← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 130

Sashe 100

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyaran murya king ya yi kafin ya canza masu topic na magana da cewa. "Bari in baku sauran labarin dana fara". Tsaida kallonsu dikka a kansa suka yi, shi kuma kallon Big Bro yake yi yana ƙoƙarin karyata zuciyarsa a kan ɗan nasa yana tsafi, yana son tilasta zuciyarsa ta yarda baya tsafi kawai dai ilimi ne.

Cigaba ya yi da cewa. "Akka tana da yara guda bakwai ba mu uku da kuka sani ba, kafin ni akwai maza biyu, bayan Abbas akwai mace ɗaya, sannan bayan Jahiz ma akwai mace ɗaya wanda tin tana da shekaru 7 ALLAH ya karɓi abarsa, cikin brothers ɗina biyu da nike da su, ɗaya tin ranar da aka haifesa ya ɓata wanda nike zargin mahaifina ne ya sace ɗansa da kansa, na biyun kuma an haifesa da sati guda shi ma ya rasu, sai ni, daga ni sai Abbas sannan sister ɗinmu mace mai suna Zunaira wanda mahaifinmu ya aurawa King Abdul Raof ita (kakansu Leesharh) sai dai kuma ashe ba auren tsakani da ALLAH ya yi mata ba, domin kuwa kasheta suka yi, da ya yi mata aure dai sun nuna so da kauna, sun kula da ita sosai har ALLAH ya bata ciki, sun tarairayi cikin suka yi renonsa cikin kulawa har ya kai wata bakwai, to a nan ne suka ɗauketa zuwa blood power, suka cuccusa mata magungunar tsafinsu a baki, amma sai da suka yi mata asirin da ko motsi bata iyawa, idanunta dai biyu tana ganin komai sai dai bata da abin da zata iya yi, suka zuba mata magunguna a baki, babu imani babu tausayi suka ɗinke bakinta kafin su tona rami mai zurfi, da ranta suka sakata cikin ramin, ga bakinta sun ɗinke cike da magunguna, sannan suka binneta a wajen da tsohon cikinta, Blood Power suka ce mun wanna abin da suka yi ya zama gagarumin abin da yasa masarautun biyu suka kara karfin iko, dan babu jarumin da ya taɓa irin wannan sadaukarwa sai mahaifina, shiyasa a lokacin mulkinsa dik balainka Kingdom ɗin nan tafi karfin ka nunata da yatsa saboda karfin mulki, wane mutum, iyayenmu sun yi son ransu a lokacin da suke kan mulki, sisterta ta tafi ta barni da ciwon kewarta a zuciyata, na gagara mantawa da ita a rayuwata, lokacin da Blood Power suka bani wannan labari, ba dan karfin tauhidi ba, wlh da sai kwakwalwata ta taɓu, saboda dik cikinmu babu wanda ya kaini shakuwa da sisterta, a lokacin da ta samu ciki har cewa take yi zata yi mun takwara idan namiji ta haifa, ina ta murna, bana taɓa yin sati biyu ban je evil kingdom dubata ba, dik dan in ganta, mun shaku da ita sosai, rana ɗaya kawai aka ce wai ta rasu saboda ciwon ciki, hankalina ya yi mummunar tashi, har suma na yi a lokacin, da na fargaɗo na ce a cire mun ɗan dake cikinta kada abine ta da shi, sai aka ce ai anrigada an binneta, wlh haukane kawai ban yi ba a lokacin, na sha jinya, kullum na zauna sai na tinata, mace mai fara'a da son jama'a yadda kuka ga Zunaira, shiyasa na sanyawa Zunaira sunanta, halinsu iri ɗaya ne, suka kasheta suka ce mutuwa ta yi daga ciwon ciki, amma ina zuwa Blood Power suka ce mun ai ba mutuwa haka kawai ta yi ba, ga abin da babana da Abdul Raof suka yi, su suka kasheta, to ta ya kuke tinanin ba zan yaki waɗan nan masarautu ba? Meyasa ba zan tsani jinin waɗan nan masarautu ba? Dole tasa na ce Ramish ya rabu da matarsa, saboda na tsani jininsu, na yi masu tsana mafi muni a rayuwata, bana son haɗa jini da su! Omranish, Herry, Abdul Raof, Abdul Malik dik na tsanesu, kuma na yi bakincikin zuwana a jinin Abdul Malik, dole in yakesu, kuma muddin basu daina tsafi ba, billahil lazi ba zan ragawa kowa daga cikinsu ba sai dai in mutu, sun cuceni, sun zalunceni, sun binne mun sister mafi soyuwa a gareni da ranta, da ranta ma da tsohon ciki a jikinta, baya ga haka sun sanyani na salwantar da yarana guda biyu ina ji ina gani, sun mun tabon da bazan taɓa mantawa ba kuma ba zan taɓa yafewa ba, yaki yanzu aka fara, babu gudu babu ja da baya muddin ina raye! Alkawari na ɗauka! Jinin Zunaira ba zai tafi a banza ba, sai na karar da gabaɗaya zuriar Abdul Raof da kuma Omranish, wannan dalilin yasa na ce Zunaira ba zata shiga cikinsu ba, saboda nasan zasu yi amfani da ita dan su dakatar dani, kuma nasan zasu azabtar da ita, zata fanshi laifina da ba ita ta aikata ba kuma bata san na aikata ba, kuma kasancewarta a cikin kingdom ɗinsu zai sanya in ji jikina ya mutu a kai masu hari, dan zan ji tsoron kada harin ya shafeta, amma dik cikinku babu wanda ya iya fahimtar cewa ni uba ne na gari, kuma ba zan taɓa kin abin da ƴata take so ba matukar bai kaucewa faɗar ALLAH ba, kuka tsaya a kaina kuna faɗin ina san cutar da rayuwar ƴata da kaina, a lokacin bana son buɗe baki in faɗa maku gaskiya ne saboda alƙawarinmu da Blood Power".

Ya ɗan dakata yana huci, idanunsa sun yi jajir suna zubar da kwallah masu zafi, ya tuna da sistersa Zunaira, ciwo mafi zafi a zuciya, kai King ya shanye abubuwa dayawa a rayuwarsa bawan ALLAH'N nan, kunga kuwa dole ayi ta gwabza yaki babu gudu babu ja da baya, dole king ya yaki family ɗin waɗan nan three kingdom ɗin, dole ya tsani jininsu, sun yi mashi mummunar tabo a cikin rayuwarsa da ba zata taɓa gogewa ba, wlh karfin tauhidi da yarda da ALLAH ne yasa har yanzu king yake tsaye a kan kafafunsa, da ya jima da mutuwa bawan ALLAH.

Tsit cikin É—akin ya yi, dik black heart na Big Bro sai da ya ji tausayin daddyn nasu yakama shi, saboda akwai tsananin zafi rasa wanda ka shaku da shi, sarashi É—in ma ba ta hanyar ALLAH ba, kai dole king ya yi yaki, an zaluncesa over to over.......... Smart kam shiru ya yi yana tinanin lokacin da ya tsaya lallai sai Auta ta bi Hoorain, ashe King ya fi su gaskiya, shi yasan irin gabar dake tsakaninsu dole ya hana Auta zuwa in da suke, ALLAH sarki.

Shi ma Ramish yanzu ya daina ganin laifin daddyn nasa na cewa da ya yi ya saki Leesharh, ashe ya fisu gaskiya, sai dai kuma ai su jikokin three kingdoms É—in basu da laifi, su basu san komai ba, hasalima su basu rayu a kingdoms É—in ba, Leesharh ta rayu a Dubai, Zash ya rayu a Paris, Hoorain a kingdom of Power, Kamran a Forest, su Sweetie suma a forest, sannan Sweetie Black World, Pretty kingdom of power, su Bobo a Paris, sadauki Rishan ne kawai ya rayu a kingdom É—insu, shi ma kuma yaro ne da bai san mafarin gabar ba, daga sama ya tsinci gabar. TO BABA KING A TAIMAKA A YI WA JIKOKI AFUWA, DAN BASU DA LAIFI, MUN SAN ANYI MAKA BA DAIDAI BA, AN KUNTATA MAKA, AMMA MU KUNGIYAR HANA RUWA GUDU NA BIG BRO MUNA NEMAN YAFIYA DA A YAFEWA JIKOKIN NAN, A BARSU DA MASOYANSU, IYAYEN KUMA MU MUN AMINTA A CIGABA DA GWABZA YAKI DA SU HAR SAI SUN ZUBDA MAKAMAI SUN AMINTA ZASU DAINA ABIN DA SUKE YI!!.

"Dad ka daina tuna baya, dan zai iya affecting heart É—inka, ka bar storyn nan haka ya isa, bama son jin saura, as from today, matsayina na first born É—inka, ina cewa kada ka sake yin magana a kansu, ka koma gefe ka yi shiru, ka bar mana yakin, zamu karisa abin da ka fara, dan lokacin daina kukanka ya yi, lokacin da za'a É—auka maka ainahin fansa ya yi". Cewar Big Bro da ya yi magana in a cool way sosai, ya kuma yita yana sharewa King kwallah.

Cikin natsuwa ya sake cewa. "Dole zasu tako har cikin nan su durkushe a gabanka su baka hakuri, dole zasu zubda makaman yaki, dole zasu koma karkashin kingdom ɗinka, daga yau kai zaka rinƙa basu umarni kafin gudanar da mulkinsu, ka haifi zakuna masu tare maka faɗa kuma masu share maka kwallah".

Matsawa King ya yi ya rungumi Big Bro yana zuba masu ruwan albarka. Matsawa su Smart suma suka yi suka rungumesu suna amsawa da Amin.

After 5 mins suka raba jikinsu dana King suna kallonsa. Cikin sanyin murya king ya ce. "Inai maku addu'ar nasara a ko yaushe Æ´aÆ´ana, Omerish É—auki wayata ka ce kowa na family ya zo yanzu".

Jinjina kai Smart ya yi tare da ɗauko wayar, sannan ya shiga kiran numbers ɗin matan gidan kafin ya kira su Uncle Abbas dik ya ce su zo. Shi kuma Big Bro ya kalli Ramish, in a cool way sosai ya ce. "Ramish ina buƙatar wayoyi guda biyu da sim card ɗinku na nan yanzu a daren nan"...... Jinjina kai Ramish ya yi kafin ya ce. "To in kawo mai registar ya yi maka kenan?". Kai ya girgiza kafin ya ce. "A'a ka yi komai kamar nine a wajen, ai ba wani amfani da wayoyi zan yi ba, just kawai kafin in koma ne".

Sosai Ramish ya ji daÉ—i yadda yayan nasa ya aminta da shi har yake cewa ya yi komai madadinsa, wannan abu ya mashi daÉ—i.

Kafin 10 mins room na King ya cika da family, dik sun zo har da su Sareena.

GabaÉ—ayansu a saman shinfiÉ—ar king suka zazzauna, su momma a saman sofas dake wajen yaran kuma saman rug na gashin jimmina, iya Big Bro, Smart and Ramish ne kasai suka zauna a saman bed tare da King.

Takaici tamkar zai kashe mama, sai dallawa Momma harara take yi, Mama fa idan ta ga su Big Bro ji take yi tamkar ta shake momma ta kasheta kowa ma ya huta, kuma daɗin abin dake bata haushi shi ne yadda momma take matsayin yar uwar king, ta kara jin hasada a wannan ɓangaren ma.
Chapter 100 · 0% Book details