← Book details Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 130

Sashe 76

Rawanin Zalinci Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kai King ya jinjina mashi kafin ya ce. "E akwai abin da ya haɗamu na alkawari, amma dogon labari ne, dama na yi wa Omerish alkawarin zan faɗa mashi gaskiyar komai tin kafin ka zo, ina tsoron sake rasa ƴaƴana a karo na biyu ne yasa na gagara faɗawa Omerish, amma yazama dole zan faɗa maku". Ya kai karshen maganar dik dakiya irin nasa da jarumta sai ga idanunsa sun ciko da kwallah, tin daga nan Smart da Ramish suka san ba karamin abu bane King ya ɓoye, abin da zai sanya shi hawaye ai babban balai ne.

"Babu Æ´aÆ´an da zaka sake rasawa daddy, faÉ—a mana meyakefaruwa? Wani alkawari ka yi masu da baka cikaba wanda ya sa suke shan jininka haka?". Cewar Big Bro.

"Zan faÉ—a maku amma ba a daren nan ba, sai zuwa gobe da safe, amma ina ji a jikina da zarar na faÉ—a maku komai zai zo karshe"...... Smart ne ya yi sauri cewa. "Tabbas komai zai zo karshe In Sha ALLAH". Shi kuma Big Bro da ya san yaren tsafi sai ya ce. "Babu abin da zai zo karshe dad, ko kusa ko alama kana tare da mu, ka kwarara kanka ka ji?".

Jinjina masu kai King ya yi, daga nan suka shiga hira King yana basu labarin ɗan uwansa mahaifin su Bobo. Har wajen karfe 10 na dare, sannan ne ya tambayesu sun je wajen Akka sun duba lafiyarta?. Kai suka girgiza alamar a'a, sam King bai ji daɗi ba, dan haka ya ce da safe kafin su zo wajensa su fara zuwa wajenta. Da okey suka amsa mashi kafin su miƙe su sauko kasa suna yi mashi good night.

One by one suka bisa suka bashi sumbata a kumatu kafin su nufi waje. Sai dai suna kaiwa daidai kofa zasu fita muryarsa ya katse su da cewa. "Ina da tabbacin na haifi waÉ—an da zasu tsaya a kan komai nawa!".

Dik cikinsu babu wanda ya fahimci maganarsa sai Big Bro, amma da yake yana da kwarin gwiwa a kansa sai bai É—auki hakan da muhimmanci ba. Smart da Ramish suka amsa da. "In Sha ALLAH a koma ina ne zamu tsaya maka dad". Shi kuma Big Bro ya ce. "Zaka tsaya da kafafunka a gaban ginunnukan dake kwance daddy".

Jinjina kai king ya yi yana sakin murmushin da ya jima bai yi kwatankwacin irinta ba. Har zasu fita again Big Bro ya sake dakatawa ya juya yana kallon King wanda shi ma su yake kallo. A karo na biyu ya sake cewa. "Zaka tsaya da kafafunka a gaban ruguzazzun palace daddy". Cikin alamar karfafawa ya faÉ—a mashi.

Sam King bai amsa masu ba har suka fice, kuma bai cire idanunsa daga kafesu da kallo da ya yi ba, sannan bai daina murmushin da ya fara ba.

Suna fita suka yi hugging juna su ukun dikka, sannan Ramish ya wuce part É—insa yana yi masu good night cike da kauna. Su ma wucewa nasu part É—in suka yi. A daidai tsakiyar kofofinsu suka tsaya suka rungumi juna kafin su yi sallama, basu je ganin momma ba.

Room É—insa Big Bro ya shiga, toilet ya wuce, a gurguje ya yi wanka ya fito. Cikin sexy sleeping dress ya shirya kafin ya tako ya nufi in da Sweetie take kwance, sai tashin wani fitinannen kamshi yake yi.
A gaban sofar da take kwance ya tsugunna, ta lulluɓa da katan bargo tana zuba barci cikin farinciki. Tsautsayi da kaddara tasa ya kai hannunsa ya ɗan yaye bargon wai dan ya ganta da kyau.

Shirye take cikin wasu kyawawan sleeping dress wanda suka zauna ɗas a jikinta, ga shi rigar tana da irin breast cuff ɗin nan, gata da siririn hannu, yadda ta kwanta kana iya ganin tula-tulanta sosai, sannan yaye bargon da ya yi yasa rigar ta kara yin ƙasa sosai, hakan ya basu damar fitowa sasai.

Ɗan lumshe idanunsa ya yi ya sake warosu a kanta, lokaci guda ya wani irin ɗauke wuta, sai ya ji tamkar an shakesa nunfashinsa bata fita da kyau, hannunsa har tana ɗan kerma ya kai zai taɓa mata tula-tula.............

Littafin RAWANIN ZALINCI na kuÉ—i ne, 1k kacal ne kuÉ—in karatunsa, ki biyani hakkina na rubutu ki karanta littafin cikin natsuwa da lumana, na tabbata ke da kanki kin san ya ci kuÉ—insa book É—in nan, dan haka kada ki rike mun hakkina, 1k ba zata rageki da komai ba yar uwa!. 08161390581 Whatsapp me only.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
-------------------------------------------🔥♥️

ZABUWAR DUNIYA STEP ONE!.🔥🔥🔥

23

Tunawa da alkawarin da suka yi wa juna na bazai taɓata bane yasa ya yi gaggawar fasawa, ya janye hannunsa dan baya karya alkawari ta daɗi, sai in abu ta fi karfinsa, kaman da yake mai magana ɗaya haka yake, dan haka sai ya kara jan barkon ya mayar ya rufeta da kyau ba dan ya so ba, ya yi shiru yana kallon face ɗinta for almost 10 mins kafin ya miƙe ya nufi bed ɗinsa.

Har zai kwanta sai ya tina bai ga momma da guyson ba, kuma yana son ganinsu. Dan haka sai ya nufi waje dan ya duba. Room É—in momma ya fara shiga kai tsaye babu ruwansa da ya tsaya tura kuyangu su nemo mashi izini.

Momma ta yi mamakin ganin yadda ya shigo mata babu neman izini, bata san shi nan babu ruwansa da wata sarautarsu ba, shi ma sarki ne a fadarsa, dan yana son ganin mahaifiyarsa sai ya nemi izini, a ta daidai ina aka ce hakan? To koma a ina ne ban da shi Black Tiger ato.

Momma na zaune gefen gado tana magana da daddyn Smart a waya, ya ce su mom Smart su dawo ne suka ce wlh kafansu kafan Smart idan ba haka ba su ba zasu dawo ba, shi ne ya kira momma wa ta sakar mashi mata da É—ansa su dawo in ba haka ba shi ma su jira dirowansa. Kun san mom Smart and daddy akwai love, to haka kawai ta biyo É—anta ta gudu ta barshi ya zama tuzuru, shi ne nan ya ce biyosu zai yi.

Sai hakuri momma take bashi yaki yarda sam, to shi ne ta zauna tana faÉ—a mashi abin da ya tsayar da Smart É—in yasa bai É—awo.

Big Bro yana shigowa ya zauna a kusa da ita shiru yana sauraron abin da take faÉ—e dik da baya jin larabci, yana ta kallonta tamkar ya ga wata bakuwar halitta daga wata duniya.

Ganin kallon ya yi mata yawa ne yasa ta kai hannunta ta É—an rufe mashi idanu tana murmushi. Nisawa ya É—an yi kafin yasa hannun ya zame hannunta dake kan fuskar tasa, sannan ya rike hannun nata yana É—an jujjuya yatsunta kaman yana duba wani abin.

A haka suka kasance har ta kammala waya, tana katse kiran ta ce. "Baka yi barci ba?". Kai ya É—an jinjina mata yana kallon yatsunta. "Ko dai wajen namu bai yi maka bane yasa baka yi barci ba?".

Nan ma kai ya jinjina kawai wanda kuma Momma bata fahimci me yake nufi ba, ta dai gane baya son magana kuma baya son hayaniya sam-sam. Shiru suka yi for almost 10 mins, a tinanin ta zai yi magana sai ta ga shi fa ko shekara zasu yi shiru ba zai damu ba, dan haka sai ta ce. "Kana son wani abin ne?".

Kai ya gyaÉ—a mata sama kafin ya ce. "Ina son ki kira Auta a kawota nan gobe". Cike da mamaki ta ce meyasa. Shiru ya yi for almost 2 mins, har ta fidda rai zai yi magana sai kuma ya ce. "Ina son ganinta".

Ajiyar zuciya momma ta sauke, da ta zaci wani abin ne. Kamar yana son yin wata magana again, sai kuma ya yi shiru tare da miƙewa tsaye, ita ma ta fahimci akwai abin da yake son faɗa mata, amma harshensa tai mashi nauyi, bai saba yawan magana ba, dan haka sai ya gagara jan dogon hira da ita.

"Good night". Shi ne kawai abin da ya iya sake faɗa kafin ya miƙe ya nufi door. Da kallo ta bi bayansa, a ranta tana jin akwai abin da ya saɓa a rayuwarsa sosai, ba haka kawai yake da mugun bawa mutum tsoro ba, ita kanta shakkar ganin cikin idanunsa take yi, idan ta kallesa a lokacin ta sake kallonsa gabanta har faɗuwa yake yi, kun tuna a birninsa ma babu mai iya ganin cikin idonsa? To kunga ai mutanan Crown Of Power sun yi kokari da suke iya ganin idonsa, dan suna sallah ne yasa suke da jarunta da kwarin gwiwar iya kallonsa.
Chapter 76 · 0% Book details