kallo ko kaÉ—an basu iya kyafta idanu, dan suna ganin kamar da zarar sun kyafta idanu za'a nemi É—aya daga cikin a rasa, wato za'a É—auke É—aya, shiyasa suka mace da ganin juna babu kyaftawa.

Yanzu Smart ya gama fahimtar cewa Sweetie tana da alaƙa mai karfi a tsakaninsu da ɗan uwansa da kuma ƴar tsanarsa, sannan ya gano cewa idan har ana son nasara a kan Black Tiger to fa a haɗa hannu da Sweetie, kun san mutanen da kaifin basira, a cikin idanun Black Tiger ya karanci cewa Sweetie tana da mahimmanci a wajensa, kuma ya gani a zahiri yadda ta taushesa cikin lokacin da bai fi minti goma ba ya sauko, abin ya ɗan sanya Smart a kokwanto da tinanin wacece ita?.

Gyaran murya ya ɗan yi masu wanda yasa dikkansu suka yi saurin janye idanunsu daga cikin na juna, a hanzarce Black Tiger ya zame hannunsa daga riƙon da ya yi mata yana wani ɗan dojewa kamar yana jin kunyar Smart kamar kuma ita yake jin kunya, yana wani ɗan sunkuyar da kansa ƙasa.

Ita kuma zabura ta yi game da matsawa kusa da Smart ta kara kusanci da Black Tiger, a razane tana zazzaro idanu ta ce. "Big Bro ka cire mun wannan almara da ka saka mun É—in, saboda yana bani tsoro, kamansa da kai yana gigitani". Words É—inta gabaÉ—aya haÉ—ewa suke yi a lokacin da ta yi wannan magana.

Slowly ya ɗago da kallonsa a kanta, in a cool way sosai tamkar mai raɗa ya ce. "You means that kema kina ganin kamata da tasa? Kenan ba saka kamannin ya yi dan ya shiga rayuwata ba?". BALA'IN WATO SHI BLACK TIGER YA ƊAUKA KAMANANNIN FUSKARSA SMART YA SAKA DOMIN YA YI KAMA DA SHI YA SHIGA RAYUWARSA, LALLAI BLACK TIGER BAI SHIRYA KARƁARSU MATSAYIN ƳAN UWA BA MA KENAN, TAB ƊI JAM!!.

"Big Bro wannan ai sak kai ne, ALLAH kuwa babu wani banbanci, please ka ɓatar da almarar mana, ban son ganinsa, yana rikitani sosai dan ban taɓa gani kama irin haka a zahiri ba".

Tana gama rufe baki sai ga Pretty da Ronnie, ya je ya kwakulota a kan lallai ta zo ta ga mai kama da yayansa, wato Ronnie fa ruɗewa ya yi, ya ga abin da bai taɓa gani ba, sai ya rasa me zai yi shi ne ya je ya kirasu. Ta sha kwalliyarta cikin irin kayan da Sweetie ta sanya a farko kafin robot ɗin can ya ɓata mata kayan, ta yi bala'in kyau. Ai tin daga kan yadda ta bar gashin kanta a buɗe Smart Tiger ya gane ga yar tsanarsa, tana wani turo baki ita a dole Ronnie ya ɓata mata rai da ya sanyata fitowa, da kyar ya samu ta zo, dan ta ce ita barci zata yi ba zata fita ba.

Nan fa shi ma Smart ya É—an ruÉ—e ya shiga rarraba eyeballs É—insa a kan face É—insu, ya kalli Pretty dake a saman bene ya wurga ido ya kalli Sweetie dake a gabansa tana korawa Black Tiger bayanin irin kamar dake a tsakaninsa da Smart.

Yanzu Smart ya gama fahimtar kamar yadda yake da Black Tiger haka ita ma Æ´ar tsanarsa take da wannan mai golden white hair É—in, take ya ji hankalinsa ya yi wani irin Musulmin kwanciya, da a tinaninsa ai juyar mashi da hankalin Æ´ar tsana aka yi ta mance da shi, sai yanzu ya gano gaskiya.

Ai Pretty na sauke kallanta a kan Smart ta zaro idanunta waje, dan kunga bata iya wani banbantasu da Black Tiger, in baku manta ba ta É—auka ma Black Tiger shi ne Smart, so bama ta mayar da hankali a kan Black Tiger da Sweetie dake tsaye a wajen suna magana ba, tana zuwa kawai a kan Smart ta sauke kallonta. Ai da gudu ta fara tattaka staircase É—in game da É—an É—aga rigarta dake jan kaya.

Tana saukowa da gudun gaske ta yi kansa tana turo baki na shagwaɓa, juyowa gareta da kyau ya yi, ya buɗe mata hannayensa, tana zuwa da gudun gaske ta faɗa jikinsa. Wani irin lumshe idanunsa ya yi tare da ɗagata sama ya manna da Lion chest ɗinsa yana sauke sanyayyar ajiyar zuciya mai Musulmin daɗi.

Da sauri Sweetie and Big Bro suka wurga eyesballs ɗinsu a kan Pretty da Smart, Sweetie bata san lokacin da ta zaro idanunta waje ba, a razane ta ce. "Ke Pretty kina iya ganinsa ne? Kin san shi ne?". A matuƙar rikice ta yi maganar.

Ɗago kai daga jikin Smart Pretty ta yi, cike da shagwaɓa ta ce. "Wannan ai shi ne mutumin da na baki labari jiya, wanda na ce maki ya hanani yi wa Kamran ɗin mu magana".

A wani irin miliyan Sweetie ta dawo da kallonta a kan Black Tiger. "Dama ba almara bane? Dama gaske ne?".
Kai ya jinjina mata, lokaci guda ta É—auke wuta diff ta yi sumar tsaye saboda razana, ita dai Pretty yarinya kamar mai motsi a kai, wlh ko a jikinta da ta É—ago ta kalli Black Tiger, ba wani razanar da ta yi, bai yi mata kamar ta ga wani abin mamaki bama, kun fa san mutuniyar abin da yake a gabanta kawai take yi, babu ruwanta da shiga wani hurumin, dai haka sai ta mayar da kanta saman gefen wuyarsa wajen shoulder É—insa ta kwanta.

Shi dai Ronnie ya tsaya a saman bene yana kallon ikon God yau, kansa ta kulle da wanna alamari.

Slowly Big Bro ya ɗan motsa lips ɗinsa tamkar suna yi mashi ciwo, can ƙasan maƙoshinsa ya kira Sweetie da wani sunan da su Smart basu iya jin me ya faɗa ba, ni kai'na ban ji me ya ce ba, tinani ma nike yi wai dama ya san sunanta ne ko dai da bai san sunanta ba sai ya raɗa mata wani nashi daban?.

Shiru bata motsa ba, kamar gunki take tsaye idanunta a kan Smart. Lokaci guda Black Tiger ya É—an ji wani abin ta tsikari zuciyarsa, hannu yasa ya jawota jikinsa yana cigaba da ambatar wannan suna da ya ki buÉ—e murya kowa ya jisa.

Smart ne ya dawo da kallonsa a kansu, cikin sanyin murya ya ce. "I think suma fa ta yi, bakaga bata breathing bane?".

Wani irin harara Black Tiger ya dalla mashi har sai da Smart ya ji makoshinsa ta bushe yana buƙatar shan ruwa, ba tare da Black Tiger ɗin ya kalli in da yake ba cikin natsuwa sosai tamkar baya son yin magana ya ce. "Me kuma zaka ce mun bayan kai ka nuna mata wannan fuskar taka kasa ta suman?!".

Maganar Big Bro ta sanya Ronnie dake a tsaye murmushi, wato Black Tiger na daban ne, ga iya yin magana a dunkule, ga shi muryarsa mai shegiyar tsada ne da in ya yi magana har tsayawa ake yi ko zai kara yi, sai ayi magana goma bai amsa ɗaya ba, bugu da ƙari muryar tasa shegen daɗi ga sanyi da matsuwa a cikinta.

Ajiyar zuciya Smart ya sauke, ba karamun daɗi ya ji ba na yadda Black Tiger ya yi mashi magana, bai taɓa mashi magana a tausashe haka ba, infact bai ma saurarensa ai...... gaskiya a yau da Sweetie da Ronnie sun shiga ruɗani sosai. Amma kuma yadda Big Bro ya yi wa Smart magana a yanzu fa kamar zuciyar Big Bro ɗin ta fara saduda tana ƙoƙarin rungumar kaddararsa.

Shi dai Smart koba komai ya yi murna yau É—an uwansa ya bashi amsa a natse da taushi.

"Ba laifina bane ai, amma amun afuwa ba zan kara razana maka Heartbeat ba, bari ma in samo ruwa..........". Smart bai iya kai karshen maganar ba sakamakon wani irin kallo da Black Tiger ya jefa mashi wanda ya sanya shi haÉ—iyar sauran zancen, ba komai yasa ya yi mashi wannan kallo ba kuma face yadda ya kira Sweetie da heartbeat É—insa, sai ka ce ya ce mashi hakan take a wajensa.
Chapter 28 · 0% Book details