Sashe 22
Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai tuni ya yi tsalle ya ce zai koma kan karagar mulkinsa yanzu. Cikin girmamawa Hoorain ya amsa da okey amma dai gaskiya akwai wasu dokikin da za'a soke su, carap Ude ya amsa da ya amince a ciresu. Tamkar Zarina zata tsoma baki a wajen, sai wani huci take yi, amma ta daure ta yi shiru dan kar asirinta ya tonu, tana ji tana gani Ude ya karɓi karagar mulki wanda tsananin ɓacin rai yasa ta yi gaggawar ficewa daga fada, shi kuwa Hoorain cigaba ya yi da zaƙulo dokikin da suka saɓa da addinin islama yana sokesu, Ude bai taka mashi birki ba, dan faɗat sunkuru zasu yi, ba gaba da gaba ba, dan in suka ce gaba da gaba ne lallai ba shakka sun san Hoorain ya fi karfinsu.
Bayan ya kammala cire dik dokokin da basu yi mashi ba, sannan ya ce da daddyn nasa. "Dad ina da shawara". Zuciyar Ude bakincikin tamkar bakin leda, while fuskarsa tana ƙaƙalo annashuwar dole, ba dan ya so ba ya ce. "Wace iriyar shawara kenan son?".
Hoorain dake zaune saman kujerarsa ne ya É—an kara gyara zama kafin ya fara magana a natse. "So nike ka bani dama akwai wasu dokoki da nike son É—aurawa a kan wannan masarauta bisa experience da nike da shi kan mulki". Cike da nuna goyon bayar lallai yana tare da shi ya ce. "Wani irin dokiki ne waÉ—an nan?".
Kara tattara hankalinsa waje guda da kyau Hoorain ya yi kafin ya ce. "Zuwa gobe ko bayan mun sha ruwa zan faɗa maka idan na gama tsarasu, na tabbata zasu ciyar mana da masarauta gaba, sannan zasu yi matuƙar tallafa mana, zasu tallafawa talakan da muke mulka".
Jinjina kai Ude ya yi, sannan ya ce. "Na tabbata dik abin da zaka kawo mai kyau ne, kuma zamu yi maraba da shi". Sosai Hoorain ya ji daÉ—in kalaman mahaifin nasa, hakan yasa ya ce. "To Dad ina son shirya liyafa ta shan ruwan buÉ—a baki da talakawa a cikin gidan nan gobe".
Babbar magana, ai gabaɗaya fada ta koma wannan ya kalli wannan wannan ma ya kalli wannan, abin da ba'a taɓa yi ba tsawon tarihi, wai su zauna da talakawa su sha ruwa da su, tab lallai Hoorain ya zo da babban. Shi kuma Hoorain yanzu a tinaninsa Zarina ce take sanya daddynsa yin wasu abubuwan mugunta, shi ne yasa ya ɗaura ɗamarar yaki da ita, aka ce rashin sani ya fi dare duhu, bai san Ude ya ci uban Zarina a makirci ba!.
"Dad ka yi shiru baka ce komai ba". Cewar Hoorain kenan. Gudun kada Hoorain ya ji ba daÉ—i ko ya zargi wani abin yasa ya ce. "Dan liyafa kawai ai ba komai zaka iya shiryawa".
Tsabar farinciki Hoorain bai san time da ya sauke ajiyar zuciya ba, sannan ya ce. "Thank you Dad". Jinjina kai kawai Ude ya yi alamar to.
Kallon sarkin gida wato mai kula da shige da fice Hoorain ya yi, a natse ya ce. "Ka bada sanarwa cewa gobe ina gayyatar kowa da kowa ya zo mu yi ifter a nan". Cikin girmamawa sarkin gida ya amsa da to sannan ya miƙe ya nufi waje.
Dai'dai lokacin gabaɗaya hayaniya ta karaɗe harabar kingdom ɗin, a take mayakan dake fada suka zare takubansu suka kara kewaye saman stage da ya kasance mallakin sarki da familynsa. Miƙewa Hoorain ya yi yana faɗin bari ya duba menene. A hanzarce waziri ya ce. "A'a ranka ya dade bari mu samu labarin menene kafin ka fita, kada ace abu mai haɗari ne da zai iya cutar da kai".
Cikin mutumtawa Hoorain ya ce. "Horon Abbona ne ni fa, kada ka damu waziri babu abin da zai faru........". Bai kammala rufe baki ba wani dakakken mayaki ya shigo cikin zafa tare da tsayawa ta bakin kofa, sannan ya risinar da kansa ƙasa, cikin girmamawa ya nemi izinin yin magana.
Kai Ude ya jinjina mashi alamar an bashi izinin yin magana. Kara risinar da kansa ya yi kafin ya ce. "Dama wasu mayaka ne daga Crown of Power suka yi mana kutse sai muka kamasu".
A take Ude ya ce. "Ku kashesu kisa mafi muni". Da sauri Hoorain ya ce. "No Dad, su dakata bari in ga su wanene? Saboda ni nasan mayakan King Zuhair basa laɓewa su yi leken asiri, basa zuwa ta baya su yi cuta, su gaba da gaba suke fuskanta, in har mayakan dad King Zuhair dole akwai ƙwaƙƙwaran abin da ya kawosu, bari in dubasu please Dad".
A É—an fusace Ude ya ce. "Bama zaka fita ba bare har ka je dubasu, dan bana son wani abin ya sameka". Ya yi maganar cike da nuna yana kaunar Hoorain É—in. "No Dad babu wani abin da zai faru, ni nasan dangerous warriors, nasan ya suke in and out".
"My son kai baka san sarauta bane, yanzu haka ina da yakinin turosu aka yi su kasheka tin da ka juyawa kingdom É—insu baya".
Kai ya girgiza game da cewa. "No Dad, ina mai imani da ALLAH dad King Zuhair ba zai taɓa turo mutane su kasheni ba, da zai kasheni tin lokacin da na je ɗaukar Hoonaira zai sanya a kasheni, amma ya barni na fita da rai'na, wlh dad yana sona sosai, ni naga hakan a cikin idanunsa, kawai rashin jituwarku ne ma yasa ya nuna wani abin, amma ina da tabbacin King Zuhair ba ragon namiji bane da zai sanya a biyo a kasheni dan na bar kingdom ɗinsu, shi ɗin namijin zaki ne da in ya ga dama har cikin palace ɗin nan zai zo ya kasheni kuma kai kasan babu wanda ya isa ya taka mashi birki". Ya kai karshen maganar tare da dimfaro stage ɗin zai sauko ƙasa, take warriors dake wajen suka buɗawa namijin zaki hanya, dan basu ga alamar wasa ba.
Lokaci guda Ude ya ji tamkar shi Hoorain ya cakawa magana yadda ya ce King Zuhair zaki ne baya tura mayakansa su yi leken asiri, sannan mayakansa basa laɓewa suna leƙe, su gaba da gaba suke zuwa, gabaɗaya sai Ude ya ji ai wannan da su Hoorain yake yi, dan su ne kolaye masu tura ƴan leken asiri, lallai kuwa akwai matsala!.
--------------------🔥
Waje Hoorain ya nufo cike da ƙagara ya ga su wanene daga kingdom of power zasu zo leƙan masarautarsu. Yana fitowa ya yi tozali da Ansar da Anwar, sun jigata sosai, saboda mayakan Zarina sun basu wahala, sai da suka sanya ragar kama zakuna kafin su iya kamasu, saboda a lokacin da suka shigo kingdom ɗin kai tsaye suka shigo babu wata kwana-kwana, shi ne mayakan Zarina suka nemi hallakasu saboda tambarin zaki dake kan hulunan kansu, sun san kingdom of power ce kawai take da tambarin zaki, to su kuma domin kare rayukansu suka zari takuba, nan fa karamun yaki ya kaure a tsakaninsu har suka kashe mayaka biyar, da dai warriors na Zarina suka ga ba zasu iya kamasu ba, sai suka sakar masu ragar kama zaki suka samu damar kamasu, suka ɗauresu da sarka shi ne suka yi masu dukan mutuwa, dik sun jigata da kyar ma suke numfashi.
ALLAH sarki sun kasa iya zama a kingdom of power ne saboda babu Hoorain, suna kewarsa sosai shi ne suka zo ganinsa, wai irin su zasu nuna jarumta ya narke ya haÉ—e da jinin jikinsu shi ne babu ko shakka bare tsoro suka afko kingdom É—in kai tsaye kawai.
Ai Hoorain yana ganinsu bai san lokacin da ya dakawa warriors da suka rirrike sarkan da aka É—auresu tsawa ba. Cikin zafa ya kariso wajen, dik suna cikin sarka, yana zuwa ya sake daka masu tsawa a kan su yi gaggawar kwance mashi su. Zarina na tsaye a sama jikin window É—inta tana ganin dik abin da yake faruwa, kazalika shi ma sadauki Rishan yana tsaye a saman jikin window yana kallonsu.
Da yake warriors dake kula da prison na Kingdom ɗin ne suka kamasu so basu san Hoorain ba, sai suka ce ba zasu sake su Anwar ɗin ba, su umarnin Zarina and Ude kawai zasu bi. Ai cikin wani irin ɓacin rai Hoorain bai san lokacin da ya sanya kafa ya takesu ba, su uku ne a tsaye suna jere dikkansu sai da suka zube ƙasa, ya ji zafin dukan da suka yi wa su Anwar, zaro takubi daga waist na warrior dake kusa da shi ya yi da nufin ya sare wanda ya ce ba zasu kuncesu ɗin ba, dan da alama shi ne shegen da ya jagoranci dukan su Anwar ɗin.
"A'a my son dakata". Cewar sadauki Rishan dake sama. Dakatawa Hoorain ya yi yana wani irin huci, a duniya kun san bashi da aminai biyun su Ansar, yana jinsu tamkar Æ´an uwansa.
Dai'dai lokacin su commander Zafar suka kariso wajen da sauri. Jin sautin muryan sadauki Rishan yasa gabaÉ—aya warriors dake wajen suka zube gwiwowinsu a kasa alamar girmamawa. Da sauri commander Zafar ya matsa ya rungumo Hoorain yana É—an bubbuga bayansa alamar ya huce haka.
Kasa sadauki Rishan ya sauko cikin sauri, kara risinar da kai warriors suka yi. Yana zuwa ya bada umarnin a kwance su Anwar. Warrior da ya yi magana ɗazun ne cikin girmamawa ya ce. "Ranka ya daɗe suna da mugun haɗari, da kyar muka iya kamasu, sai da ma muka sanya masu ragar kama zaki sannan muka iya kamasu, sun kashe mana mayaka har guda biyar, kana ganin kamar sun jigata, ana sakesu ɓarna zasu sake yi mana........."
Bai kai karshen maganar ba sadauki Rishan ya É—aga mashi hannu, a natse ya ce. "Kwancesu!". With harsh voice ya yi maganar!.
Cikin zafa gabaɗaya mayakan suka miƙe tare da zare takubansu suka yi gaggawar kewaye su Hoorain da su wai dan basu tsaro, dan su fa suna bala'in tsoron ɓarnar mayakan King Zuhair, dan sun san ɓarnarsu dayawa yake.
Wanda ya yi magana ɗazun shi ya miƙe cike da tsoron abin da su Anwar zasu iya aikata masu dik da sun kwace takubansu, haka yasa makulli ya buɗe kwaɗon sarkokin da suka ɗauresu. Ai suna buɗewa Anwar and Ansar suka ɗan girgiza jikinsu wanda hakan yasa gabaɗaya warriors na wajen suka sake yi gaggawar ready da takubansu.