← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 130

Sashe 55

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Perfume dake aljihunta ta fito da shi ta fara fesa mashi a kan fuska. Da yake basu da nauyi barci shi da É—an uwansa, hakan yasa yana jin saukar abu a kan fuskarsa ya É—an motsa tare da fara kokarin waro idanunsa waje.

Ai daddagewa ta yi ta canza murya. Tamkar saukar aradu haka ya ji ta ce. "Manrabbuka"....... Haba ai da yake ya yi karatu yasan su waye zasu yi mashi irin wannan tambaya a kabari, a miliyan É—ari ya zabura ya waro idanunsa waje, sai ya ga ko'ina duhu except É—an gefensa, sannan ga mutum fari tas a tsaye a kansa, take ya fara tinanin ko ya mutu ne yanzu yana cikin kabari mala'ika ya zo yi mashi tambayoyi. A addini yasan idan mala'ika ya tambayeka a kabari baka amsa ba guduma zaka sha, dan haka gudun ya ci azaba yasa ya ce. "Rabiyallahul lazi kalakani". Ya faÉ—a yana zazzare ido, take ya haÉ—a wata uwar zufa yadda kuka san daga cikin gidan bread ya fito, jikinsa na wani irin kerma, gabaÉ—aya ya yi mugum tsorata bawan ALLAH.

WLH DA ZAI SAN MAHREEN CE INA GA IN BAI KASHETA BA DA WUYA TA SAKE MORUWA, YARINYA TA SANYA HATSABIBI JIN TSORO.

Sake daddagewa ta yi ta ce. "Mahdinuka?". Izuwa yanzu ya fara rasa wasu daga cikin kuzarinsa, tsoro ya baibayesa, amma gudun kada ya gagara iya amsa tambayar kabarinsa ya shiga uku yasa ya daddage ya ce. "Diniyal islam".

Hegiya Mahreen bata kyalesa ba ta sake cewa. "Mahhuwan nabika?"....... "An..... An...... Annabiyi..... Huwa Muhammad...... Sallalahu....... Alaihi wa...... Wa sallam". Da kyar da suÉ—in goshi ya iya bada wannan amsa, saboda tsabar kerma da rawar jiki da muryarsa suke yi, wlh ya kai kololuwa wajen tsorata, numfashinsa sama-sama yake fita gwanin ban tausayi.

Sai wani ƙoƙarin danne dariya take yi ita kuma, saboda yadda yake muzurai da ido a gaskiya ya girgizata sosai kuma ya bata dariya, bata yi zatan yana tsoron Mala'iku har haka ba, ashe karamin ɗan iska ne shi, ta faɗa a ranta. NI KAM NA CE DAN KEMA YARINYA CE SHIYASA KIKE GANIN KAMAR MALA'IKUN KABARI BA ABIN TSORO BANE, HMMMM ALLAH DAI KA BAMU WUCEWA LAFIYA, AMMA BAWA YANA CIKIN TASHIN HANKALI!

Tsabar tsorata bai iya tina cewa Mala'ikun ALLAH babu baki a kan fuskarsu kamar da ta zana baki ba, shi dai ya firgita ya tsure.

Shiru ta yi tana kokarin danne dariyarta, dan kada ya ganota, dariyar na neman cin karfinta ne, ga shi yadda ya gagara ko motsin kirki, yana kwance flat bawan ALLAH. Da kyar ta iya shanye dariyar tata kafin ta ce. "Dik da ka amsa tambayoyinka daidai sai ka ɗanɗani azaba, saboda yadda ka rinƙa cin zarafin ƴan adam bayin ALLAH a duniya, ka tozarta mutane!". Ta faɗa da kyar saboda yadda idan ta ga yana zazzaro ido dariya ke shirin kubce mata.

ALLAH sarki Obaid bai san time da ya shiga rawar jini sosai ya fara faÉ—in. "Wlh bani bane, Omaid ne yake shirya komai, ni bana cin zarafin mutane, ALLAH na tuba, wlh na tuba, kuma kullum idan muka yi laifi muna tuba, dan ALLAH kada ku gana mun azaba, na shiga uku mommah na, kullum Yah Jaish sai ya ce mana muji tsoron ALLAH irin wannan rana zata zo, amma muke banza da magarsa, dan ALLAH ku mayar dani duniya in faÉ—awa É—an uwana ya daina zalintar mutane dan kada ya sha azaba shi ma, ina son É—an uwana ban son ya sha azaba".

Tun da ya fara magana Mahreen ta daddage ta toshe baki tana matse kafafu, dan wlh har fitsari ta ji yana ƙoƙarin zubo mata saboda balain dariyar da ya bata, bawan ALLAH ya zaci a lahira yake, wai a mayar da shi duniya ya sanar da Omaid ya tuba, ALLAH sarki yana son ɗan uwansa.

UHM MU YI AIKIN ALKHAIRI, IDAN BA HAKA BA, YADDA OBAID YA KWATANTA DANASANI MARA AMFANI HAKA WANDA BAI KOMA GA ALLAH BA ZAI YI A LOKACIN DA BASHI DA MADOGARA BABU MAI CETANSA A LOKACIN, BA'A KARƁAR TUBA KUMA BA'A SAURARON BAWA.

--------------------🔥♥️

"Yanzu ina Omaid É—an uwan naka yake?".( KUN JI ISKANCI, YO MALAIKA YANA TAMBAYAR IN DAWANI YAKE NE IN BANSA MAHREEN DA IYA SHEGE BA)

Shi kuwa ya fara fita a hayyacinsa ya amsa mata da cewa. "Yana garden, wlh na yi danasani, kuma na yi nadama, na tuba ba zan kara ba".

"Danasani bata amfani a nan, kuma ba'a karɓar tuba, dole ka girbi abin da ka shuka, ka kuntatawa mutane dayawa, dan haka walakiri ku kama shi ku fara ɗanɗana mashi azaban wuta tin daga yanzu kafin ranar hisabi ya ji mai gabaɗaya daga wajen UBANGIJINMU".

Ta faÉ—a tana É—aga hannun riga sama alamar tana kiran su walakiri.

Ai wani irin zabura Obaid ya yi sai ga fitsari a wando malala ta fara zubowa, ya ji za'a gana mashi azaba, fitsari sosai ya tsula a wando fa, KAI GASKIYA MAHREEN TA WUCI TINANINA, ALLAH YA CECEKI RANAR DA OBAID ZAI SAN KE KIKA YI MASHI WANNAN ÆŠANYEN AIKIN, UHM AKWAI CASE.

Wannan zabura da ya yi ya saki fitsari a wandon ashe numfashinsa ta É—auke, diff ya sume a wajen, bawan ALLAH yana da ilimin addini, yasan me ake kira da wutar jahannama, yasan hell fire yaro.

"To idan kana son a sassauta maka hukunci abu biyu zaka yi, kai wannan yaron ma baka ji, babu abin da ya fi kona mana rai irin wannan baiwar ALLAH Mahreen da ka takurawa har da cewa zaka daketa ranar a duniya, yarinya baiwar ALLAH saliha bata tarema komai ba wai zaka daketa, amma ba komai zan yi maka sassauci". Ta faÉ—a tana wani irin jan numfashi. KAI JAMA'A WAI MAHREEN BAIWAR ALLAH, NI KAM MY PEOPLE'S YA ZAMU YI DA MAHREEN NE? DAN TANA NEMAN FIN KARFINA!.

Jin shiru bai amsa mata bane yasa ta sake yin magana, nan ma shiru bai amsa mata ba. Ɗan leƙo fuskarsa ta yi, sai ta ga idanunsa a kakkafe suna kallon sama, ita da bata san suma ba sai ta zaci ya gagara yin magana ne ya tsorata, dan haka sai ta ciro igiyar chajin dake aljihunta, ta hau zuba mashi a jiki. Sai dai har ta zuba mashi sau uku bai motsa ba, hakan yasa ta razana ta hau zazzare ido. A tsora ce ta ce. "Na shiga uku, kar fa ace ya mutu ne da gaske saboda tsorata?!". Ta faɗa tana leƙo fuskarsa.

Daidai wannan lokaci ita ma Sareena dake É—akinsu tana frog jump ta sulale kasa sumammiya, ta ji azaba, bata iya frog jump sosai ba yau ta koya, dan dole ta yi kafa 200, kafafu dik sun kumbura, kuma dik a tinaninta aljanar tana a É—akin shiyasa bata dakata da yi ba, bata san ga Mahreen kam a nan tana shuka wata tsiyar ba ko in ce ta shuka wata tsiyar.

Ai ganin baya motsi yasa Mahreen ta zabura, a miliyan ta nufi waje, kuma tsabar rashin ji bafa ta yi nadama ba, daga karshe ma garden ta nufa wajen Omaid dan shi ma ta yi mashi aljanar karya, har da cewa daga Omaid sai Aneesa da Heleena, wai Heleena ma ta harareta, yau ranar É—aukar fansa ne a kan dik wanda ya yi mata laifi.

Fitowa harabar gidan ta yi, ta nufi garden da sauri tana addu'ar ALLAH yasa Obaid ba mutuwa ya yi ba, amma kuma bata sare da abin da ta yi niya ba.

Daidai zata wuce wasu flower dake shuke kafin ka isa garden É—in sai ganin mutum ta yi a gabanta yana nufota, daga garden shi ma ya fito, sanye yake da white jallabiya irin na jikinta. Da kallo É—aya ta yi mashi ta gane wanene dik da babu wadataccen light a wajen, hakan yasa ta canza tafiya ta koma irin na horori tana wani É—age kafafu da kafaÉ—u sama wai dan ta bashi tsoro.

Daga garden É—in ya fito shi ma. A tsananin natse yake tafiya cikin kamala da natsuwa. A daidai tsakiyar flowers É—in suka haÉ—u da ita, wani irin canza murya ta yi ta ce. "Kai bil adama zo nan".

Juyowa ya yi yana kallonta kafin ya ce. "Oh ranar da na ce ba zan tsorata bane yau kuma kika dawo ko? To wlh yau zaneki zan yi, wai ma uban me kike yi mana yawo a cikin gida ne da daddare? Uban waye ya aikoki kuma wajen waye aka aikoki da kika ishi mutane?." TO JAMA'A ALJANAR KARYA TA HAƊU DA NA GASKE, DAN DAI GUYSON KAM RABI MUTUM NE RABI ALJANI.........😸

Mamaki ne ya kamata, a ranta ta ce kenan ya taɓa haɗuwa da aljanar gaske? Balain can, lallai wannan ya kai namiji, kai ko tsorata bai yi ba.

Bata karisa tinanin nata ba ta ji ya damko wuyar rigarta yana jijjigata da karfi yana faÉ—in. "FaÉ—a mun uban da ya aikoki ko kuma yanzu in ga bayanki".

Tsuru-tsuru ta yi da ido, ga shi bata son asirinta ya tonu. "Idan kina cigaba da zazzare mun idanun nan naki sai na kwakwalesu, zaki faÉ—a mun wanda ya aikoki cikin family É—in mu ne ko sai na canza maki kamanni yanzu?". Yana magana yana kara jijjigata.

Jin hakan yasa ta sake daddagewa ta canza murya wajen cewa. "Ka yi hakuri yanzu zan tafi, kuma ba zan sake dawowa ba". "Ba zan hakura ba yau kam, dole ki faÉ—a mun uban da ya aikoki gidanmu, saboda in ci mutumcin koma wanene ya aikoki".

Cike da mamaki ta ce. "Kana da karfin cin mutumcinsu ne?". ÆŠan zaro mata dara-daran eyes É—insa ya yi kafin ya ce. "Kina tantama ne? To bari in gwada maki kaÉ—an daga cikin karfina". Yana kai karshen maganar da hannu É—aya yasa ya É—agata sama kamar Æ´ar tsana, ya nunawa sama ita kafin ya ce. "Ko kwatan karfina baki gani ba, hannu É—ayana ya fi karfinki, amma bari ki ga yadda zan yi dake". Ya kai karshen maganar zai yi jifa da ita ya makata da jikin bango.

Ai a miliyan ta ware muryarta wajen cewa. "Yah Omar Mahreen ce fa". Yar ƙaniya ta ji zata sha kasa waɗan nan siraran kasusuwan hakarkarin nata su kakkarye tini ta dawo kan saiti, wai Mahreen ce.
Chapter 55 · 0% Book details