← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 130

Sashe 120

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin da ya faru shi ne, da ya dawo hayyacinsa ya ga aika-aikan da ya yi, bai bi ta kan Pretty É—in ba ya maida kayan jikinsa ya nufo waje cikin zafa, saboda ya zargi ba lafiya ba. Har ya fita ya dawo ya duba cup É—in da suka sha drinks, a nan ya ga diddigar magani a kasa, shi ne fa ya fusata ya nufi room na Jaish, a nan ya isko Mahnoor tsaye a gaban mirror.

Tsabar fusata ko sallama bai yi mata ba ya ce. "Waye ya baki drinks É—in can ki kawo mana?". Ta tsorata sosai da ganin yanayinsa, muryarta har yana rawa ta ce mashi Sareena, cikin fushi ya juya ya nufi part na uncle Abbas. Yana zuwa bai tsaya tambayar waye ya bata ba ya fara jibgarta tamkar an aikosa.

Da ta ji kamshin mutuwa shi ne ta ce ai Omaid ne ya bata. Ya yi mamakin jin hakan, amma sai ya damkota suka koma family part. Ya wuce room É—insa ya É—auki belt É—insu mai balain zafi.

Omaid da Obaid suna ɗaki ya iskosu, ai yana shiga ya haɗesu da Sareena ya hau zanesu tamkar wanda aka yi wa wahayin duka, shi ne fa Obaid ya samu ya gudu ya je ya sanar da momma. Ko tambayarsu dalili Smart bai yi ba ya hau basu a jikinsu, ga shi shi kansa mugun zazzaɓi yake ji a jikinsa, in ya tina abin da ya yi wa Pretty sai ya taune tongue ɗinsa tamkar zai kashesa saboda haushi. Kansa na yi mashi balain ciwo, amma haka yake dukansu tamkar baya jin wani ciwo a jikinsa, ya ji haushi iya haushi, yasan yanzu ko Pretty ta rayu ba zata yarda da shi ba, dik da ita ta kawo mashi drinks ɗin, bai shirya dis virgin ɗinta ta wanna hanya ba, gaskiya yaran sun cutar da shi.

Da ya tuna haka sai ya kara ɗaga belt ɗin ya hau sauke masu a jikinsu ta ko'ina. Da gudu momma ta shiga tsakaninsu ta rike belt ɗin tana ya isa haka. Ƙoƙarin kwace belt ɗin ya yi saboda yana cikin fushi idanunsa sun rufe. Sai da ta yi magana da karfi sannan ya gane ita ce. A hankali ya sake mata belt ɗin ya koma saman sofa ya zauna.

Daidai lokacin king da Big Bro suka shigo kusan a tare, Big Bro da Sweetie suka shigo, shi kuma King shi kaÉ—ai. Family ta gama haÉ—uwa, dama saura saboda jin ihun su Sareena yasa suka fito da gudu.

Ganin abin dake faruwa yasa King ya umarci da kowa ya zauna dan su ji me yake faruwa ne da Smart ya yi masu irin wanna duka haka. Babu wanda ya ja da batun king, dik suka samu waje suka zazzauna. Kallon momma King ya yi ya tambayi me yake faruwa ne haka?.

Cike da tashin hankali ta ce. "Wlh nima ban sani ba, ga dai Omerish É—in ya yi mana bayanin me yake faruwa".

Dawo da kallonsa a kan Smart King ya yi kafin ya ce. "Omerish me yake faruwa?".

Shiru Smart ya yi for almost 5 mins, sai ajiyar zuciya yake saukewa, har sun fidda ran zai yi magana kafin ya ɗago kai, da kyar ya ɗan taƙaita abin da ya faru tare da ɓoye ɓarnar da ya aikatawa Pretty ya bayyana a matsayin magani suka saka mashi a drinks.

Salati gabaÉ—aya parlon suka sa ban da Big Bro da ya É—aura kafa É—aya bisa É—aya yana ciro wayarsa daga aljihunsa.

Wani irin huci mai tada hankali Smart yake saki, a nan ne momma ta iya fahimtar lallai akwai abin da ya yi wa Pretty, ba iya maganin kawai bane, akwai abin da ya ɓoye.

GabaÉ—aya parlon kallonsu ya dawo a kan twis, Obaid ya makale a baya bayansu Omaid yaki sakin jiki, dan yana tsoron Smart. ALLAH ya cecesa bai sha jibga ba ya gudu wajen momma.

Pointining Smart da hannu Omaid ya yi kafin ya ce. "Na yi É—in, idan kana jin kana da karfi ba sai ka yi abin da zaka yi ba". Babbar magana!.

Zazzaro idanu Momma ta yi a kan twins, idanunsu a bushe garau babu alamar tsoro ko shakka, Jaish har hannu ya kai yana mutsustsuke idanunsa dan ya tabbatar wai shin da gaske su Omaid ne kuwa?.

Dik cikin parlon babu wanda bai zaro idanu a kansu ba sai Big Bro da yake zaune yana danna waya, tamkar babu shi a cikin parlon, kuma dik abin da suke yi a kan kunnensa, sai dai bai motsa ba. Hakan ya yi mugun É—agawa Sweetie hankali, dan ita da Ronnie sun san shirunsa sau da dama baya zama alkhairi.

Smart gagara yin magana ya yi, saboda bai san me zai ce ba, zuciyarsa tamkar zata yi bindiga yake ji, ga shi Momma ta ce kada ya taɓasu kuma, saboda tasan in ya ce zai cigaba da dukansu again ba zasu yi saura ba yadda ransa ya kai ƙololuwar ɓacin nan.

Miƙewa guyson ya yi yana wani irin huci, kafin su momma su ankara sai suka ga guyson ya ɗauke Omaid da wani gigitaccen marin da ya sanya shi zabura ya miƙe tsaye. Unexpected guyson ya ga Omaid ya damko wuyar rigarsa da hannu ɗaya, ɗayan hannunsa kuma ya dafe kuncinsa da shi yana kallon guyson har cikin ido. "Sabome me zaka dakeni?". Omaid ya faɗa.

Ai wani irin zabura su Jaish suka yi ganin abin da yake faruwa, a tarbiyansu ko da sunan wasa Omaid bai isa É—agawa guyson murya ba. GabaÉ—aya jama'ar parlon mimmikewa suka yi suna salati except King and Big Bro sai Smart da ya kifa kansa da gwiwowinsa saboda zafin da zuciyarsa take yi mashi, in ya tuna abin da ya aikata mata yana jin É—aci over.

"Omaid kana da hankali kuwa?!!". Momma ta faÉ—a cikin tsawa. ÆŠagawa momma hannu ya yi yana faÉ—in. "Babu ruwanki a cikin wanna faÉ—ar". Cikin fushi ya faÉ—a yana wani irin huci tamkar kububuwa, kamar zai rufe momma É—in ma da duka.

Haba ai yana faÉ—awa momma haka guyson ya rasa control É—insa, a fusace ya dalla mashi wani marin har sai da ya sake mashi wuyar riga, da karfi yasa kafa ya take Omaid É—in a kirji har sai da ya faÉ—i kasa. Cikin fushi ya fisge belt dake hannun Smart ya hau jibgawa Omid tamkar ALLAH ne ya aikosa.

Can dai ya ga duka da betl bata yi mashi ba, ya yi jifa da betl É—in ya hau tattakasa da kafa, ta ko'ina duka yake kai mashi cikin fushi, idanunsa sun rufe. Kuka Obaid ya fara yi yana faÉ—in su dakatar da Yah Omar kada ya kashe mashi É—an uwa. Sai dai dik parlon babu wanda ya sauraresa.

Da ya ga haka sai ya nufi guyson da kansa, hannunsa ya riko yana bashi hakuri. Guyson ya rigada ya zuciya, baya ji baya gani, ai wani irin kakkarfar jifa ya yi da Obaid É—in har sai da ya daki glass table na tsakiyar parlon, ya cigaba da tattaka Omaid da kafafunsa.

Momma na kokarin yin magana sai gani ta yi Omaid ya miƙe tsaye ya cakumi wuyar guyson yana ƙoƙarin karawa da shi. Nan fa hankalinsu ya kara mummunar tashi, zuciya da zuciya ne suka haɗu. UHM YAU AKE YINTA FA, WAYE ZAI RABA WANNA FAƊA, MEYASA BIG BRO BAI SHIGA FAƊAR BA? ME ZAI BIYO BAYA? MEYASA KING MA YA YI SHIRU?.

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only please.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
Momma na kokarin yin magana sai gani ta yi Omaid ya miƙe tsaye ya cakumi wuyan guyson yana ƙoƙarin karawa da shi. Nan fa hankalinsu ya kara mummunar tashi, zuciya da zuciya ne suka haɗu.

Zuciyar guyson ne ta kara fusata over, hakan yasa ya yi wa Omaid dukan da bai tsammaci zai yi mashi ba, dukan haushi, kuma dik cikin parlon babu wanda ya dakatar da guyson, Jaish ma ya so tashi ya karɓi Omaid ɗin ya yi mashi duka mai kyau, saboda yadda ya riki wuyar guyson ya ɓatawa kowa rai a cikin parlon, abin da ba'a taɓa yi ba a tarihinsu, wai kani ya ɗagawa yayansa murya, kai basu taɓa ganin wannan masifa ba, suna da tarbiya fiye da tinaninku.

Yau dai Mahreen ta tsorata sosai ganin irin fusatar da Omar ya yi, a ranta ta ce kai wai dama haka yake shi ma? Dama balaÆ´aÆ´Æ´e ne. Ganin guyson zai iya kashe mashi É—an uwa babu wanda ya sanya baki ko ya yi yunkurin dakatar da shi ne yasa Obaid ya kwalla kara tare da daka tsalle ya shako wuyan guyson ta baya yana wani irin huci. Kun fa san su twins zasu iya jibgar junansu, amma ba zasu iya bari wani daga can gefe ya daki É—ayansu ba, a kan hakan sai in da karfinsu ya kare, sai dai a kashesu tare.

Ganin ya shake guyson ta sama yasa Omaid kuma ya kama kafafun guyson É—in wai zasu kaisa kasa su ji daÉ—in jibgarsa yadda yakamata, dan ba zasu yafe jinin da ya zubarwa Omaid ba.

Da sauri Dr Raj ya miƙe a nufin zai rabasu faɗa. Hannu king Zuhair ya ɗagawa Dr Raj alamar ya dakata, da mamaki yake bin king da kallo, ya dakata kuma? Ya jefi kansa da wannan tambayar. Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya koma ya zauna yana kallonsu.

Daidai lokacin suka kai guyson kasa, sai ƙoƙarin kwace shakar da Obaid ya yi mashi yake yi, Omaid kuma ya hau kan cikinsa yadda kuka ga damisoshi suke faɗa a daji haka yaran nan twins suka zama. Da kyar guyson ya kwaci shakar nan.
Chapter 120 · 0% Book details