← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 130

Sashe 24

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ji daɗin maganarta sosai, dama wayau ya yi mata ya bugi cikinta domin ya ji shin tana damuwa a kan halin da suke ciki ne ko kuwa, yanzu ya gane cewa ta fawwalawa ALLAH komai kenan, ya ji daɗin hakan sosai. Gyara zamansa da kyau ya yi game da ware kafafunsa, ya miƙesu, slowly ya kwanto da kansa a saman laps ɗinta yana mai ɗago da kallonsa a kansa. Wani irin Musulmin daɗi ya ji da suka haɗa idanu, ai mancewa ya yi da wata kunya suka kafe juna da kallo, take idanunsu suka sarkafe, kallo mai cike da sirrikar dake ɓoye a cikin zuciya suke aikawa junansu. Hannu tasa ta fara shafa kyakkyawan Koreans hair ɗinsa dake kyalli sosai yana ɗaukar ido kasancewarsa golden white.

Slowly ta É—an shafo kyakkyawa kuma lallausan kumatunsa dake ta faman glowing. "Ina sonka sosai mijina, ina sonka soyayyar da baki ba zai iya faÉ—anta ba, nasan kana sona, dan wani lokaci ina mamakin irin son da kake yi mun, sai in ga kamar bana yi maka ko kwatansa, ban ta shi sanin ka yi haukar sona ba sai lokacin da na shiga É—akinka baka nan".

Ɗan zaro Koreans eyes ɗin nan nasa ya yi kafin ya ce. "Dama kin taɓa zuwa room ɗina bana nan ne?". Kai ta jinjina mashi before ta ɗaura da cewa. "E na taɓa zuwa, babu kowa a ciki, na kuma yi sa'a kofar a buɗe, nan na shiga na fara binciken ɗik abin da kake ɓoye mun, hotunana tin ina jaririya, abin hannuna da ya taɓa tsinkewa a garden, harta rigarka da ka taɓa ɗaure mun hannu da shi sai da ka yi mashi ajiya mai kyau saboda jini dake jiki, dik wani abin da ya shafeni ajiya na musamman kake yi mashi, ni kam nasan idan na ce na fi kowa dace ma bai faɗi cikakke yadda ya dace ba, baki ba zai iya faɗar girman son da kake mun ba, abu ɗaya zan iya cewa shi ne ALLAH ya bani ikon faranta maka har karshen rayuwarmu".

Ai bai san time da ya riƙo hannunta ya ware tafin hannun nata ya manna a kumatunsa ba, a sanyaye sosai ya ce. "Matata ban san me zan yi dan sakaki farinciki ba, komai na yi sai in ga kin wuce hakan nesa ba kusa ba, please ki faɗa mun me kike so yanzu in yi maki?".

Tana kallan tsakiyar kwayar idanunsa ta ce. "Kunyata nike son ka dai'na ji, saboda ina son mu yi soyayya kamar na Yah Jawad and Aunty Chuchu, kai kuma sai ka ce kana jin kunyata".

Shiru ya ɗan yi, a ransa yake faɗin. "Ina jin kunyarki, amma ba yacce kika zata har can sosai ba, kawai dai ina tsananin tausaya maki ne yasa ko da wasa bana son haɗa ido dake ko wani abin da zai tayarmun da hankalina ya sa na gagara controlling ɗin kai'na a kanki, bana son baki wahala a yanzu, saboda nasan kin yi ƙankanta, abin da nike gudun maki kenan ba wai ina jin kunyarki sosai har haka bane, amma tin da ke da kanki kika nemi da na ajiye kunyar, In Sha ALLAH na ajiyeta, dik kuma ranar da na gagara rike kai'na to bani da bakin furta sorry ma kam".

A fili kuma ce mata ya yi. "Na yi alkawarin na cire kunyar daga yau"......... Uhm rashin sani ya fi dare, cike da murna ta É—an ja dogon hancinsa tana murmushi, sunkuyowa kansa kaÉ—an ta yi game da manna mashi sumbata a kumatu, É—an limshe idanu ya yi ya sake warosu a kanta. "Ba dan ina azumi ba ai da yanzu na ce muje É—aki dan ki tabbatar da na dai'na jin kunyar".

Kara faɗaɗa murmushinta ta yi, hannu ta kai ta fara ɓalle botir na wuyar rigarsa. "Yanzu fa ni a gida ba kowa ya san fuskar mijina ba, saboda tin tasowanka baka buɗe fuska, na kamu da sonka ban san face ɗinka ba, kai my Hero kai ɗin na daban ne". "Kamar yacce kike ta daban ba, mai soyayyar gaskiya, kin kamu da san mutumin da baki sani ba, mutumin da yakasance mai tsaronki, bodyguard ɗinki da baki san ya yake ba, gaskiya kece ainahin ta daban, garani ina kallan face ɗinki tin kina jaririya, amma ke ko sauɗaya baki taɓa ganina ba har ALLAH ya mallakamun zuciyar zinarin nan.

Tana jin daɗi sosai a dik lokacin da mijin nata yake yaba mata, sanyi na ratsa zuciyarta sosai. Haka suka ƙasance cikin tsantsar farinciki har lokacin buɗa baki ya yi, miƙewa ya yi ya ɗauketa cak a kan su shiga ciki, kuka ta saka mashi kan lallai ya sauketa tana jin kunyar su Ude, sai dai bai kulata ba dan ya san ba zai haɗu da su a hanya ba, sai da ya kaita bedroom ɗinsu, a saman bed ya zaunar da ita, sannan ya zauna a gefenta, can ƙasan makoshinsa ya ce. "Lokacin buɗa maki ya yi, zan so fara buɗa baki da hot kiss ɗinki a maimakon ruwa". Yana fuskantarta ya faɗa.

"To rufe ido". Ta faɗa tana matsawa kusa da shi. Slowly ya rufe idanun nasa, a hankali ta matsa dab da shi ta ɗan saƙalo wuyarsa kafin ta haɗe fuskokinsu, cikin salo mai jan hankali ta fara bashi hot kiss mai kara rikita ƙwaƙwalwa. Ai bai san time ɗin da ya kara matsawa ya mannata da jikinsa sosai ba, yasa hannu ya tallabo bayanta game da ɗan ɗaga kanta kaɗan ya shiga bata hot kiss mai zafi.

Take ya fara fita daga hayyacinsa, da kyar ya iya jurewa ya raba bakinsa da nata, sannan miƙe da sauri dan lokacin kiran Sallah ta yi, toilet ya nufa, a gurguje ya watsa ruwa ya fito, shiryawa ya yi cikin jallabiya mai kyau da tsada, yana nufar hanyar fita ya ce. "My Hoonaira sai bayan sallar isha'i zan dawo, zamu tsaya yin jam'i da su Papa".

Tana ƙoƙarin saukowa kasan bed ɗin ta amsa mashi da. "ALLAH ya tsare mun kai da tsarewarsa a dik in da kake, ALLAH ya cika maka burinka na alkhairi, ALLAH ya dawo mun da kai lafiya".

Ba dan lokaci ya kure ba da sai ya dawo ya bata hot kiss saboda daÉ—in wannan addu'a da ta yi mashi, amma ya yi alkawarin bata idan ya dawo, yanzu dai sai ya amsa da Amin ya yi gaggawar ficewa. Kasa ta sauko ta shiga toilet dan yin wanka, a gaggauce ta yi ta fito, kaya ta É—auko daga close É—insu ta zo ta hau shiryawa. Sai da ta fito fes sosai, sannan ta sako alkyabbarta dan gabatar da sallah.

Sai dai tana fitowa tsakiyar ɗakin nata a wutsiyar ido ta kalli mutum a tsaye, a hanzarce ta juyo da kallonta a kansa. Lokacin guda ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, a shagwaɓe sosai ta ce. "My Hero ka bani tsoro, me ya dawo da kai bayan ka tafi masjid?".

Cool murmushi ya sakar mata kafin ya ce. "Na gagara tafiya ne yasa na dawo, ba zan iya barinki ba, kewarki ya dawo dani".

Tin daga kan murmushin da ya yi ta fahimci ba shi bane, saboda tin da take da Hoorain bai taɓa murmushi ba ko da wasa, ko abokansa na wasan kasa su Ansar basu taɓa ganin murmushinsa ba, to su ma basa murmushin bare shi, kun tina lokacin da take damunsa ya yi murmushi ya ce mata bai iya ba? To ko da wasa, komai farincikin da zai shiga bai taɓa murmushi ba, hakan ya sa ta shiga mugun shakku game da ɗan zaro idanu tana karewa fuskarsa kallo.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta zaƙulo abubuwa ɗai-ɗai har guda goma da ya banbanta shi da Hoorain, ciki har da kyakkyawan lips da ta yi wa kiss yanzu, na Hoorain ya fi nasa ƙanƙanta nesa ba kusa ba, kuma ya fi nasa kyau nesa ba kusa ba. Ai wani irin razana ta yi, a take jikinta ya fara kerma, kun santa akwai kaifin basira, dan haka sai ta yi amfani da ƙwaƙwalwata bata nuna mashi ta gane ba Hoorain bane, dan tasan idan ta nuna hakan cutar da ita zai, ga shi Hoorain and sadauki Rishan sun ta fi gidan Papa, sun yi nisa kenan. A kaifin ƙwaƙwalwa irin nata da kaifin tinaninta sai ta ga babu abin da ya dace da ita a wannan lokacin face ta ja shi da shiririta har zuwa lokacin dawowar su Hoorain.

Wannan yana É—aga daga cikin wasiyar Manzon ALLAH a garemu, Annabi ya ce a dik lokacin da musifa ta tasowa muminai, lokacin da wata bala'i ta afko masu, to kada su tashi hankalinsu, su natsu domin su san ta in da yakama su fara, natsuwarsu shi zai basu damar tinanin mafita mai kyau, amma idan suka tashi hankalinsu zasu iya zuwa su afka cikin musifar ba tare da sun sani ba. Akwai watarana da Manzon ALLAH suna cikin gida sai suka ji wata kara mai karfi a bayan gari, hankalin mutane ya tashi, sahabbai dik suka firfito dan su je su ga menene? Sai dai kun san me? Suna hanyar zuwa duba menene suka ci karo da Manzon ALLAH har ya je ya duba menene yana hanyar dawowa, sun yi mamaki sosai, yana tafiya cikin natsuwa da kamala babu wani tashin hankali a tattare da shi, so natsuwa a koma ina ne yana daga cikin wasiyar Manzon ALLAH a garemu mu musulmi, ALLAH ka bamu ikon koyi da shi!!.

Ta tsorata ainun, amma ta yi ƙoƙarin dakewa, muryarta har yana sarkewa ta ce. "Amma ai daje ka yi sallar ai sai ka dawo mai gabaɗaya ko?".

Takowa ya fara yi yana nufota sannan ya ce. "Gagara yin hakan na yi ai, ba zan iya yin sallah a cikin natsuwa ba shiyasa gara in dawo in samu natsuwa daga wajenki kafin in yo sallah".. KUNA JIN MAGANARSA KUN SAN BAI ÆŠAUKI SALLAH DA MUHIMMANCI BA SHAIÆŠANI, HOORAIN KUWA AI KUNGA YA ÆŠAUKI SALLAH DA MUHIMMANCI OVER TO OVER.
Chapter 24 · 0% Book details