Sashe 128
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Harara ya dallawa Smart kafin ya koma ya zauna. Cinye wannan spoon da ya ɗebo ya yi ya sake ɗebo mashi wani, a wannan karon sai yai bismillah a cikin ransa kafin ya kawo mashi saitin ɗan bakinsa. Karɓa ya yi ya fara tauna a hankali yana rubutawa Sweetie ta zo ya bata abinci a baki kamar yadda Smart yake bashi. Yau dai har ya koshi Smart ne ya rinƙa bashi a baki, ko sau ɗaya bai taɓa spoon ba, ya zama shalelen Smart ba iya shalelen King kawai ba.
-------------------------🔥
"Maysh, Maysh, Maysh, barci kike son hanani ko? To in na kasa barci kema ba zan bari ki yi ba, dan sai na zo É—akin momma na É—aukeki, sai dai mu kwana a zaune a tare. Yanzu please a hot kiss". Shi ne abin da ya tura mata a voice na É—azun. Jin alamar muryarsa ta sauya sosai kuma wlh tasan idan ya kasa barci tsab zai zo ya tadata ita ma, sai ta nemi canza topic na hirar tasu ta hanyar tambayarsa ina mom É—insu da ya ce zai kawo masu?.
Shiru ya É—an yi kafin yai mata reply da. "Very soon zaki haÉ—u da mom É—inki".......... "Mekafi so a rayuwarka My King?". Ta sake turo mashi. Nan ma shiru ya É—an yi kafin ya ce. "Akwai Yesu, wannan daban ne bana haÉ—a shi da kowa, sannan my cross, Momma and dad, Omerish, Omar, my second mom (Elevender) Ronnie, Maysh, Zunaira dik da ban ganta a kusani da ni ba amma ina sonta, Jaish and twins, abubuwan da nike so suna da yawa kam gaskiya, but waÉ—an nan su ne the most".
Ta yi mamakin ganin abin da ya rubuta, dan haka sai ta ce mashi. "Wanne kafi kauna wanda ba zaka iya rabuwa da su ba?". Kai tsaye ya ce mata. "My cross, momma, Omerish and you, then Omar".
Mugun mamaki ne ya kamata ganin zai iya rabuwa da mutane irinsu Jaish amma ba zai iya rabu da cross ba, a gefe guda kuma ta ji daɗin yadda yake faɗan abin da yake a ransa ba tare da shakka ba, sannan ta ji daɗin yadda yake son momma da Smart, watau su ne ba zai iya rabuwa da su ba. Gaskiya abin ya ƙayatar da ita.
"Wani special gift zaka bani a ranar aurenmu?". Ta rubuta ta turo mashi. Shiru ya É—an yi again kafin ya ce. "Dik abin da kike so". Cike da zolaya ta ce. "Cross É—inka nike so, dan naga kana son shi fiye da komai, in har ina da mahimmanci a rayuwarka to zan so ka bani". Ba da wani manufa tai wannan magana ba, ta yi ne kawai saboda zolaya dan kuma ta ga irin karfin son da yake yi mata.
Tin da ta yi mashi wannan message ɗin bai sake yin reply ba, saboda baya karya, kuma baya son ranta ya ɓaci shiyasa ba zai iya faɗa mata abin da yake shirin fita daga bakinsa a kan wannan Cross ɗin ba, is better ya yi shiru. A wannan shiru da ya yi ne Smart ya zo ya jasa suka wuce wajen cin abinci. Da ya zauna zasu ci abinci sai ya tura mata cewa Smart na bashi abinci a baki, ita ma ta zo ya bata.
Ta ɗan yi mamakin ganin bai bata amsar abin da ta buƙata ba, amma sai ta kawar da zancen dan ita ma dama ba serious take yi ba, zolayarsa kawai take yi, ta biye mashi kawai suka canza topic.
AFTER TWO DAYS.🔥
Acikin waɗan nan kwanaki biyu da suka wuce abubuwa sun faru, ciki har da farfaɗowarsu Omaid, goyson yanzu ya samu cikakkiyar lafiya, kuma ya koma ainahin Omar ɗinsa, sannan su Sareena dik sun farfaɗo, da ta ji cewa ga abin da ya faru da Mammie ɗinta sai hankalinta ya tashi sosai, ta rinƙa kuka momma tana rarrashinta. Aneesa dai ta rabu da aljannun dake kanta, yanzu ta koma ainahin Aneesa yar mama.
A ɓangaren Big Bro kuwa, da kyar ya yarda yai kwana biyu a daddafe ba tare da ita ba, ya kai karshen hakurinsa, ya ce lallai sai dai momma ta bashi matarsa, sai dai kuma a kan hakan kusan ɓatawa suka yi da Smart, dan Smart ya ce idan yana sonta ya musulunta, shi kuma ya ce ba zai musulunta ba, a cikin waɗan nan kwanaki biyun sun sakosa a gaba a kan lallai ya musulunta, shi kuma ya ce ba zai musulunta ba, da Momma taga ba sarki sai ALLAH sai ta sanar da King ga abin da yake faruwa, shi kuwa King da ya kirasa ya ce ya musulunta kai tsaye ya ce shi fa ba zai musulunta ba, kuma su daina yi mashi maganar addininsu ko ya bar masu kingdom ɗinsu.
Da ya faÉ—i haka sai ran King ya É—an sosu, zuciya ta É—ebesa ya ce. "In dai ba zaka musulunta ba babu kai babu auren Omaish, dan musulma sai musulmi!".
Wannan magana ta yi mugun ɓata mashi rai har ya kusa ɗauke King da mari, amma Momma ta dakatar da shi, cikin fushi ya ce. "Babu wanda ya isa ya rabani da ita, zan aureta a gaban idonku ne! Kuma ni ba zan shiga addininku ba! Zan bar maku kingdom ɗinku, Amma sai na auri Omaish a gaban idanunku ku tabbatar da zan iya".
Sosai hankalin momma ya tashi, dan tasan tsab zai aikata, ita wannan lamari ya sake jagule mata, wlh sam ba haka ta so ba, ta so su bi komai ne a hankali, amma king yana neman ɓata komai.
Da ya faÉ—i haka sai King kuma ya ce. "Bazata yarda ta aureka ba, tasan me take yi ai!". Cikin fushi ya ce. "To ka hanata yarda zata aureni in gani!".
Dafe kai momma ta yi tana salati a cikin zuciyarta, shi ma dai Smart shiru ya yi yana salati game da damuwa, dan tin jiya Big Bro bai kula shi ba, tin da Smart ɗin ya ce mashi ya musulunta ko su ɓata, shikenan Big Bro ya ce sun ma ɓata kada ya sake kula shi, ya ɗauka wasa ne, sai ya ga akasin haka, domin kuwa tin jiyan ko ya yi mashi magana baya amsawa, ya bashi hakuri har ya gaji Big Bro yaki kulasa, ya ji babu daɗi, ya ce ya yi danasani, amma dik Big Bro yaki sauraransu. To rikicin da ake ta yi kenan, yau tin safe da wanna rikici suka tashi, King ya kafe Big Bro ba zai auri Sweetie ba, idan har yana sonta to ya musulunta, kuma ita ma ba zata yarda ta auresa ba.
Tsaye suke a tsakiyar ɗakin King sun yi cirko-cirko, ga can su Zarina suna ta faman yi masu ɓarin wuta amma suna ta ƙoƙarin karewa, har yanzu ko missile ɗaya bai sauka a cikin kasan ba dai.
Momma, King, Smart and Big Bro ne suke tsaitsayen nan. A fusace Big Bro ya juya ya fita, kallon juna su momma suka yi, Smart ne ya ce. "Momma kada fa ace tafiyar zai yi da gaske, dan ALLAH kada ku barshi ya koma birninsa, idan har ya koma wlh ba zai sake yarda ya zo in da muke ba, kuma ba zai taɓa musulunta ba, dan ALLAH momma ku dakatar da shi, dan cetansa ku yarda a aura mashi Sweetie ɗin a haka, zamu yi kokari ya musulunta sai ayi auren gaskiya!".
Momma ta lura Smart ya rikice ne, burinsa kawai kada É—an uwansa ya koma birninsa, shiyasa har ya ce a aura mashi Sweetie É—in, ya manta haramcin abin da yake faÉ—e.
"Momma ki yi magana, dan ALLAH ku dakatar da shi, ke kaÉ—ai zaki iya dakatar da shi, ki taushesa, ki faÉ—a mashi zai auri Omaish, ki cecesa momma". A tsananin ruÉ—e Smart yake maganar.
King ne ya ce. "Babu aura mashi ita da zamu yi har sai ya musulunta, ko zai koma birninsa sai dai ya tafi shi kaÉ—ai, ita kuma zamu mayarwa iyayenta ita".
"Hmmmm daddy baka san shi bane, wlh ka ji na rantse ba zan yi kaffara ba a kan Omaish idan bai shafe masarautarsu a doran duniya ba, su karɓeta su ce ba zasu bashi ita ba? Tab lallai daddy baka son zaman lafiya, ina son ka fahimci wani abu dad, shi fa Big Bro karfi baya tankwarasa wlh, dama ka bisa a hankali ne zai yi abin da kake so, kana tinanin ko iyayen Omaish suka tsaya a gabansa sun isa su hanasa aurenta da ya ce zai yi ne? Ba addini ne da shi ba, yana iya kashe iyayen Omaish kuma ya aureta muddin suka ce zasu shiga tsakaninsa da ita, kai kanka daddy wlh ba zai raga maka ba, saboda shi yanzu a juye yake, ba daidai yake da mu ba, momma ki faɗa mashi waye King Of five Empires! Kasan da cewa shi sarki ne a Daular aljanu? Kasan da cewa shi sarki ne na Dauloli har gida huɗu? Kasan kujerar mulkinsa dake black world babu wani sarkin da yake da kwatanta a yanzu? Kasan karfin mulkinsa kuwa? Fito na fito da shi babu riba, gara kawai ku rarrashesa shi zai fi maku". Cikin tashin hankali Smart yake kora masu wanna jawabi.
Yana rufe baki sai ga Big Bro ya shigo damke da hannun Sweetie. Yana zuwa ya saketa a tsakiyar room É—in, ido cikin ido ya kalleta kafin ya ce. "FaÉ—awa dad zaki aureni kamar yadda kika mun alkawari". Ya yi maganar yana pointining King da yatsarsa É—aya.
Kallonsu ta fara yi one by one kafin ta tsayar da kallonta a kansa. Da kyar ta iya cewa. "Zan aureka, amma sai ka musulunta tukun nan zamu yi aure...."
Bata iya karisar da maganar ba sakamakon tsawar da ya daka mata. "No Omaish! Ni ba zan musulunta ba, kuma dole yau zamu yi aure!". Ya faÉ—a tare da sake damko hannunta da nufin su fita waje, a ransa yasa yau zasu yi aure kuma zasu bar kingdom É—in.