← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 130

Sashe 87

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai suna karisawa main parlor bata san lokacin da ta wuce Big Bro da gudu ta faÉ—o tsakiyar parlon ba, daidai lokacin Smart ma ya fito, family dik suna wajen banda Mommah dake barci, King da bashi da lafiya, sai mummyn Chuchu dake barci ita ma, amma dik harda aunty MieMie tana wajen, ga Uncle Taheer baje a kasa baya numfashi, tamkar rai ya yi halinsa, gefe guda kuma Ronnie ne yake tsaye a kan kafafunsa yana wani irin huci, ya yage rigar jikinsa dikka, forehead É—insa sai dubar da jini yake yi, ga Bilal a tsaye suna fuskantar juna shima gaban goshinsa na zubar da jini, da alama kokawa suka yi.

Guyson na tsaye kusa da su Sareena suna kallonsu, hankalin guyson dik ya yi mummunar tashi, faÉ—a ake yi da uncle Taheer Bilal ya shiga, guyson da Ronnie sun fito ne daga room É—insu za su je side na uncle Abban sai suka haÉ—u da uncle Taheer ya fito daga side na mama.

Ronnie da uncle Taheer suma ci karo, to kun san ɗabiar mutanen Black World ne basa cewa mutum sorry, sai Ronni bai ce mashi sorry ba zai wuce, to kun san mutanen kingdom of power, sarauta da son girma da nuna isa a jininsu take, dan haka uncle Taheer bai yi wata-wata ba ya ɗauke fuskar Ronnie da marin da tin da ya zo duniya ba'a taɓa yi mashi ba.

Aikuwa kun san Ronnie renon Big Bro kuma É—an wrestling, zakarar Black World ba zai yafe ba, cikin fushi ya juyo ya É—auke Uncle Taheer da gigitaccen marin da sai da ya sanya shi yin tangal-tangal zai faÉ—i, take kunnuwansa suka É—auke ji na wucin gadin. Sai da ya É—auki minti É—aya kafin ya dawo daidai, shi ne har su Ronnie sun juya zasu tafi ya cakumo wuyar rigar Ronnie É—in, daga nan suka kafa kokawa, daidai lokacin da Bilal ya iso wajen a time É—in Ronnie ya yi wa Uncle Taheer one blow seven die da ya sanya shi suma.

Kun san modarawa da haɗin kai, ka taɓa ɗaya ashirin zasu tarun maka, to shi ne Bilal ya shiganwa Uncle Taheer shi da bai san waye Ronnie ba. Dik da Bilal yake horarre kuma dakken jami'i karfinsu ya zo kusan ɗaya da Ronnie, amma Ronnie ma ya ɗan ɗarasa, hakan yasa suka gwabza faɗa suka jiwa juna ciwo, Bilal da ya ga Ronnie zai iya kashesa sai ya ɗauki wani kwalbar decoration ya bugawa Ronnie a gaban goshi, shi ne ta fashe take jini haka.

Sai magiya guyson yake yi masu a kan su daina sun ki kula shi, da ya ga an fasawa Ronnie goshi ne ya zunduma ihu mai sautin da ya ja hankalin kowa, to tin da family suka zo su Dr Raj sun yi kokarin raba faÉ—ar abin ya ci tura, dan Ronnie ba wasa ba, renon Big Bro ya gwada masu banbancin kwanji. ABIN DA YA FARU KENAN.

Ai Sweetie tana ganin jini a jikin Ronnie ta nufesa da gudu tana ambatar sunansa. Daidai lokacin Bilal ya zo da gudu ya rarumi Ronnie sama zai buga shi da kasa, irin É—aukar unexpected É—in nan ya yi mashi.

Gabaɗaya mutanen dake wajen babu wanda zai iya ce maka ya ga giftawar Big Bro a tsakaninsu sai suka gansa ya tari Ronnie da Bilal ya yi jifa da shi, yau ransa ya yi mummunar ɓaci, sabida ko shi bai taɓa kwanta hakan a kan Ronnie ba, yadda yake kaunar kanin nan nasa, wlh basu isa sun zubar mashi da jini a banza ba.

Cikin fushi ya sauke Ronnie kasa, Bilal na tsaye bai san ya aka yi ba sai jinsa ya yi ya yi sama, kafin ya farga Big Bro ya bugasa da kasa har sai da kafarsa ta bada wata iriyar sauti alamar karaya.

Da karfi Smart ya ce. "Subhanallahi komai kuma ya lalace". Ya kai karshen maganar tare da afkawa tsakiyar parlon da gudu dan in ya barsu ya karawa Bilal duka É—aya sai mutuwa, yanzu ma haka Bilal kam ya fita a hayyacinsa.

GabaÉ—aya parlon salati suka saka, Pretty ta matsa ta rungume Mahnoor tana zazzare ido, sabida ita tasan kokawarsu bata kyau ne, ga É—an banzan tsoro. Ita kuma Sweetie kan Ronnie ta yi da gudu tana ambatar sunansa.

Big Bro yana shirin sanya kafa ya take wuyan Bilal a kasa Smart ya yi zafan rikosa ta baya yana faÉ—in. "Please Big Bro, for give him, nasan dik yadda aka yi su suka tsokani Safras, dan bashi da neman faÉ—a, amma please ka yafe masu".

A cikin fushi ya hankaɗe Smart da karfi, sabida bai ga dalilin da zai sanya ya yafewa wanda zai dubar da jinin Ronnie yana a raye ba. Hannu yasa ya cicciɓo Bilal sama ya kara yin jifa da shi da karfi wanda hakan yasa Bilal numfashinsa ta ɗauke cak. Tsoro ne ya kama gabaɗaya mutanen parlon, Sharifa mai cewa tana son Big Bro ne jikinta ya hau kerma.

Heleena kuwa ruɗewa ta yi, ta kalli Smart ta kalli Big Bro, ta ga kamannin har ya ɓaci. Da gudu Ramish ya fito daga room ɗin king, ganin abin dake faruwa ba karamin ɗaga mashi hankali ya yi ba, da sauri ya kariso cikin parlon dan sanin me yake faruwa?.

Dr Raj dai baya ya ja yana salati yau za'ayi kisan kai a cikin family, Smart da baya gajiya da ƙoƙarin dannan ɗan uwan nasa ne ya sake nufar Big Bro da gudu yana ƙoƙarin rikesa, a karo na biyu ma sake hankaɗe Smart da karfi ya yi.

Hakan yasa Smart ya miƙewa tsaye ya kalli Sweetie dake rungume da Ronnie tana bashi hakuri ya ce. "Sister dakatar mana da heartbeat ɗin nan naki kada ya yi kisan kai, karya kashe kaninsa da kansa". Shi fa Smart yanzu ya gano idan ba Sweetie ba babu wacce zata yi yin gaggawar tausar zuciyar Big Bro cikin ƙanƙanin lokacin, shiyasa ya ce bari ya daina wahalar da kansa yana shan azaba.

Sai a lokacin daga ita har Ronnie ɗin dikka suka kai kallonsu a kan Big Bro, ganin yadda yake huci suka fahimci ransa ya ɓaci. Smart yana faɗin hakan gabaɗaya kallon family ya dawo kan Sweetie, har suka sanya ta ji kunya.

Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta saki Ronnie ta nufi in da Big Bro yake, yana tinkarar Bilal dake kwance baya motsi ne tamkar wani zaki. Daidai zai sanya hannu ya shako wuyar Bilal ya É—agasa sama ta yi gaggawar shiga tsakaninsu, tamkar zata yi kuka, ta É—an tsuke fuska wajen cewa. "Please Big Bro, ka barsa haka, kaga baya motsi ko?".

Hannu yasa zai tureta gefe guda ta yi gaggawar faÉ—awa jikinsa, dan in ba haka ta yi mashi ba ita ma jifa da ita zai yi.

(Big Bro ɗan ikka mai rai ne asuway, yana yin abin da kwata-kwata isn't kamatable, to ni dai bari in haɗa kayana, zuwa gobe zamu ga zai iya tsalleke wannan runguma ya yi jifa da ita ne, ko kuma dai family zasu sha mamaki?🤔 Sweetie ta san ya kan tsiya, ta ce kada ya taɓata, amma yanzu da yake cutarsa zata yi har da rungumesa bawan ALLAH, ba komai zamu rama ne!.)

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
------------------------------------------🔥♥️

SABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥

Anwar ne ya ce. "Dik ba wannan ba, yanaga kamar Lion namu yana cikin ɓacin rai ne?"........... Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Babu komai". Dafa shoulder ɗinsa Ansar ya yi. "Baka taɓa ɓoye mana komai naka ba, meyasa yanzu zaka fara ɓoye mana? Ka manta tare muke kuka kuma mu rarrashi juna?".

Kai ya girgiza kafin ya ce. "Tare muke komai, amma ku yarda dani ba wani abin ke damuna ba, kawai na ji babu daÉ—i ne da nazama sanadiyar zuban hawayen Zunaira yau".

Murmushi Ansar ya yi tare da cewa. "Awwww batu ake na ma'aurata, to shikenan a wannan gaɓa bamu nemi jin me yake damunka ba, je ka yi rarrashi, idan anki kulaka kuma sai ka dawo mu kwana a nan, mu ba zamu hanaka wajen kwana ba kuma ba zamu kiraka tuzuru ba". Cikin zolaya ya yi maganar.

Anwar ne ya capki zancen da cewa. "Gaskiya ina fatan watarana nima in ga wannan rana, ace na yi faÉ—a da matata ina rarrashi tana ja mun rai da yanga, ina son yin aure our Lion". Ya faÉ—a fuskarsa da alamar damuwa..... Dafa shoulder É—insa Hoorain ya yi alamar karfafawa kafin ya ce. "Fito da mata zan yi maka aure É—an uwana, for sure rayuwar aure akwai daÉ—i sosai musamman ka samu wanda kake so yake kuma sonka".

Damuwa ce sosai ta kara bayyana kan fuskar Anwar, murya a rauna ce ya ce. "Ai ni kam bana jin zan samu wanda raina yake so É—in nan, na sota ne tin tana karama amma ni kaina nasan na yi gangancin fara sonta saboda ba samu zan yi ba, amma ba laifina bane, laifin zuciyata ce da bata iya tantance abin da zata iya samu da wanda ya fi karfinta ba kawai ta fara so".

Kallon juna Ansar da Hoorain suka yi kafin su matsa kusa da Anwar sosai dan tausan shi, har suna haÉ—e baki wajen cewa. "Wa kake so É—an uwa".

"Babu amfanin in faÉ—a maku ita, kawai ku bar zancen ALLAH ya bani mafi alkhairi a gareni". Girgiza kai Hoorain ya yi. "A'a please ka faÉ—a mana, zamu tayaka yakin nemanta har mu samu"....... "ÆŠaya ne daga cikin Æ´aÆ´an king Zuhair sister É—in Zunaira". Ya faÉ—a a raunace sosai.

Kallon juna a karo na biyu Ansar da Hoorain suka yi kafin Hoorain cikin tausasawa ya ce. "Wacece daga ciki?".
Chapter 87 · 0% Book details